Shafin farko › Surori › Suratu Ash-Shu'araa
Suratu Ash-Shu'araa الشعراء
Ayoyi 227 · Makka · tsarin saukarwa 47
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ طسٓمٓ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi T. S̃. M̃.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
تِلْكَ ءَايَٰتُ ٱلْكِتَٰبِ ٱلْمُبِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَعَلَّكَ بَٰخِعٌ نَّفْسَكَ أَلَّا يَكُونُوا۟ مُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba! [1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِن نَّشَأْ نُنَزِّلْ عَلَيْهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ءَايَةً فَظَلَّتْ أَعْنَٰقُهُمْ لَهَا خَٰضِعِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا يَأْتِيهِم مِّن ذِكْرٍ مِّنَ ٱلرَّحْمَٰنِ مُحْدَثٍ إِلَّا كَانُوا۟ عَنْهُ مُعْرِضِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَقَدْ كَذَّبُوا۟ فَسَيَأْتِيهِمْ أَنۢبَٰٓؤُا۟ مَا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَوَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَى ٱلْأَرْضِ كَمْ أَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذْ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱئْتِ ٱلْقَوْمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَوْمَ فِرْعَوْنَ أَلَا يَتَّقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ رَبِّ إِنِّىٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيَضِيقُ صَدْرِى وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِى فَأَرْسِلْ إِلَىٰ هَٰرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci[1] kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَهُمْ عَلَىَّ ذَنۢبٌ فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ كَلَّا فَٱذْهَبَا بِـَٔايَٰتِنَآ إِنَّا مَعَكُم مُّسْتَمِعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأْتِيَا فِرْعَوْنَ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولُ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَنْ أَرْسِلْ مَعَنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ أَلَمْ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدًا وَلَبِثْتَ فِينَا مِنْ عُمُرِكَ سِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفَعَلْتَ فَعْلَتَكَ ٱلَّتِى فَعَلْتَ وَأَنتَ مِنَ ٱلْكَٰفِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ فَعَلْتُهَآ إِذًا وَأَنَا۠ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَفَرَرْتُ مِنكُمْ لَمَّا خِفْتُكُمْ فَوَهَبَ لِى رَبِّى حُكْمًا وَجَعَلَنِى مِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتِلْكَ نِعْمَةٌ تَمُنُّهَا عَلَىَّ أَنْ عَبَّدتَّ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ فِرْعَوْنُ وَمَا رَبُّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَآ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ لِمَنْ حَوْلَهُۥٓ أَلَا تَسْتَمِعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ رَبُّكُمْ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ ٱلَّذِىٓ أُرْسِلَ إِلَيْكُمْ لَمَجْنُونٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ رَبُّ ٱلْمَشْرِقِ وَٱلْمَغْرِبِ وَمَا بَيْنَهُمَآ إِن كُنتُمْ تَعْقِلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ لَئِنِ ٱتَّخَذْتَ إِلَٰهًا غَيْرِى لَأَجْعَلَنَّكَ مِنَ ٱلْمَسْجُونِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكَ بِشَىْءٍ مُّبِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ فَأْتِ بِهِۦٓ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَلْقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِىَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِىَ بَيْضَآءُ لِلنَّٰظِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ لِلْمَلَإِ حَوْلَهُۥٓ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٌ عَلِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُم بِسِحْرِهِۦ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوٓا۟ أَرْجِهْ وَأَخَاهُ وَٱبْعَثْ فِى ٱلْمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَجُمِعَ ٱلسَّحَرَةُ لِمِيقَٰتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلْ أَنتُم مُّجْتَمِعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ ٱلسَّحَرَةَ إِن كَانُوا۟ هُمُ ٱلْغَٰلِبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالُوا۟ لِفِرْعَوْنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجْرًا إِن كُنَّا نَحْنُ ٱلْغَٰلِبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ نَعَمْ وَإِنَّكُمْ إِذًا لَّمِنَ ٱلْمُقَرَّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلْقُوا۟ مَآ أَنتُم مُّلْقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَلْقَوْا۟ حِبَالَهُمْ وَعِصِيَّهُمْ وَقَالُوا۟ بِعِزَّةِ فِرْعَوْنَ إِنَّا لَنَحْنُ ٱلْغَٰلِبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَلْقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِىَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأُلْقِىَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
رَبِّ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ubangijin Mũsa da Hãrũna."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ ءَامَنتُمْ لَهُۥ قَبْلَ أَنْ ءَاذَنَ لَكُمْ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِى عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحْرَ فَلَسَوْفَ تَعْلَمُونَ لَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلَٰفٍ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمْ أَجْمَعِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ لَا ضَيْرَ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا نَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَٰيَٰنَآ أَن كُنَّآ أَوَّلَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنْ أَسْرِ بِعِبَادِىٓ إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã[1] ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَرْسَلَ فِرْعَوْنُ فِى ٱلْمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَشِرْذِمَةٌ قَلِيلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّهُمْ لَنَا لَغَآئِظُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَٰذِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَخْرَجْنَٰهُم مِّن جَنَّٰتٍ وَعُيُونٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكُنُوزٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da taskõki da mazauni mai kyau.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَٰلِكَ وَأَوْرَثْنَٰهَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَتْبَعُوهُم مُّشْرِقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَمَّا تَرَٰٓءَا ٱلْجَمْعَانِ قَالَ أَصْحَٰبُ مُوسَىٰٓ إِنَّا لَمُدْرَكُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ كَلَّآ إِنَّ مَعِىَ رَبِّى سَيَهْدِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضْرِب بِّعَصَاكَ ٱلْبَحْرَ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرْقٍ كَٱلطَّوْدِ ٱلْعَظِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge,[1] kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَزْلَفْنَا ثَمَّ ٱلْـَٔاخَرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَنجَيْنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجْمَعِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ أَغْرَقْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ إِبْرَٰهِيمَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦ مَا تَعْبُدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ نَعْبُدُ أَصْنَامًا فَنَظَلُّ لَهَا عَٰكِفِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ هَلْ يَسْمَعُونَكُمْ إِذْ تَدْعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَوْ يَنفَعُونَكُمْ أَوْ يَضُرُّونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ بَلْ وَجَدْنَآ ءَابَآءَنَا كَذَٰلِكَ يَفْعَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ أَفَرَءَيْتُم مَّا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُمُ ٱلْأَقْدَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِنَّهُمْ عَدُوٌّ لِّىٓ إِلَّا رَبَّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِى خَلَقَنِى فَهُوَ يَهْدِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلَّذِى هُوَ يُطْعِمُنِى وَيَسْقِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلَّذِى يُمِيتُنِى ثُمَّ يُحْيِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلَّذِىٓ أَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لِى خَطِيٓـَٔتِى يَوْمَ ٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
رَبِّ هَبْ لِى حُكْمًا وَأَلْحِقْنِى بِٱلصَّٰلِحِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱجْعَل لِّى لِسَانَ صِدْقٍ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya[1] a cikin mutãnen ƙarshe."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱجْعَلْنِى مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ ٱلنَّعِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱغْفِرْ لِأَبِىٓ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَا تُخْزِنِى يَوْمَ يُبْعَثُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَوْمَ لَا يَنفَعُ مَالٌ وَلَا بَنُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا مَنْ أَتَى ٱللَّهَ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأُزْلِفَتِ ٱلْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَبُرِّزَتِ ٱلْجَحِيمُ لِلْغَاوِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقِيلَ لَهُمْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مِن دُونِ ٱللَّهِ هَلْ يَنصُرُونَكُمْ أَوْ يَنتَصِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَكُبْكِبُوا۟ فِيهَا هُمْ وَٱلْغَاوُۥنَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai aka kikkife su[1] a cikinta, su da halakakkun.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَجُنُودُ إِبْلِيسَ أَجْمَعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ وَهُمْ فِيهَا يَخْتَصِمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
تَٱللَّهِ إِن كُنَّا لَفِى ضَلَٰلٍ مُّبِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَضَلَّنَآ إِلَّا ٱلْمُجْرِمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَا لَنَا مِن شَٰفِعِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma bã mu da abõki, masõyi."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَوْ أَنَّ لَنَا كَرَّةً فَنَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَتْ قَوْمُ نُوحٍ ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Bã zã ku ji tsoron Allah ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوٓا۟ أَنُؤْمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلْأَرْذَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ وَمَا عِلْمِى بِمَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنْ حِسَابُهُمْ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّى لَوْ تَشْعُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ban zama mai kõre mũminai ba."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنْ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَٰنُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمَرْجُومِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوْمِى كَذَّبُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱفْتَحْ بَيْنِى وَبَيْنَهُمْ فَتْحًا وَنَجِّنِى وَمَن مَّعِىَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَنجَيْنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِى ٱلْفُلْكِ ٱلْمَشْحُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ أَغْرَقْنَا بَعْدُ ٱلْبَاقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَتْ عَادٌ ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَتَبْنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةً تَعْبَثُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin, kunã yin ginin sitadiyo[1] a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمْ تَخْلُدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?[1]"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا بَطَشْتُم بَطَشْتُمْ جَبَّارِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱتَّقُوا۟ ٱلَّذِىٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعْلَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمَدَّكُم بِأَنْعَٰمٍ وَبَنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَجَنَّٰتٍ وَعُيُونٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Da gõnaki da marẽmari."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنِّىٓ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ سَوَآءٌ عَلَيْنَآ أَوَعَظْتَ أَمْ لَمْ تَكُن مِّنَ ٱلْوَٰعِظِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنْ هَٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen[1] mutãnen farko."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَكَذَّبُوهُ فَأَهْلَكْنَٰهُمْ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَتْ ثَمُودُ ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ صَٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَتُتْرَكُونَ فِى مَا هَٰهُنَآ ءَامِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin, anã barin ku[1] a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِى جَنَّٰتٍ وَعُيُونٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "A cikin gõnaki da marẽmari."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَزُرُوعٍ وَنَخْلٍ طَلْعُهَا هَضِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi[1] mãsu narkẽwa a ciki?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَنْحِتُونَ مِنَ ٱلْجِبَالِ بُيُوتًا فَٰرِهِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَا تُطِيعُوٓا۟ أَمْرَ ٱلْمُسْرِفِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِينَ يُفْسِدُونَ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا يُصْلِحُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوٓا۟ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلْمُسَحَّرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا فَأْتِ بِـَٔايَةٍ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ هَٰذِهِۦ نَاقَةٌ لَّهَا شِرْبٌ وَلَكُمْ شِرْبُ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan[1] yini, kuma kunã da shan yini sasanne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابُ يَوْمٍ عَظِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَعَقَرُوهَا فَأَصْبَحُوا۟ نَٰدِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَخَذَهُمُ ٱلْعَذَابُ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍ ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da ɗan'uwansu,[1] Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَتَأْتُونَ ٱلذُّكْرَانَ مِنَ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمْ رَبُّكُم مِّنْ أَزْوَٰجِكُم بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ عَادُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَٰلُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُخْرَجِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ إِنِّى لِعَمَلِكُم مِّنَ ٱلْقَالِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
رَبِّ نَجِّنِى وَأَهْلِى مِمَّا يَعْمَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَنَجَّيْنَٰهُ وَأَهْلَهُۥٓ أَجْمَعِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا عَجُوزًا فِى ٱلْغَٰبِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ دَمَّرْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا فَسَآءَ مَطَرُ ٱلْمُنذَرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَ أَصْحَٰبُ لْـَٔيْكَةِ ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ قَالَ لَهُمْ شُعَيْبٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَوْفُوا۟ ٱلْكَيْلَ وَلَا تَكُونُوا۟ مِنَ ٱلْمُخْسِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَزِنُوا۟ بِٱلْقِسْطَاسِ ٱلْمُسْتَقِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَا تَبْخَسُوا۟ ٱلنَّاسَ أَشْيَآءَهُمْ وَلَا تَعْثَوْا۟ فِى ٱلْأَرْضِ مُفْسِدِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱتَّقُوا۟ ٱلَّذِى خَلَقَكُمْ وَٱلْجِبِلَّةَ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوٓا۟ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلْمُسَحَّرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا وَإِن نَّظُنُّكَ لَمِنَ ٱلْكَٰذِبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَسْقِطْ عَلَيْنَا كِسَفًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ رَبِّىٓ أَعْلَمُ بِمَا تَعْمَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمْ عَذَابُ يَوْمِ ٱلظُّلَّةِ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije[1] ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّهُۥ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلْأَمِينُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Rũhi[1] amintacce ne ya sauka da shi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَلَىٰ قَلْبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلْمُنذِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بِلِسَانٍ عَرَبِىٍّ مُّبِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da harshe na Larabci mai bayãni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّهُۥ لَفِى زُبُرِ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَوَلَمْ يَكُن لَّهُمْ ءَايَةً أَن يَعْلَمَهُۥ عُلَمَٰٓؤُا۟ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَوْ نَزَّلْنَٰهُ عَلَىٰ بَعْضِ ٱلْأَعْجَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَقَرَأَهُۥ عَلَيْهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ مُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَٰلِكَ سَلَكْنَٰهُ فِى قُلُوبِ ٱلْمُجْرِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَا يُؤْمِنُونَ بِهِۦ حَتَّىٰ يَرَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَلِيمَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَيَأْتِيَهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَيَقُولُوا۟ هَلْ نَحْنُ مُنظَرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ashe, to, da azãbar Mu suke nẽman gaggãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَرَءَيْتَ إِن مَّتَّعْنَٰهُمْ سِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ جَآءَهُم مَّا كَانُوا۟ يُوعَدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَآ أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يُمَتَّعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare[1] su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍ إِلَّا لَهَا مُنذِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ذِكْرَىٰ وَمَا كُنَّا ظَٰلِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا تَنَزَّلَتْ بِهِ ٱلشَّيَٰطِينُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا يَنۢبَغِى لَهُمْ وَمَا يَسْتَطِيعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُمْ عَنِ ٱلسَّمْعِ لَمَعْزُولُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَا تَدْعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلْمُعَذَّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَنذِرْ عَشِيرَتَكَ ٱلْأَقْرَبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱخْفِضْ جَنَاحَكَ لِمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka sassauta fikãfikanka[1] ga wanda ya bĩ ka daga mũminai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِنْ عَصَوْكَ فَقُلْ إِنِّى بَرِىٓءٌ مِّمَّا تَعْمَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَوَكَّلْ عَلَى ٱلْعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِى يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَقَلُّبَكَ فِى ٱلسَّٰجِدِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Shi, Shi[1] ne Mai ji, Masani.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَلْ أُنَبِّئُكُمْ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَٰطِينُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, (kunã so) in gaya[1] muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يُلْقُونَ ٱلسَّمْعَ وَأَكْثَرُهُمْ كَٰذِبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلْغَاوُۥنَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma mawãƙa[1] halakakku ne ke bin su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَلَمْ تَرَ أَنَّهُمْ فِى كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَنَّهُمْ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَذَكَرُوا۟ ٱللَّهَ كَثِيرًا وَٱنتَصَرُوا۟ مِنۢ بَعْدِ مَا ظُلِمُوا۟ وَسَيَعْلَمُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓا۟ أَىَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Al-Furqaan
Suratu An-Naml →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.