Shafin farko › Surori › Suratu Al-Qamar
Suratu Al-Qamar القمر
Ayoyi 55 · Makka · tsarin saukarwa 37
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ ٱقْتَرَبَتِ ٱلسَّاعَةُ وَٱنشَقَّ ٱلْقَمَرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sã'a ta yi kusa, kuma wata [1]ya tsãge.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِن يَرَوْا۟ ءَايَةً يُعْرِضُوا۟ وَيَقُولُوا۟ سِحْرٌ مُّسْتَمِرٌّ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكَذَّبُوا۟ وَٱتَّبَعُوٓا۟ أَهْوَآءَهُمْ وَكُلُّ أَمْرٍ مُّسْتَقِرٌّ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ جَآءَهُم مِّنَ ٱلْأَنۢبَآءِ مَا فِيهِ مُزْدَجَرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
حِكْمَةٌۢ بَٰلِغَةٌ فَمَا تُغْنِ ٱلنُّذُرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَتَوَلَّ عَنْهُمْ يَوْمَ يَدْعُ ٱلدَّاعِ إِلَىٰ شَىْءٍ نُّكُرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
خُشَّعًا أَبْصَٰرُهُمْ يَخْرُجُونَ مِنَ ٱلْأَجْدَاثِ كَأَنَّهُمْ جَرَادٌ مُّنتَشِرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مُّهْطِعِينَ إِلَى ٱلدَّاعِ يَقُولُ ٱلْكَٰفِرُونَ هَٰذَا يَوْمٌ عَسِرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ فَكَذَّبُوا۟ عَبْدَنَا وَقَالُوا۟ مَجْنُونٌ وَٱزْدُجِرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata Bawan Mu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنِّى مَغْلُوبٌ فَٱنتَصِرْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَفَتَحْنَآ أَبْوَٰبَ ٱلسَّمَآءِ بِمَآءٍ مُّنْهَمِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفَجَّرْنَا ٱلْأَرْضَ عُيُونًا فَٱلْتَقَى ٱلْمَآءُ عَلَىٰٓ أَمْرٍ قَدْ قُدِرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umarni da aka riga aka ƙaddara shi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَحَمَلْنَٰهُ عَلَىٰ ذَاتِ أَلْوَٰحٍ وَدُسُرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
تَجْرِى بِأَعْيُنِنَا جَزَآءً لِّمَن كَانَ كُفِرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Tanã gudãna, a kan idãnun Mu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَد تَّرَكْنَٰهَآ ءَايَةً فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِى وَنُذُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, yãyã azãbã Ta take da gargaɗi Na?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ يَسَّرْنَا ٱلْقُرْءَانَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَتْ عَادٌ فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِى وَنُذُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗi Na?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّآ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِيحًا صَرْصَرًا فِى يَوْمِ نَحْسٍ مُّسْتَمِرٍّ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
تَنزِعُ ٱلنَّاسَ كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ مُّنقَعِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِى وَنُذُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, yãya azãbã Ta take da gargaɗi Na?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ يَسَّرْنَا ٱلْقُرْءَانَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِٱلنُّذُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَقَالُوٓا۟ أَبَشَرًا مِّنَّا وَٰحِدًا نَّتَّبِعُهُۥٓ إِنَّآ إِذًا لَّفِى ضَلَٰلٍ وَسُعُرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَءُلْقِىَ ٱلذِّكْرُ عَلَيْهِ مِنۢ بَيْنِنَا بَلْ هُوَ كَذَّابٌ أَشِرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَيَعْلَمُونَ غَدًا مَّنِ ٱلْكَذَّابُ ٱلْأَشِرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا مُرْسِلُوا۟ ٱلنَّاقَةِ فِتْنَةً لَّهُمْ فَٱرْتَقِبْهُمْ وَٱصْطَبِرْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar[1] ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنَبِّئْهُمْ أَنَّ ٱلْمَآءَ قِسْمَةٌۢ بَيْنَهُمْ كُلُّ شِرْبٍ مُّحْتَضَرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَنَادَوْا۟ صَاحِبَهُمْ فَتَعَاطَىٰ فَعَقَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِى وَنُذُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, yãya azãbaTa take da gargaɗi Na?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّآ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ صَيْحَةً وَٰحِدَةً فَكَانُوا۟ كَهَشِيمِ ٱلْمُحْتَظِرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ يَسَّرْنَا ٱلْقُرْءَانَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍۭ بِٱلنُّذُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّآ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ حَاصِبًا إِلَّآ ءَالَ لُوطٍ نَّجَّيْنَٰهُم بِسَحَرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
نِّعْمَةً مِّنْ عِندِنَا كَذَٰلِكَ نَجْزِى مَن شَكَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ أَنذَرَهُم بَطْشَتَنَا فَتَمَارَوْا۟ بِٱلنُّذُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙar Mu, sai suka yi musu game da gargaɗin.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ رَٰوَدُوهُ عَن ضَيْفِهِۦ فَطَمَسْنَآ أَعْيُنَهُمْ فَذُوقُوا۟ عَذَابِى وَنُذُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩ Na."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ صَبَّحَهُم بُكْرَةً عَذَابٌ مُّسْتَقِرٌّ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَذُوقُوا۟ عَذَابِى وَنُذُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩ Na.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ يَسَّرْنَا ٱلْقُرْءَانَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ جَآءَ ءَالَ فِرْعَوْنَ ٱلنُّذُرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَٰتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذْنَٰهُمْ أَخْذَ عَزِيزٍ مُّقْتَدِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sun ƙaryata game da ãyõyin Mu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَكُفَّارُكُمْ خَيْرٌ مِّنْ أُو۟لَٰٓئِكُمْ أَمْ لَكُم بَرَآءَةٌ فِى ٱلزُّبُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ يَقُولُونَ نَحْنُ جَمِيعٌ مُّنتَصِرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَيُهْزَمُ ٱلْجَمْعُ وَيُوَلُّونَ ٱلدُّبُرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Zã a karya[1] tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلِ ٱلسَّاعَةُ مَوْعِدُهُمْ وَٱلسَّاعَةُ أَدْهَىٰ وَأَمَرُّ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ ٱلْمُجْرِمِينَ فِى ضَلَٰلٍ وَسُعُرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَوْمَ يُسْحَبُونَ فِى ٱلنَّارِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمْ ذُوقُوا۟ مَسَّ سَقَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا كُلَّ شَىْءٍ خَلَقْنَٰهُ بِقَدَرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَمْرُنَآ إِلَّا وَٰحِدَةٌ كَلَمْحٍۭ بِٱلْبَصَرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma umurnin Mu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ أَهْلَكْنَآ أَشْيَاعَكُمْ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكُلُّ شَىْءٍ فَعَلُوهُ فِى ٱلزُّبُرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكُلُّ صَغِيرٍ وَكَبِيرٍ مُّسْتَطَرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى جَنَّٰتٍ وَنَهَرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِى مَقْعَدِ صِدْقٍ عِندَ مَلِيكٍ مُّقْتَدِرٍۭ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu An-Najm
Suratu Ar-Rahmaan →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.