Shafin farko › Surori › Suratu As-Saaffaat
Suratu As-Saaffaat الصافات
Ayoyi 182 · Makka · tsarin saukarwa 56
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلصَّٰٓفَّٰتِ صَفًّا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱلزَّٰجِرَٰتِ زَجْرًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan mãsu yin tsãwa[1] dõmin gargaɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱلتَّٰلِيَٰتِ ذِكْرًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ إِلَٰهَكُمْ لَوَٰحِدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَرَبُّ ٱلْمَشَٰرِقِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنْيَا بِزِينَةٍ ٱلْكَوَاكِبِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَحِفْظًا مِّن كُلِّ شَيْطَٰنٍ مَّارِدٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلْمَلَإِ ٱلْأَعْلَىٰ وَيُقْذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
دُحُورًا وَلَهُمْ عَذَابٌ وَاصِبٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا مَنْ خَطِفَ ٱلْخَطْفَةَ فَأَتْبَعَهُۥ شِهَابٌ ثَاقِبٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱسْتَفْتِهِمْ أَهُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَم مَّنْ خَلَقْنَآ إِنَّا خَلَقْنَٰهُم مِّن طِينٍ لَّازِبٍۭ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلْ عَجِبْتَ وَيَسْخَرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ذُكِّرُوا۟ لَا يَذْكُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا رَأَوْا۟ ءَايَةً يَسْتَسْخِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَالُوٓا۟ إِنْ هَٰذَآ إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَوَءَابَآؤُنَا ٱلْأَوَّلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ashe kõ da ubanninmu na farko?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قُلْ نَعَمْ وَأَنتُمْ دَٰخِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِنَّمَا هِىَ زَجْرَةٌ وَٰحِدَةٌ فَإِذَا هُمْ يَنظُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَالُوا۟ يَٰوَيْلَنَا هَٰذَا يَوْمُ ٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱحْشُرُوا۟ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ وَأَزْوَٰجَهُمْ وَمَا كَانُوا۟ يَعْبُدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مِن دُونِ ٱللَّهِ فَٱهْدُوهُمْ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلْجَحِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقِفُوهُمْ إِنَّهُم مَّسْـُٔولُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَا لَكُمْ لَا تَنَاصَرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلْ هُمُ ٱلْيَوْمَ مُسْتَسْلِمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَآءَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوٓا۟ إِنَّكُمْ كُنتُمْ تَأْتُونَنَا عَنِ ٱلْيَمِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ بَل لَّمْ تَكُونُوا۟ مُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيْكُم مِّن سُلْطَٰنٍۭ بَلْ كُنتُمْ قَوْمًا طَٰغِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَحَقَّ عَلَيْنَا قَوْلُ رَبِّنَآ إِنَّا لَذَآئِقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَغْوَيْنَٰكُمْ إِنَّا كُنَّا غَٰوِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِنَّهُمْ يَوْمَئِذٍ فِى ٱلْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِٱلْمُجْرِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُمْ كَانُوٓا۟ إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوٓا۟ ءَالِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَّجْنُونٍۭ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلْ جَآءَ بِٱلْحَقِّ وَصَدَّقَ ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّكُمْ لَذَآئِقُوا۟ ٱلْعَذَابِ ٱلْأَلِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أُو۟لَٰٓئِكَ لَهُمْ رِزْقٌ مَّعْلُومٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Waɗannan sunã da abinci sananne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَوَٰكِهُ وَهُم مُّكْرَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِى جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A cikin gidãjen Aljannar ni'ima.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَٰبِلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يُطَافُ عَلَيْهِم بِكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍۭ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَيْضَآءَ لَذَّةٍ لِّلشَّٰرِبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Farã mai dãɗi ga mashãyan.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَا فِيهَا غَوْلٌ وَلَا هُمْ عَنْهَا يُنزَفُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَعِندَهُمْ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرْفِ عِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَأَنَّهُنَّ بَيْضٌ مَّكْنُونٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَآءَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ قَآئِلٌ مِّنْهُمْ إِنِّى كَانَ لِى قَرِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَقُولُ أَءِنَّكَ لَمِنَ ٱلْمُصَدِّقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَدِينُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ هَلْ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱطَّلَعَ فَرَءَاهُ فِى سَوَآءِ ٱلْجَحِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ تَٱللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرْدِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَوْلَا نِعْمَةُ رَبِّى لَكُنتُ مِنَ ٱلْمُحْضَرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَمَا نَحْنُ بِمَيِّتِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا مَوْتَتَنَا ٱلْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لِمِثْلِ هَٰذَا فَلْيَعْمَلِ ٱلْعَٰمِلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَذَٰلِكَ خَيْرٌ نُّزُلًا أَمْ شَجَرَةُ ٱلزَّقُّومِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا جَعَلْنَٰهَا فِتْنَةً لِّلظَّٰلِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهَا شَجَرَةٌ تَخْرُجُ فِىٓ أَصْلِ ٱلْجَحِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
طَلْعُهَا كَأَنَّهُۥ رُءُوسُ ٱلشَّيَٰطِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِنَّهُمْ لَـَٔاكِلُونَ مِنْهَا فَمَالِـُٔونَ مِنْهَا ٱلْبُطُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ إِنَّ لَهُمْ عَلَيْهَا لَشَوْبًا مِّنْ حَمِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ إِنَّ مَرْجِعَهُمْ لَإِلَى ٱلْجَحِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُمْ أَلْفَوْا۟ ءَابَآءَهُمْ ضَآلِّينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَهُمْ عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِمْ يُهْرَعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ ضَلَّ قَبْلَهُمْ أَكْثَرُ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلْمُنذَرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ نَادَىٰنَا نُوحٌ فَلَنِعْمَ ٱلْمُجِيبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنَجَّيْنَٰهُ وَأَهْلَهُۥ مِنَ ٱلْكَرْبِ ٱلْعَظِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَجَعَلْنَا ذُرِّيَّتَهُۥ هُمُ ٱلْبَاقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَلَٰمٌ عَلَىٰ نُوحٍ فِى ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle shi, yanã daga bãyin Mu mũminai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ أَغْرَقْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِۦ لَإِبْرَٰهِيمَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ جَآءَ رَبَّهُۥ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da ya je wa ubangijinsa da zũciya kuɓutacciya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦ مَاذَا تَعْبُدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَئِفْكًا ءَالِهَةً دُونَ ٱللَّهِ تُرِيدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَنَظَرَ نَظْرَةً فِى ٱلنُّجُومِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَقَالَ إِنِّى سَقِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَتَوَلَّوْا۟ عَنْهُ مُدْبِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَرَاغَ إِلَىٰٓ ءَالِهَتِهِمْ فَقَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَا لَكُمْ لَا تَنطِقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Me ya sãme ku, bã ku magana?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَرَاغَ عَلَيْهِمْ ضَرْبًۢا بِٱلْيَمِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَقْبَلُوٓا۟ إِلَيْهِ يَزِفُّونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ ٱبْنُوا۟ لَهُۥ بُنْيَٰنًا فَأَلْقُوهُ فِى ٱلْجَحِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَرَادُوا۟ بِهِۦ كَيْدًا فَجَعَلْنَٰهُمُ ٱلْأَسْفَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَالَ إِنِّى ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّى سَيَهْدِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
رَبِّ هَبْ لِى مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَبَشَّرْنَٰهُ بِغُلَٰمٍ حَلِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro [1]mai haƙuri.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ ٱلسَّعْىَ قَالَ يَٰبُنَىَّ إِنِّىٓ أَرَىٰ فِى ٱلْمَنَامِ أَنِّىٓ أَذْبَحُكَ فَٱنظُرْ مَاذَا تَرَىٰ قَالَ يَٰٓأَبَتِ ٱفْعَلْ مَا تُؤْمَرُ سَتَجِدُنِىٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّٰبِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَمَّآ أَسْلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلْجَبِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنَٰدَيْنَٰهُ أَن يَٰٓإِبْرَٰهِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَدْ صَدَّقْتَ ٱلرُّءْيَآ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلْبَلَٰٓؤُا۟ ٱلْمُبِينُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفَدَيْنَٰهُ بِذِبْحٍ عَظِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِبْرَٰهِيمَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَبَشَّرْنَٰهُ بِإِسْحَٰقَ نَبِيًّا مِّنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka yi masa bushãra[1] Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَبَٰرَكْنَا عَلَيْهِ وَعَلَىٰٓ إِسْحَٰقَ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحْسِنٌ وَظَالِمٌ لِّنَفْسِهِۦ مُبِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنَجَّيْنَٰهُمَا وَقَوْمَهُمَا مِنَ ٱلْكَرْبِ ٱلْعَظِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنَصَرْنَٰهُمْ فَكَانُوا۟ هُمُ ٱلْغَٰلِبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَءَاتَيْنَٰهُمَا ٱلْكِتَٰبَ ٱلْمُسْتَبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَهَدَيْنَٰهُمَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلْمُسْتَقِيمَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِمَا فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَلَٰمٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُمَا مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ إِلْيَاسَ لَمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِۦٓ أَلَا تَتَّقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَتَدْعُونَ بَعْلًا وَتَذَرُونَ أَحْسَنَ ٱلْخَٰلِقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱللَّهَ رَبَّكُمْ وَرَبَّ ءَابَآئِكُمُ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِلْ يَاسِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Aminci ya tabbata ga Ilyãs.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle shĩ, yanã daga bãyin Mu mũminai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ لُوطًا لَّمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ نَجَّيْنَٰهُ وَأَهْلَهُۥٓ أَجْمَعِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا عَجُوزًا فِى ٱلْغَٰبِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ دَمَّرْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِم مُّصْبِحِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَبِٱلَّيْلِ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ أَبَقَ إِلَى ٱلْفُلْكِ ٱلْمَشْحُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ ٱلْمُدْحَضِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱلْتَقَمَهُ ٱلْحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَوْلَآ أَنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلْمُسَبِّحِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَلَبِثَ فِى بَطْنِهِۦٓ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَنَبَذْنَٰهُ بِٱلْعَرَآءِ وَهُوَ سَقِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَنۢبَتْنَا عَلَيْهِ شَجَرَةً مِّن يَقْطِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَرْسَلْنَٰهُ إِلَىٰ مِا۟ئَةِ أَلْفٍ أَوْ يَزِيدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَـَٔامَنُوا۟ فَمَتَّعْنَٰهُمْ إِلَىٰ حِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱسْتَفْتِهِمْ أَلِرَبِّكَ ٱلْبَنَاتُ وَلَهُمُ ٱلْبَنُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ خَلَقْنَا ٱلْمَلَٰٓئِكَةَ إِنَٰثًا وَهُمْ شَٰهِدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَلَآ إِنَّهُم مِّنْ إِفْكِهِمْ لَيَقُولُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَدَ ٱللَّهُ وَإِنَّهُمْ لَكَٰذِبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَصْطَفَى ٱلْبَنَاتِ عَلَى ٱلْبَنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannan hukunci)?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, bã ku tunãni?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ لَكُمْ سُلْطَٰنٌ مُّبِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأْتُوا۟ بِكِتَٰبِكُمْ إِن كُنتُمْ صَٰدِقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَجَعَلُوا۟ بَيْنَهُۥ وَبَيْنَ ٱلْجِنَّةِ نَسَبًا وَلَقَدْ عَلِمَتِ ٱلْجِنَّةُ إِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma suka sanya nasaba a tsakãnin Sa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سُبْحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَآ أَنتُمْ عَلَيْهِ بِفَٰتِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا مَنْ هُوَ صَالِ ٱلْجَحِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا مِنَّآ إِلَّا لَهُۥ مَقَامٌ مَّعْلُومٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,[1] fãce yanã da matsayi sananne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّا لَنَحْنُ ٱلصَّآفُّونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّا لَنَحْنُ ٱلْمُسَبِّحُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِن كَانُوا۟ لَيَقُولُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَوْ أَنَّ عِندَنَا ذِكْرًا مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَكُنَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَكَفَرُوا۟ بِهِۦ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ سَبَقَتْ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, haƙĩƙa kalmar Mu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُمْ لَهُمُ ٱلْمَنصُورُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ ٱلْغَٰلِبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَبْصِرْهُمْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمْ فَسَآءَ صَبَاحُ ٱلْمُنذَرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَبْصِرْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سُبْحَٰنَ رَبِّكَ رَبِّ ٱلْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَسَلَٰمٌ عَلَى ٱلْمُرْسَلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Yaseen
Suratu Saad →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.