قَالَ رَبِّ ٱغْفِرْ لِى وَهَبْ لِى مُلْكًا لَّا يَنۢبَغِى لِأَحَدٍ مِّنۢ بَعْدِىٓ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْوَهَّابُ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna.[1] Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.