caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu An-Najm النجم

Ayoyi 62 · Makka · tsarin saukarwa 23

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلنَّجْمِ إِذَا هَوَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiInã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمْ وَمَا غَوَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMa'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلْهَوَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْىٌ يُوحَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلْقُوَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi [1]ya sanar da shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ذُو مِرَّةٍ فَٱسْتَوَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMa'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَهُوَ بِٱلْأُفُقِ ٱلْأَعْلَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAlhãli kuwa yanã a sararin samã mafi daukaka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiHar ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَوْحَىٰٓ إِلَىٰ عَبْدِهِۦ مَآ أَوْحَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَا كَذَبَ ٱلْفُؤَادُ مَا رَأَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiZũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَفَتُمَٰرُونَهُۥ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ رَءَاهُ نَزْلَةً أُخْرَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عِندَ سِدْرَةِ ٱلْمُنتَهَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA wurin da magaryar tuƙẽwa take.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عِندَهَا جَنَّةُ ٱلْمَأْوَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA inda taken, nan Aljannar makoma take.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِذْ يَغْشَى ٱلسِّدْرَةَ مَا يَغْشَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَا زَاغَ ٱلْبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiGaninsa[1] bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَقَدْ رَأَىٰ مِنْ ءَايَٰتِ رَبِّهِ ٱلْكُبْرَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma[1] daga ãyõyin Ubangijinsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَفَرَءَيْتُمُ ٱللَّٰتَ وَٱلْعُزَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, kun ga Lãta da uzza?[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَنَوٰةَ ٱلثَّالِثَةَ ٱلْأُخْرَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَكُمُ ٱلذَّكَرُ وَلَهُ ٱلْأُنثَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تِلْكَ إِذًا قِسْمَةٌ ضِيزَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWannan fa ya zama rabo naƙasasshe.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنْ هِىَ إِلَّآ أَسْمَآءٌ سَمَّيْتُمُوهَآ أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلْطَٰنٍ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهْوَى ٱلْأَنفُسُ وَلَقَدْ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلْهُدَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar[1] ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ لِلْإِنسَٰنِ مَا تَمَنَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKo (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلِلَّهِ ٱلْـَٔاخِرَةُ وَٱلْأُولَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَكَم مِّن مَّلَكٍ فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ لَا تُغْنِى شَفَٰعَتُهُمْ شَيْـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعْدِ أَن يَأْذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرْضَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAkwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ لَيُسَمُّونَ ٱلْمَلَٰٓئِكَةَ تَسْمِيَةَ ٱلْأُنثَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنْ عِلْمٍ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغْنِى مِنَ ٱلْحَقِّ شَيْـًٔا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَعْرِضْ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكْرِنَا وَلَمْ يُرِدْ إِلَّا ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambaton Mu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ذَٰلِكَ مَبْلَغُهُم مِّنَ ٱلْعِلْمِ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ ٱهْتَدَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلِلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ لِيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ أَسَٰٓـُٔوا۟ بِمَا عَمِلُوا۟ وَيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ أَحْسَنُوا۟ بِٱلْحُسْنَى

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَٰٓئِرَ ٱلْإِثْمِ وَٱلْفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلْمَغْفِرَةِ هُوَ أَعْلَمُ بِكُمْ إِذْ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ وَإِذْ أَنتُمْ أَجِنَّةٌ فِى بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمْ فَلَا تُزَكُّوٓا۟ أَنفُسَكُمْ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake[1] kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَفَرَءَيْتَ ٱلَّذِى تَوَلَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, ka ga wannan da ya jũya baya?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَعْطَىٰ قَلِيلًا وَأَكْدَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَعِندَهُۥ عِلْمُ ٱلْغَيْبِ فَهُوَ يَرَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ لَمْ يُنَبَّأْ بِمَا فِى صُحُفِ مُوسَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKo kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِبْرَٰهِيمَ ٱلَّذِى وَفَّىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiCẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَن لَّيْسَ لِلْإِنسَٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنَّ سَعْيَهُۥ سَوْفَ يُرَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, aikinsa zã a gan shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ يُجْزَىٰهُ ٱلْجَزَآءَ ٱلْأَوْفَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلْمُنتَهَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضْحَكَ وَأَبْكَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحْيَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوْجَيْنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مِن نُّطْفَةٍ إِذَا تُمْنَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDaga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنَّ عَلَيْهِ ٱلنَّشْأَةَ ٱلْأُخْرَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغْنَىٰ وَأَقْنَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعْرَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنَّهُۥٓ أَهْلَكَ عَادًا ٱلْأُولَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَثَمُودَا۟ فَمَآ أَبْقَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ هُمْ أَظْلَمَ وَأَطْغَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْمُؤْتَفِكَةَ أَهْوَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa waɗanda aka birkice [1]ƙasarsu, Ya kãyar da su.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake [1]yin shakka?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هَٰذَا نَذِيرٌ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلْأُولَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumiwannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَزِفَتِ ٱلْـَٔازِفَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMakusanciya[1] fa, tã yi kusa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَيْسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَفَمِنْ هَٰذَا ٱلْحَدِيثِ تَعْجَبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, kuma daga wannan [1]lãbãri kuke mãmãki?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَتَضْحَكُونَ وَلَا تَبْكُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنتُمْ سَٰمِدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAlhãli kunã mãsu wãsã?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱسْجُدُوا۟ لِلَّهِ وَٱعْبُدُوا۟

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, ku yi tawãli'u [1]ga Allah, kuma ku bauta (masa).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70