Shafin farko › Surori › Suratu Al-Qalam
Suratu Al-Qalam القلم
Ayoyi 52 · Makka · tsarin saukarwa 2
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ نٓ وَٱلْقَلَمِ وَمَا يَسْطُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَآ أَنتَ بِنِعْمَةِ رَبِّكَ بِمَجْنُونٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ لَكَ لَأَجْرًا غَيْرَ مَمْنُونٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَتُبْصِرُ وَيُبْصِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بِأَييِّكُمُ ٱلْمَفْتُونُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ga wanenku haukã take.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkin Sa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَا تُطِعِ ٱلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَدُّوا۟ لَوْ تُدْهِنُ فَيُدْهِنُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَا تُطِعْ كُلَّ حَلَّافٍ مَّهِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَمَّازٍ مَّشَّآءٍۭ بِنَمِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عُتُلٍّۭ بَعْدَ ذَٰلِكَ زَنِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَن كَانَ ذَا مَالٍ وَبَنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Idan ana karanta masa ãyõyin Mu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَنَسِمُهُۥ عَلَى ٱلْخُرْطُومِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا بَلَوْنَٰهُمْ كَمَا بَلَوْنَآ أَصْحَٰبَ ٱلْجَنَّةِ إِذْ أَقْسَمُوا۟ لَيَصْرِمُنَّهَا مُصْبِحِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَا يَسْتَثْنُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَطَافَ عَلَيْهَا طَآئِفٌ مِّن رَّبِّكَ وَهُمْ نَآئِمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَصْبَحَتْ كَٱلصَّرِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَتَنَادَوْا۟ مُصْبِحِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَنِ ٱغْدُوا۟ عَلَىٰ حَرْثِكُمْ إِن كُنتُمْ صَٰرِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱنطَلَقُوا۟ وَهُمْ يَتَخَٰفَتُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَن لَّا يَدْخُلَنَّهَا ٱلْيَوْمَ عَلَيْكُم مِّسْكِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَغَدَوْا۟ عَلَىٰ حَرْدٍ قَٰدِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَمَّا رَأَوْهَا قَالُوٓا۟ إِنَّا لَضَآلُّونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ أَوْسَطُهُمْ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ لَوْلَا تُسَبِّحُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ سُبْحَٰنَ رَبِّنَآ إِنَّا كُنَّا ظَٰلِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَلَٰوَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ يَٰوَيْلَنَآ إِنَّا كُنَّا طَٰغِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَسَىٰ رَبُّنَآ أَن يُبْدِلَنَا خَيْرًا مِّنْهَآ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا رَٰغِبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَٰلِكَ ٱلْعَذَابُ وَلَعَذَابُ ٱلْـَٔاخِرَةِ أَكْبَرُ لَوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Haka dai azãbar[1] take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَنَجْعَلُ ٱلْمُسْلِمِينَ كَٱلْمُجْرِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ لَكُمْ كِتَٰبٌ فِيهِ تَدْرُسُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ لَكُمْ فِيهِ لَمَا تَخَيَّرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ لَكُمْ أَيْمَٰنٌ عَلَيْنَا بَٰلِغَةٌ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَٰمَةِ إِنَّ لَكُمْ لَمَا تَحْكُمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kan Mu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَلْهُمْ أَيُّهُم بِذَٰلِكَ زَعِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ لَهُمْ شُرَكَآءُ فَلْيَأْتُوا۟ بِشُرَكَآئِهِمْ إِن كَانُوا۟ صَٰدِقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَوْمَ يُكْشَفُ عَن سَاقٍ وَيُدْعَوْنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ فَلَا يَسْتَطِيعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujada, sai bã zã su iyãwa ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
خَٰشِعَةً أَبْصَٰرُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ وَقَدْ كَانُوا۟ يُدْعَوْنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ وَهُمْ سَٰلِمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَذَرْنِى وَمَن يُكَذِّبُ بِهَٰذَا ٱلْحَدِيثِ سَنَسْتَدْرِجُهُم مِّنْ حَيْثُ لَا يَعْلَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأُمْلِى لَهُمْ إِنَّ كَيْدِى مَتِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ina jinkirtã musu, lalle kaidi Na mai ƙarfi ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ تَسْـَٔلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَمْ عِندَهُمُ ٱلْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلَا تَكُن كَصَاحِبِ ٱلْحُوتِ إِذْ نَادَىٰ وَهُوَ مَكْظُومٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّوْلَآ أَن تَدَٰرَكَهُۥ نِعْمَةٌ مِّن رَّبِّهِۦ لَنُبِذَ بِٱلْعَرَآءِ وَهُوَ مَذْمُومٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱجْتَبَٰهُ رَبُّهُۥ فَجَعَلَهُۥ مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِن يَكَادُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَيُزْلِقُونَكَ بِأَبْصَٰرِهِمْ لَمَّا سَمِعُوا۟ ٱلذِّكْرَ وَيَقُولُونَ إِنَّهُۥ لَمَجْنُونٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Al-Mulk
Suratu Al-Haaqqa →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.