caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Hijr الحجر

Ayoyi 99 · Makka · tsarin saukarwa 54

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ الٓر تِلْكَ ءَايَٰتُ ٱلْكِتَٰبِ وَقُرْءَانٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA. L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

رُّبَمَا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَوْ كَانُوا۟ مُسْلِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ذَرْهُمْ يَأْكُلُوا۟ وَيَتَمَتَّعُوا۟ وَيُلْهِهِمُ ٱلْأَمَلُ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍ إِلَّا وَلَهَا كِتَابٌ مَّعْلُومٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَّا تَسْبِقُ مِنْ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسْتَـْٔخِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالُوا۟ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِى نُزِّلَ عَلَيْهِ ٱلذِّكْرُ إِنَّكَ لَمَجْنُونٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَّوْ مَا تَأْتِينَا بِٱلْمَلَٰٓئِكَةِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَا نُنَزِّلُ ٱلْمَلَٰٓئِكَةَ إِلَّا بِٱلْحَقِّ وَمَا كَانُوٓا۟ إِذًا مُّنظَرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,[1] bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا ٱلذِّكْرَ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ فِى شِيَعِ ٱلْأَوَّلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãnin ka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا يَأْتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَذَٰلِكَ نَسْلُكُهُۥ فِى قُلُوبِ ٱلْمُجْرِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKamar wancan ne Muke shigar da shi[1] a cikin zukãtan mãsu laifi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَا يُؤْمِنُونَ بِهِۦ وَقَدْ خَلَتْ سُنَّةُ ٱلْأَوَّلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige[1] .

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَوْ فَتَحْنَا عَلَيْهِم بَابًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فَظَلُّوا۟ فِيهِ يَعْرُجُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَقَالُوٓا۟ إِنَّمَا سُكِّرَتْ أَبْصَٰرُنَا بَلْ نَحْنُ قَوْمٌ مَّسْحُورُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ جَعَلْنَا فِى ٱلسَّمَآءِ بُرُوجًا وَزَيَّنَّٰهَا لِلنَّٰظِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَحَفِظْنَٰهَا مِن كُلِّ شَيْطَٰنٍ رَّجِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَّا مَنِ ٱسْتَرَقَ ٱلسَّمْعَ فَأَتْبَعَهُۥ شِهَابٌ مُّبِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiFãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْأَرْضَ مَدَدْنَٰهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَٰسِىَ وَأَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ شَىْءٍ مَّوْزُونٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَٰيِشَ وَمَن لَّسْتُمْ لَهُۥ بِرَٰزِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã[1] da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِن مِّن شَىْءٍ إِلَّا عِندَنَا خَزَآئِنُهُۥ وَمَا نُنَزِّلُهُۥٓ إِلَّا بِقَدَرٍ مَّعْلُومٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَرْسَلْنَا ٱلرِّيَٰحَ لَوَٰقِحَ فَأَنزَلْنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَسْقَيْنَٰكُمُوهُ وَمَآ أَنتُمْ لَهُۥ بِخَٰزِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّا لَنَحْنُ نُحْىِۦ وَنُمِيتُ وَنَحْنُ ٱلْوَٰرِثُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ عَلِمْنَا ٱلْمُسْتَقْدِمِينَ مِنكُمْ وَلَقَدْ عَلِمْنَا ٱلْمُسْتَـْٔخِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَحْشُرُهُمْ إِنَّهُۥ حَكِيمٌ عَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَٰنَ مِن صَلْصَٰلٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْجَآنَّ خَلَقْنَٰهُ مِن قَبْلُ مِن نَّارِ ٱلسَّمُومِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar[1] iskar zafi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَٰٓئِكَةِ إِنِّى خَٰلِقٌۢ بَشَرًا مِّن صَلْصَٰلٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِذَا سَوَّيْتُهُۥ وَنَفَخْتُ فِيهِ مِن رُّوحِى فَقَعُوا۟ لَهُۥ سَٰجِدِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa[1] a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَسَجَدَ ٱلْمَلَٰٓئِكَةُ كُلُّهُمْ أَجْمَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَّآ إِبْلِيسَ أَبَىٰٓ أَن يَكُونَ مَعَ ٱلسَّٰجِدِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiFãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ يَٰٓإِبْلِيسُ مَا لَكَ أَلَّا تَكُونَ مَعَ ٱلسَّٰجِدِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ لَمْ أَكُن لِّأَسْجُدَ لِبَشَرٍ خَلَقْتَهُۥ مِن صَلْصَٰلٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ فَٱخْرُجْ مِنْهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّ عَلَيْكَ ٱللَّعْنَةَ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلدِّينِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ رَبِّ فَأَنظِرْنِىٓ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ ٱلْمُنظَرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْوَقْتِ ٱلْمَعْلُومِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sanan ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ رَبِّ بِمَآ أَغْوَيْتَنِى لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمْ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَّا عِبَادَكَ مِنْهُمُ ٱلْمُخْلَصِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ هَٰذَا صِرَٰطٌ عَلَىَّ مُسْتَقِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ عِبَادِى لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَٰنٌ إِلَّا مَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلْغَاوِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوْعِدُهُمْ أَجْمَعِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'akawartarsu gabã ɗaya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَهَا سَبْعَةُ أَبْوَٰبٍ لِّكُلِّ بَابٍ مِّنْهُمْ جُزْءٌ مَّقْسُومٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTanã da ƙõfõfi bakwai,[1] ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى جَنَّٰتٍ وَعُيُونٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱدْخُلُوهَا بِسَلَٰمٍ ءَامِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَنَزَعْنَا مَا فِى صُدُورِهِم مِّنْ غِلٍّ إِخْوَٰنًا عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَٰبِلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَا يَمَسُّهُمْ فِيهَا نَصَبٌ وَمَا هُم مِّنْهَا بِمُخْرَجِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikin ta ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

نَبِّئْ عِبَادِىٓ أَنِّىٓ أَنَا ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنَّ عَذَابِى هُوَ ٱلْعَذَابُ ٱلْأَلِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma azãbãTa ita ce Azãba mai raɗaɗi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَنَبِّئْهُمْ عَن ضَيْفِ إِبْرَٰهِيمَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِذْ دَخَلُوا۟ عَلَيْهِ فَقَالُوا۟ سَلَٰمًا قَالَ إِنَّا مِنكُمْ وَجِلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوا۟ لَا تَوْجَلْ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَٰمٍ عَلِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ أَبَشَّرْتُمُونِى عَلَىٰٓ أَن مَّسَّنِىَ ٱلْكِبَرُ فَبِمَ تُبَشِّرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Shin kun bã ni bushãra[1] ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوا۟ بَشَّرْنَٰكَ بِٱلْحَقِّ فَلَا تَكُن مِّنَ ٱلْقَٰنِطِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ وَمَن يَقْنَطُ مِن رَّحْمَةِ رَبِّهِۦٓ إِلَّا ٱلضَّآلُّونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijin sa, fãce ɓatattu?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا ٱلْمُرْسَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوٓا۟ إِنَّآ أُرْسِلْنَآ إِلَىٰ قَوْمٍ مُّجْرِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَّآ ءَالَ لُوطٍ إِنَّا لَمُنَجُّوهُمْ أَجْمَعِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَّا ٱمْرَأَتَهُۥ قَدَّرْنَآ إِنَّهَا لَمِنَ ٱلْغَٰبِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَمَّا جَآءَ ءَالَ لُوطٍ ٱلْمُرْسَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ إِنَّكُمْ قَوْمٌ مُّنكَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوا۟ بَلْ جِئْنَٰكَ بِمَا كَانُوا۟ فِيهِ يَمْتَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَتَيْنَٰكَ بِٱلْحَقِّ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَسْرِ بِأَهْلِكَ بِقِطْعٍ مِّنَ ٱلَّيْلِ وَٱتَّبِعْ أَدْبَٰرَهُمْ وَلَا يَلْتَفِتْ مِنكُمْ أَحَدٌ وَٱمْضُوا۟ حَيْثُ تُؤْمَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَضَيْنَآ إِلَيْهِ ذَٰلِكَ ٱلْأَمْرَ أَنَّ دَابِرَ هَٰٓؤُلَآءِ مَقْطُوعٌ مُّصْبِحِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga Asuba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَآءَ أَهْلُ ٱلْمَدِينَةِ يَسْتَبْشِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ ضَيْفِى فَلَا تَفْضَحُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَلَا تُخْزُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوٓا۟ أَوَلَمْ نَنْهَكَ عَنِ ٱلْعَٰلَمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَ هَٰٓؤُلَآءِ بَنَاتِىٓ إِن كُنتُمْ فَٰعِلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna[1] idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَعَمْرُكَ إِنَّهُمْ لَفِى سَكْرَتِهِمْ يَعْمَهُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRantsuwa da[1] rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَخَذَتْهُمُ ٱلصَّيْحَةُ مُشْرِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَجَعَلْنَا عَٰلِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِمْ حِجَارَةً مِّن سِجِّيلٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَٰتٍ لِّلْمُتَوَسِّمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّهَا لَبِسَبِيلٍ مُّقِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّلْمُؤْمِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِن كَانَ أَصْحَٰبُ ٱلْأَيْكَةِ لَظَٰلِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne ma'abũta Al'aika[1] sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱنتَقَمْنَا مِنْهُمْ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَامٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ كَذَّبَ أَصْحَٰبُ ٱلْحِجْرِ ٱلْمُرْسَلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri[1] sun ƙaryata Manzanni.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَءَاتَيْنَٰهُمْ ءَايَٰتِنَا فَكَانُوا۟ عَنْهَا مُعْرِضِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَكَانُوا۟ يَنْحِتُونَ مِنَ ٱلْجِبَالِ بُيُوتًا ءَامِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَخَذَتْهُمُ ٱلصَّيْحَةُ مُصْبِحِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga Asuba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَمَآ أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا خَلَقْنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَآ إِلَّا بِٱلْحَقِّ وَإِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَـَٔاتِيَةٌ فَٱصْفَحِ ٱلصَّفْحَ ٱلْجَمِيلَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلْخَلَّٰقُ ٱلْعَلِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ ءَاتَيْنَٰكَ سَبْعًا مِّنَ ٱلْمَثَانِى وَٱلْقُرْءَانَ ٱلْعَظِيمَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗan da ake maimaita karatunsu[1] da Alƙur'ãni mai girma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَا تَمُدَّنَّ عَيْنَيْكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعْنَا بِهِۦٓ أَزْوَٰجًا مِّنْهُمْ وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَٱخْفِضْ جَنَاحَكَ لِلْمُؤْمِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقُلْ إِنِّىٓ أَنَا ٱلنَّذِيرُ ٱلْمُبِينُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyanan ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَمَآ أَنزَلْنَا عَلَى ٱلْمُقْتَسِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ جَعَلُوا۟ ٱلْقُرْءَانَ عِضِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَوَرَبِّكَ لَنَسْـَٔلَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, rantsuwa da Ubangijinka![1] Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عَمَّا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDaga abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱصْدَعْ بِمَا تُؤْمَرُ وَأَعْرِضْ عَنِ ٱلْمُشْرِكِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّا كَفَيْنَٰكَ ٱلْمُسْتَهْزِءِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu[1] izgili.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ يَجْعَلُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدْرُكَ بِمَا يَقُولُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَكُن مِّنَ ٱلسَّٰجِدِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّىٰ يَأْتِيَكَ ٱلْيَقِينُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70