وَمَا خَلَقْنَا ٱلسَّمَآءَ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا بَٰطِلًا ذَٰلِكَ ظَنُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنَ ٱلنَّارِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã.