Shafin farko › Surori › Suratu Saad
Suratu Saad ص
Ayoyi 88 · Makka · tsarin saukarwa 38
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ صٓ وَٱلْقُرْءَانِ ذِى ٱلذِّكْرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni mai hukunce-hukunce.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فِى عِزَّةٍ وَشِقَاقٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ã'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al'ãdunsu) da sãɓãni (tsakãnin jũnansu).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَمْ أَهْلَكْنَا مِن قَبْلِهِم مِّن قَرْنٍ فَنَادَوا۟ وَّلَاتَ حِينَ مَنَاصٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu lõkacin kuɓucewa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَعَجِبُوٓا۟ أَن جَآءَهُم مُّنذِرٌ مِّنْهُمْ وَقَالَ ٱلْكَٰفِرُونَ هَٰذَا سَٰحِرٌ كَذَّابٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَجَعَلَ ٱلْـَٔالِهَةَ إِلَٰهًا وَٰحِدًا إِنَّ هَٰذَا لَشَىْءٌ عُجَابٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱنطَلَقَ ٱلْمَلَأُ مِنْهُمْ أَنِ ٱمْشُوا۟ وَٱصْبِرُوا۟ عَلَىٰٓ ءَالِهَتِكُمْ إِنَّ هَٰذَا لَشَىْءٌ يُرَادُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَا سَمِعْنَا بِهَٰذَا فِى ٱلْمِلَّةِ ٱلْـَٔاخِرَةِ إِنْ هَٰذَآ إِلَّا ٱخْتِلَٰقٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَءُنزِلَ عَلَيْهِ ٱلذِّكْرُ مِنۢ بَيْنِنَا بَلْ هُمْ فِى شَكٍّ مِّن ذِكْرِى بَل لَّمَّا يَذُوقُوا۟ عَذَابِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ عِندَهُمْ خَزَآئِنُ رَحْمَةِ رَبِّكَ ٱلْعَزِيزِ ٱلْوَهَّابِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ لَهُم مُّلْكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا فَلْيَرْتَقُوا۟ فِى ٱلْأَسْبَٰبِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
جُندٌ مَّا هُنَالِكَ مَهْزُومٌ مِّنَ ٱلْأَحْزَابِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَعَادٌ وَفِرْعَوْنُ ذُو ٱلْأَوْتَادِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka kafe mulkinsa).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَثَمُودُ وَقَوْمُ لُوطٍ وَأَصْحَٰبُ لْـَٔيْكَةِ أُو۟لَٰٓئِكَ ٱلْأَحْزَابُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, [1]waɗancan ne ƙungiyõyin.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِن كُلٌّ إِلَّا كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ عِقَابِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا يَنظُرُ هَٰٓؤُلَآءِ إِلَّا صَيْحَةً وَٰحِدَةً مَّا لَهَا مِن فَوَاقٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma waɗannan [1]bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَالُوا۟ رَبَّنَا عَجِّل لَّنَا قِطَّنَا قَبْلَ يَوْمِ ٱلْحِسَابِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike."[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَٱذْكُرْ عَبْدَنَا دَاوُۥدَ ذَا ٱلْأَيْدِ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwan Mu Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا سَخَّرْنَا ٱلْجِبَالَ مَعَهُۥ يُسَبِّحْنَ بِٱلْعَشِىِّ وَٱلْإِشْرَاقِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar rãnã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلطَّيْرَ مَحْشُورَةً كُلٌّ لَّهُۥٓ أَوَّابٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَشَدَدْنَا مُلْكَهُۥ وَءَاتَيْنَٰهُ ٱلْحِكْمَةَ وَفَصْلَ ٱلْخِطَابِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima[1] da rarrabẽwar magana.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَهَلْ أَتَىٰكَ نَبَؤُا۟ ٱلْخَصْمِ إِذْ تَسَوَّرُوا۟ ٱلْمِحْرَابَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun masallaci?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ دَخَلُوا۟ عَلَىٰ دَاوُۥدَ فَفَزِعَ مِنْهُمْ قَالُوا۟ لَا تَخَفْ خَصْمَانِ بَغَىٰ بَعْضُنَا عَلَىٰ بَعْضٍ فَٱحْكُم بَيْنَنَا بِٱلْحَقِّ وَلَا تُشْطِطْ وَٱهْدِنَآ إِلَىٰ سَوَآءِ ٱلصِّرَٰطِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ هَٰذَآ أَخِى لَهُۥ تِسْعٌ وَتِسْعُونَ نَعْجَةً وَلِىَ نَعْجَةٌ وَٰحِدَةٌ فَقَالَ أَكْفِلْنِيهَا وَعَزَّنِى فِى ٱلْخِطَابِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ لَقَدْ ظَلَمَكَ بِسُؤَالِ نَعْجَتِكَ إِلَىٰ نِعَاجِهِۦ وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ ٱلْخُلَطَآءِ لَيَبْغِى بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَقَلِيلٌ مَّا هُمْ وَظَنَّ دَاوُۥدُ أَنَّمَا فَتَنَّٰهُ فَٱسْتَغْفَرَ رَبَّهُۥ وَخَرَّ رَاكِعًا وَأَنَابَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce[1] ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai." Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara, kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَغَفَرْنَا لَهُۥ ذَٰلِكَ وَإِنَّ لَهُۥ عِندَنَا لَزُلْفَىٰ وَحُسْنَ مَـَٔابٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka Muka gãfarta masa wancan, kuma lalle yanã da wata kusantar daraja a wurin Mu, da kyaun makõma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَٰدَاوُۥدُ إِنَّا جَعَلْنَٰكَ خَلِيفَةً فِى ٱلْأَرْضِ فَٱحْكُم بَيْنَ ٱلنَّاسِ بِٱلْحَقِّ وَلَا تَتَّبِعِ ٱلْهَوَىٰ فَيُضِلَّكَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَضِلُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ لَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌۢ بِمَا نَسُوا۟ يَوْمَ ٱلْحِسَابِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Yã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا خَلَقْنَا ٱلسَّمَآءَ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا بَٰطِلًا ذَٰلِكَ ظَنُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنَ ٱلنَّارِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ نَجْعَلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ كَٱلْمُفْسِدِينَ فِى ٱلْأَرْضِ أَمْ نَجْعَلُ ٱلْمُتَّقِينَ كَٱلْفُجَّارِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كِتَٰبٌ أَنزَلْنَٰهُ إِلَيْكَ مُبَٰرَكٌ لِّيَدَّبَّرُوٓا۟ ءَايَٰتِهِۦ وَلِيَتَذَكَّرَ أُو۟لُوا۟ ٱلْأَلْبَٰبِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَوَهَبْنَا لِدَاوُۥدَ سُلَيْمَٰنَ نِعْمَ ٱلْعَبْدُ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn) mai mayar da al'amari ne ga Allah.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ عُرِضَ عَلَيْهِ بِٱلْعَشِىِّ ٱلصَّٰفِنَٰتُ ٱلْجِيَادُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, [1]a lõkacin maraice.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَقَالَ إِنِّىٓ أَحْبَبْتُ حُبَّ ٱلْخَيْرِ عَن ذِكْرِ رَبِّى حَتَّىٰ تَوَارَتْ بِٱلْحِجَابِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya ce: "Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã) ta faku da shãmaki!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
رُدُّوهَا عَلَىَّ فَطَفِقَ مَسْحًۢا بِٱلسُّوقِ وَٱلْأَعْنَاقِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu[1] da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ فَتَنَّا سُلَيْمَٰنَ وَأَلْقَيْنَا عَلَىٰ كُرْسِيِّهِۦ جَسَدًا ثُمَّ أَنَابَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini[1] Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ رَبِّ ٱغْفِرْ لِى وَهَبْ لِى مُلْكًا لَّا يَنۢبَغِى لِأَحَدٍ مِّنۢ بَعْدِىٓ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْوَهَّابُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna.[1] Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَخَّرْنَا لَهُ ٱلرِّيحَ تَجْرِى بِأَمْرِهِۦ رُخَآءً حَيْثُ أَصَابَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka Muka hõre masa iska[1] tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلشَّيَٰطِينَ كُلَّ بَنَّآءٍ وَغَوَّاصٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna.)
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَءَاخَرِينَ مُقَرَّنِينَ فِى ٱلْأَصْفَادِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا عَطَآؤُنَا فَٱمْنُنْ أَوْ أَمْسِكْ بِغَيْرِ حِسَابٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wannan kyautar Mu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ لَهُۥ عِندَنَا لَزُلْفَىٰ وَحُسْنَ مَـَٔابٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurin Mu da kyaun makõma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱذْكُرْ عَبْدَنَآ أَيُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّى مَسَّنِىَ ٱلشَّيْطَٰنُ بِنُصْبٍ وَعَذَابٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka ambaci bãwan Mu Ayyũba[1] a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱرْكُضْ بِرِجْلِكَ هَٰذَا مُغْتَسَلٌۢ بَارِدٌ وَشَرَابٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَوَهَبْنَا لَهُۥٓ أَهْلَهُۥ وَمِثْلَهُم مَّعَهُمْ رَحْمَةً مِّنَّا وَذِكْرَىٰ لِأُو۟لِى ٱلْأَلْبَٰبِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَخُذْ بِيَدِكَ ضِغْثًا فَٱضْرِب بِّهِۦ وَلَا تَحْنَثْ إِنَّا وَجَدْنَٰهُ صَابِرًا نِّعْمَ ٱلْعَبْدُ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al'amari ga Allah ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱذْكُرْ عِبَٰدَنَآ إِبْرَٰهِيمَ وَإِسْحَٰقَ وَيَعْقُوبَ أُو۟لِى ٱلْأَيْدِى وَٱلْأَبْصَٰرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka ambaci bãyin Mu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar umurnin Mu) da basĩra.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّآ أَخْلَصْنَٰهُم بِخَالِصَةٍ ذِكْرَى ٱلدَّارِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّهُمْ عِندَنَا لَمِنَ ٱلْمُصْطَفَيْنَ ٱلْأَخْيَارِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle sũ a wurin Mu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱذْكُرْ إِسْمَٰعِيلَ وَٱلْيَسَعَ وَذَا ٱلْكِفْلِ وَكُلٌّ مِّنَ ٱلْأَخْيَارِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا ذِكْرٌ وَإِنَّ لِلْمُتَّقِينَ لَحُسْنَ مَـَٔابٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
جَنَّٰتِ عَدْنٍ مُّفَتَّحَةً لَّهُمُ ٱلْأَبْوَٰبُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Gidãjen Aljannar zama, alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مُتَّكِـِٔينَ فِيهَا يَدْعُونَ فِيهَا بِفَٰكِهَةٍ كَثِيرَةٍ وَشَرَابٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَعِندَهُمْ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرْفِ أَتْرَابٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِيَوْمِ ٱلْحِسَابِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ هَٰذَا لَرِزْقُنَا مَا لَهُۥ مِن نَّفَادٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwar Mu ce, bã ta ƙãrẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا وَإِنَّ لِلطَّٰغِينَ لَشَرَّ مَـَٔابٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
جَهَنَّمَ يَصْلَوْنَهَا فَبِئْسَ ٱلْمِهَادُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا فَلْيَذُوقُوهُ حَمِيمٌ وَغَسَّاقٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَءَاخَرُ مِن شَكْلِهِۦٓ أَزْوَٰجٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wani daga siffarsa nau'i-nau'i.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا فَوْجٌ مُّقْتَحِمٌ مَّعَكُمْ لَا مَرْحَبًۢا بِهِمْ إِنَّهُمْ صَالُوا۟ ٱلنَّارِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ بَلْ أَنتُمْ لَا مَرْحَبًۢا بِكُمْ أَنتُمْ قَدَّمْتُمُوهُ لَنَا فَبِئْسَ ٱلْقَرَارُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ رَبَّنَا مَن قَدَّمَ لَنَا هَٰذَا فَزِدْهُ عَذَابًا ضِعْفًا فِى ٱلنَّارِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَالُوا۟ مَا لَنَا لَا نَرَىٰ رِجَالًا كُنَّا نَعُدُّهُم مِّنَ ٱلْأَشْرَارِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَتَّخَذْنَٰهُمْ سِخْرِيًّا أَمْ زَاغَتْ عَنْهُمُ ٱلْأَبْصَٰرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ ذَٰلِكَ لَحَقٌّ تَخَاصُمُ أَهْلِ ٱلنَّارِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قُلْ إِنَّمَآ أَنَا۠ مُنذِرٌ وَمَا مِنْ إِلَٰهٍ إِلَّا ٱللَّهُ ٱلْوَٰحِدُ ٱلْقَهَّارُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka ce: "Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ٱلْعَزِيزُ ٱلْغَفَّٰرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قُلْ هُوَ نَبَؤٌا۟ عَظِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka ce: "Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma".
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَنتُمْ عَنْهُ مُعْرِضُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَا كَانَ لِىَ مِنْ عِلْمٍۭ بِٱلْمَلَإِ ٱلْأَعْلَىٰٓ إِذْ يَخْتَصِمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (malã'iku) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِن يُوحَىٰٓ إِلَىَّ إِلَّآ أَنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَٰٓئِكَةِ إِنِّى خَٰلِقٌۢ بَشَرًا مِّن طِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, "Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِذَا سَوَّيْتُهُۥ وَنَفَخْتُ فِيهِ مِن رُّوحِى فَقَعُوا۟ لَهُۥ سَٰجِدِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga Ruhĩ Na a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَجَدَ ٱلْمَلَٰٓئِكَةُ كُلُّهُمْ أَجْمَعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّآ إِبْلِيسَ ٱسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنَ ٱلْكَٰفِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ يَٰٓإِبْلِيسُ مَا مَنَعَكَ أَن تَسْجُدَ لِمَا خَلَقْتُ بِيَدَىَّ أَسْتَكْبَرْتَ أَمْ كُنتَ مِنَ ٱلْعَالِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Allah) Ya ce, "Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ أَنَا۠ خَيْرٌ مِّنْهُ خَلَقْتَنِى مِن نَّارٍ وَخَلَقْتَهُۥ مِن طِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce, "Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ فَٱخْرُجْ مِنْهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce, "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ عَلَيْكَ لَعْنَتِىٓ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ رَبِّ فَأَنظِرْنِىٓ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce, "Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ ٱلْمُنظَرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce, "To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْوَقْتِ ٱلْمَعْلُومِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Zuwa ga yinin lõkaci sananne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ فَبِعِزَّتِكَ لَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce, "To, inã rantsuwa da buwãyar Ka, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا عِبَادَكَ مِنْهُمُ ٱلْمُخْلَصِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Fãce bãyin Ka tsarkakakku daga gare su."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ فَٱلْحَقُّ وَٱلْحَقَّ أَقُولُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Allah) Ya ce, "To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَأَمْلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكَ وَمِمَّن تَبِعَكَ مِنْهُمْ أَجْمَعِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su, gabã ɗaya"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قُلْ مَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلْمُتَكَلِّفِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen faɗarsa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shĩ (Alkur'ãn) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَتَعْلَمُنَّ نَبَأَهُۥ بَعْدَ حِينٍۭ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa[1] a bayan ɗan lõkaci."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu As-Saaffaat
Suratu Az-Zumar →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.