caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Yaseen يس

Ayoyi 83 · Makka · tsarin saukarwa 41

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ يسٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiY. S̃.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْقُرْءَانِ ٱلْحَكِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiInã rantsuwa da Al-ƙur'ãni[1] Mai hikima.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّكَ لَمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle kai, haƙĩƙa kanã cikin Manzanni.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عَلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA kan hanya madaidaiciya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تَنزِيلَ ٱلْعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِتُنذِرَ قَوْمًا مَّآ أُنذِرَ ءَابَآؤُهُمْ فَهُمْ غَٰفِلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَقَدْ حَقَّ ٱلْقَوْلُ عَلَىٰٓ أَكْثَرِهِمْ فَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle, haƙĩƙa, kalma[1] tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّا جَعَلْنَا فِىٓ أَعْنَٰقِهِمْ أَغْلَٰلًا فَهِىَ إِلَى ٱلْأَذْقَانِ فَهُم مُّقْمَحُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَعَلْنَا مِنۢ بَيْنِ أَيْدِيهِمْ سَدًّا وَمِنْ خَلْفِهِمْ سَدًّا فَأَغْشَيْنَٰهُمْ فَهُمْ لَا يُبْصِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَسَوَآءٌ عَلَيْهِمْ ءَأَنذَرْتَهُمْ أَمْ لَمْ تُنذِرْهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّمَا تُنذِرُ مَنِ ٱتَّبَعَ ٱلذِّكْرَ وَخَشِىَ ٱلرَّحْمَٰنَ بِٱلْغَيْبِ فَبَشِّرْهُ بِمَغْفِرَةٍ وَأَجْرٍ كَرِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّا نَحْنُ نُحْىِ ٱلْمَوْتَىٰ وَنَكْتُبُ مَا قَدَّمُوا۟ وَءَاثَٰرَهُمْ وَكُلَّ شَىْءٍ أَحْصَيْنَٰهُ فِىٓ إِمَامٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱضْرِبْ لَهُم مَّثَلًا أَصْحَٰبَ ٱلْقَرْيَةِ إِذْ جَآءَهَا ٱلْمُرْسَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni[1] suka jẽ mata.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِذْ أَرْسَلْنَآ إِلَيْهِمُ ٱثْنَيْنِ فَكَذَّبُوهُمَا فَعَزَّزْنَا بِثَالِثٍ فَقَالُوٓا۟ إِنَّآ إِلَيْكُم مُّرْسَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوا۟ مَآ أَنتُمْ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا وَمَآ أَنزَلَ ٱلرَّحْمَٰنُ مِن شَىْءٍ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا تَكْذِبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوا۟ رَبُّنَا يَعْلَمُ إِنَّآ إِلَيْكُمْ لَمُرْسَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا عَلَيْنَآ إِلَّا ٱلْبَلَٰغُ ٱلْمُبِينُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوٓا۟ إِنَّا تَطَيَّرْنَا بِكُمْ لَئِن لَّمْ تَنتَهُوا۟ لَنَرْجُمَنَّكُمْ وَلَيَمَسَّنَّكُم مِّنَّا عَذَابٌ أَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوا۟ طَٰٓئِرُكُم مَّعَكُمْ أَئِن ذُكِّرْتُم بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ مُّسْرِفُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَآءَ مِنْ أَقْصَا ٱلْمَدِينَةِ رَجُلٌ يَسْعَىٰ قَالَ يَٰقَوْمِ ٱتَّبِعُوا۟ ٱلْمُرْسَلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱتَّبِعُوا۟ مَن لَّا يَسْـَٔلُكُمْ أَجْرًا وَهُم مُّهْتَدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا لِىَ لَآ أَعْبُدُ ٱلَّذِى فَطَرَنِى وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ءَأَتَّخِذُ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةً إِن يُرِدْنِ ٱلرَّحْمَٰنُ بِضُرٍّ لَّا تُغْنِ عَنِّى شَفَٰعَتُهُمْ شَيْـًٔا وَلَا يُنقِذُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنِّىٓ إِذًا لَّفِى ضَلَٰلٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنِّىٓ ءَامَنتُ بِرَبِّكُمْ فَٱسْمَعُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قِيلَ ٱدْخُلِ ٱلْجَنَّةَ قَالَ يَٰلَيْتَ قَوْمِى يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAka ce [1](masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

بِمَا غَفَرَ لِى رَبِّى وَجَعَلَنِى مِنَ ٱلْمُكْرَمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَنزَلْنَا عَلَىٰ قَوْمِهِۦ مِنۢ بَعْدِهِۦ مِن جُندٍ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا كُنَّا مُنزِلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama[1] a kan (halaka) mutãnensa, daga bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِن كَانَتْ إِلَّا صَيْحَةً وَٰحِدَةً فَإِذَا هُمْ خَٰمِدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَٰحَسْرَةً عَلَى ٱلْعِبَادِ مَا يَأْتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã nadãma a kan bãyĩ Na! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَمْ يَرَوْا۟ كَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّنَ ٱلْقُرُونِ أَنَّهُمْ إِلَيْهِمْ لَا يَرْجِعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutãnen) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa su bã zã su kõmo ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِن كُلٌّ لَّمَّا جَمِيعٌ لَّدَيْنَا مُحْضَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurin Mu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَءَايَةٌ لَّهُمُ ٱلْأَرْضُ ٱلْمَيْتَةُ أَحْيَيْنَٰهَا وَأَخْرَجْنَا مِنْهَا حَبًّا فَمِنْهُ يَأْكُلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ãyã ce a gare su: ¡asã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَعَلْنَا فِيهَا جَنَّٰتٍ مِّن نَّخِيلٍ وَأَعْنَٰبٍ وَفَجَّرْنَا فِيهَا مِنَ ٱلْعُيُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka sanya, a cikinta (ƙasã), waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِيَأْكُلُوا۟ مِن ثَمَرِهِۦ وَمَا عَمِلَتْهُ أَيْدِيهِمْ أَفَلَا يَشْكُرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bã zã su gõdẽ ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

سُبْحَٰنَ ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلْأَزْوَٰجَ كُلَّهَا مِمَّا تُنۢبِتُ ٱلْأَرْضُ وَمِنْ أَنفُسِهِمْ وَمِمَّا لَا يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَءَايَةٌ لَّهُمُ ٱلَّيْلُ نَسْلَخُ مِنْهُ ٱلنَّهَارَ فَإِذَا هُم مُّظْلِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu shiga duhu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلشَّمْسُ تَجْرِى لِمُسْتَقَرٍّ لَّهَا ذَٰلِكَ تَقْدِيرُ ٱلْعَزِيزِ ٱلْعَلِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْقَمَرَ قَدَّرْنَٰهُ مَنَازِلَ حَتَّىٰ عَادَ كَٱلْعُرْجُونِ ٱلْقَدِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَا ٱلشَّمْسُ يَنۢبَغِى لَهَآ أَن تُدْرِكَ ٱلْقَمَرَ وَلَا ٱلَّيْلُ سَابِقُ ٱلنَّهَارِ وَكُلٌّ فِى فَلَكٍ يَسْبَحُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَءَايَةٌ لَّهُمْ أَنَّا حَمَلْنَا ذُرِّيَّتَهُمْ فِى ٱلْفُلْكِ ٱلْمَشْحُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ãyã ce a gare su. Lalle Mũ, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lõdi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَخَلَقْنَا لَهُم مِّن مِّثْلِهِۦ مَا يَرْكَبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِن نَّشَأْ نُغْرِقْهُمْ فَلَا صَرِيخَ لَهُمْ وَلَا هُمْ يُنقَذُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan Mun so, zã Mu nutsar da su, har bãbu kururuwar neman ãgaji, a gare su, kuma ba su zama anã tsirar da su ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَّا رَحْمَةً مِّنَّا وَمَتَٰعًا إِلَىٰ حِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa dãɗi zuwa ga wani ɗan lõkaci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّقُوا۟ مَا بَيْنَ أَيْدِيكُمْ وَمَا خَلْفَكُمْ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan aka ce musu, "Ku kãre abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a bãyanku, dõmin tsammãninku a ji tausayinku."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا تَأْتِيهِم مِّنْ ءَايَةٍ مِّنْ ءَايَٰتِ رَبِّهِمْ إِلَّا كَانُوا۟ عَنْهَا مُعْرِضِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wata ãyã daga ãyõyin Ubangijinsu bã ta zuwa a gare su, sai sun kasance sunã mãsu bijirẽwa daga gare ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ أَنفِقُوا۟ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ قَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لِلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَنُطْعِمُ مَن لَّوْ يَشَآءُ ٱللَّهُ أَطْعَمَهُۥٓ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا فِى ضَلَٰلٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan aka ce musu, "Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku," sai waɗanda suka kãfirta su ce ga waɗanda suka yi ĩmãni, "Ashe, zã mu ciyar da wanda idan Allah Ya so Yanã ciyar da shi? Ba ku zama ba fãce a cikin ɓata bayyananniya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَٰدِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi yake (aukuwa) idan kun kasance mãsu gaskiya?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَا يَنظُرُونَ إِلَّا صَيْحَةً وَٰحِدَةً تَأْخُذُهُمْ وَهُمْ يَخِصِّمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã su jiran (kõme) fãce wata tsãwa guda, zã ta kãma su, alhãli kuwa sunã yin husũma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَا يَسْتَطِيعُونَ تَوْصِيَةً وَلَآ إِلَىٰٓ أَهْلِهِمْ يَرْجِعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã zã su iya yin wasiyya[1] ba, kuma bã zã su iya kõmãwa zuwa ga iyãlansu ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَنُفِخَ فِى ٱلصُّورِ فَإِذَا هُم مِّنَ ٱلْأَجْدَاثِ إِلَىٰ رَبِّهِمْ يَنسِلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gã su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, sunã ta gudu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوا۟ يَٰوَيْلَنَا مَنۢ بَعَثَنَا مِن مَّرْقَدِنَا هَٰذَا مَا وَعَدَ ٱلرَّحْمَٰنُ وَصَدَقَ ٱلْمُرْسَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Yã bonenmu! Wãne ne ya tãyar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِن كَانَتْ إِلَّا صَيْحَةً وَٰحِدَةً فَإِذَا هُمْ جَمِيعٌ لَّدَيْنَا مُحْضَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa ta kasance ba fãce wata tsãwa ce guda, sai gã su duka, sunã abin halartarwa a gare Mu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱلْيَوْمَ لَا تُظْلَمُ نَفْسٌ شَيْـًٔا وَلَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, a yau, bã zã a zãlunci wani rai da kõme ba. Kuma bã zã a sãkã muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ أَصْحَٰبَ ٱلْجَنَّةِ ٱلْيَوْمَ فِى شُغُلٍ فَٰكِهُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هُمْ وَأَزْوَٰجُهُمْ فِى ظِلَٰلٍ عَلَى ٱلْأَرَآئِكِ مُتَّكِـُٔونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَهُمْ فِيهَا فَٰكِهَةٌ وَلَهُم مَّا يَدَّعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

سَلَٰمٌ قَوْلًا مِّن رَّبٍّ رَّحِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Aminci," da magana,[1] daga Ubangiji Mai jin ƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱمْتَٰزُوا۟ ٱلْيَوْمَ أَيُّهَا ٱلْمُجْرِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَمْ أَعْهَدْ إِلَيْكُمْ يَٰبَنِىٓ ءَادَمَ أَن لَّا تَعْبُدُوا۟ ٱلشَّيْطَٰنَ إِنَّهُۥ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنِ ٱعْبُدُونِى هَٰذَا صِرَٰطٌ مُّسْتَقِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ أَضَلَّ مِنكُمْ جِبِلًّا كَثِيرًا أَفَلَمْ تَكُونُوا۟ تَعْقِلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هَٰذِهِۦ جَهَنَّمُ ٱلَّتِى كُنتُمْ تُوعَدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱصْلَوْهَا ٱلْيَوْمَ بِمَا كُنتُمْ تَكْفُرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلْيَوْمَ نَخْتِمُ عَلَىٰٓ أَفْوَٰهِهِمْ وَتُكَلِّمُنَآ أَيْدِيهِمْ وَتَشْهَدُ أَرْجُلُهُم بِمَا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَوْ نَشَآءُ لَطَمَسْنَا عَلَىٰٓ أَعْيُنِهِمْ فَٱسْتَبَقُوا۟ ٱلصِّرَٰطَ فَأَنَّىٰ يُبْصِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDã Mun so, dã Mun shãfe gani [1]daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَوْ نَشَآءُ لَمَسَخْنَٰهُمْ عَلَىٰ مَكَانَتِهِمْ فَمَا ٱسْتَطَٰعُوا۟ مُضِيًّا وَلَا يَرْجِعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَن نُّعَمِّرْهُ نُنَكِّسْهُ فِى ٱلْخَلْقِ أَفَلَا يَعْقِلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su hankalta?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا عَلَّمْنَٰهُ ٱلشِّعْرَ وَمَا يَنۢبَغِى لَهُۥٓ إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ وَقُرْءَانٌ مُّبِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa Mu sanar da shi (Annabi) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِّيُنذِرَ مَن كَانَ حَيًّا وَيَحِقَّ ٱلْقَوْلُ عَلَى ٱلْكَٰفِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kãfirai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَوَلَمْ يَرَوْا۟ أَنَّا خَلَقْنَا لَهُم مِّمَّا عَمِلَتْ أَيْدِينَآ أَنْعَٰمًا فَهُمْ لَهَا مَٰلِكُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, ba su gani ba (cẽwa) lalle Mun halitta musu dabbõbi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai sunã mallakar su?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَذَلَّلْنَٰهَا لَهُمْ فَمِنْهَا رَكُوبُهُمْ وَمِنْهَا يَأْكُلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka hõre su, sabõda su, sabõda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَهُمْ فِيهَا مَنَٰفِعُ وَمَشَارِبُ أَفَلَا يَشْكُرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma sunã da waɗansu amfãnõni a cikinsu, da abũbuwan shã. Ashe fa, bã zã; su gõdẽ ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱتَّخَذُوا۟ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةً لَّعَلَّهُمْ يُنصَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa wanin Allah, ɗammãninsu zã su taimake su.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَا يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَهُمْ وَهُمْ لَهُمْ جُندٌ مُّحْضَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã zã su iya taimakonsu ba, alhãli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa (a cikin wutã).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَا يَحْزُنكَ قَوْلُهُمْ إِنَّا نَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, kada maganarsu ta ɓãta maka rai. Lalle Mũ, Munã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَوَلَمْ يَرَ ٱلْإِنسَٰنُ أَنَّا خَلَقْنَٰهُ مِن نُّطْفَةٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٌ مُّبِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, kuma mutum bai ga (cẽwa) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gã shi mai yawan husũma, mai bayyanãwar husũmar.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَضَرَبَ لَنَا مَثَلًا وَنَسِىَ خَلْقَهُۥ قَالَ مَن يُحْىِ ٱلْعِظَٰمَ وَهِىَ رَمِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wãne ne ke rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ يُحْيِيهَا ٱلَّذِىٓ أَنشَأَهَآ أَوَّلَ مَرَّةٍ وَهُوَ بِكُلِّ خَلْقٍ عَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلشَّجَرِ ٱلْأَخْضَرِ نَارًا فَإِذَآ أَنتُم مِّنْهُ تُوقِدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare shi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَوَلَيْسَ ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يَخْلُقَ مِثْلَهُم بَلَىٰ وَهُوَ ٱلْخَلَّٰقُ ٱلْعَلِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne, Mai ilmi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّمَآ أَمْرُهُۥٓ إِذَآ أَرَادَ شَيْـًٔا أَن يَقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiUmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَسُبْحَٰنَ ٱلَّذِى بِيَدِهِۦ مَلَكُوتُ كُلِّ شَىْءٍ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70