caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Mulk الملك

Ayoyi 30 · Makka · tsarin saukarwa 77

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ تَبَٰرَكَ ٱلَّذِى بِيَدِهِ ٱلْمُلْكُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Allah), Wanda gudãnar da mulki yake ga hannun Sa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko ne a kan kome.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلْمَوْتَ وَٱلْحَيَوٰةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْغَفُورُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِى خَلَقَ سَبْعَ سَمَٰوَٰتٍ طِبَاقًا مَّا تَرَىٰ فِى خَلْقِ ٱلرَّحْمَٰنِ مِن تَفَٰوُتٍ فَٱرْجِعِ ٱلْبَصَرَ هَلْ تَرَىٰ مِن فُطُورٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna, bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ ٱرْجِعِ ٱلْبَصَرَ كَرَّتَيْنِ يَنقَلِبْ إِلَيْكَ ٱلْبَصَرُ خَاسِئًا وَهُوَ حَسِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan ka sake maimaita, dũbãwa, ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa bã.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنْيَا بِمَصَٰبِيحَ وَجَعَلْنَٰهَا رُجُومًا لِّلشَّيَٰطِينِ وَأَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابَ ٱلسَّعِيرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu, kuma Muka yi musu tattalin azãbar Sa'ĩr.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلِلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِرَبِّهِمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azãbar Jahannama, tã munana ga zamanta makõmarsu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِذَآ أُلْقُوا۟ فِيهَا سَمِعُوا۟ لَهَا شَهِيقًا وَهِىَ تَفُورُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiIdan an jẽfa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙãra, tana tafasa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تَكَادُ تَمَيَّزُ مِنَ ٱلْغَيْظِ كُلَّمَآ أُلْقِىَ فِيهَا فَوْجٌ سَأَلَهُمْ خَزَنَتُهَآ أَلَمْ يَأْتِكُمْ نَذِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTana kusa ta tsãge domin hushi, ko da yaushe aka jẽfa wani ɓangaren jama'a a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, "Wani mai gargaɗi bai je muku ba?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوا۟ بَلَىٰ قَدْ جَآءَنَا نَذِيرٌ فَكَذَّبْنَا وَقُلْنَا مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ مِن شَىْءٍ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا فِى ضَلَٰلٍ كَبِيرٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai su ce: "I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi, muka ce, 'Allah bai saukar da kome ba, bã ku cikin kõme sai ɓata babba.'"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالُوا۟ لَوْ كُنَّا نَسْمَعُ أَوْ نَعْقِلُ مَا كُنَّا فِىٓ أَصْحَٰبِ ٱلسَّعِيرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suka ce: "Dã mun zamo muna saurãre, kõ muna da hankali, dã ba mu kasance a cikin 'yan sa'ĩr ba."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱعْتَرَفُوا۟ بِذَنۢبِهِمْ فَسُحْقًا لِّأَصْحَٰبِ ٱلسَّعِيرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWato su yi iƙrãri da laifinsu. Allah Ya la'ani'yan sa'ĩr!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُم بِٱلْغَيْبِ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ كَبِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle waɗanda ke tsõron Ubangjinsu, a ɓoye, suna da wata gãfara da wani sakamako mai girma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَسِرُّوا۟ قَوْلَكُمْ أَوِ ٱجْهَرُوا۟ بِهِۦٓ إِنَّهُۥ عَلِيمٌۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta, lalle shi, (Allah), Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَا يَعْلَمُ مَنْ خَلَقَ وَهُوَ ٱللَّطِيفُ ٱلْخَبِيرُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa ne, kuma Mai labartawa?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هُوَ ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ ذَلُولًا فَٱمْشُوا۟ فِى مَنَاكِبِهَا وَكُلُوا۟ مِن رِّزْقِهِۦ وَإِلَيْهِ ٱلنُّشُورُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikin Sa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ءَأَمِنتُم مَّن فِى ٱلسَّمَآءِ أَن يَخْسِفَ بِكُمُ ٱلْأَرْضَ فَإِذَا هِىَ تَمُورُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin kõ kun amince cewa wanda ke cikin sama, bã zai iya shãfe ƙasa tãre da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ أَمِنتُم مَّن فِى ٱلسَّمَآءِ أَن يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا فَسَتَعْلَمُونَ كَيْفَ نَذِيرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKõ kun amincẽ cewa wanda ke cikin sama bã zai iya sako muku iskar gũguwa ba? To, zã ku san yadda (ãƙibar) gargaɗi Na take.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata (manzanni). To, yãya (ãƙibar) gargaɗi Na ta kasance?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَوَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَى ٱلطَّيْرِ فَوْقَهُمْ صَٰٓفَّٰتٍ وَيَقْبِضْنَ مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلَّا ٱلرَّحْمَٰنُ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَىْءٍۭ بَصِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa, bãbu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمَّنْ هَٰذَا ٱلَّذِى هُوَ جُندٌ لَّكُمْ يَنصُرُكُم مِّن دُونِ ٱلرَّحْمَٰنِ إِنِ ٱلْكَٰفِرُونَ إِلَّا فِى غُرُورٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWãne ne wanda zai zame muku mayãƙin da zai taimake ku, wanda bã (Allah) ba, Mai rahama? Kãfirai ba su a cikin kõme fãce rũɗu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمَّنْ هَٰذَا ٱلَّذِى يَرْزُقُكُمْ إِنْ أَمْسَكَ رِزْقَهُۥ بَل لَّجُّوا۟ فِى عُتُوٍّ وَنُفُورٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWãne ne wanda zai ciyar da ku, idan (Allah) Ya riƙe arzikin Sa? A'aha, sun yi zurfi cikin girman kai da tãshin hankali.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَفَمَن يَمْشِى مُكِبًّا عَلَىٰ وَجْهِهِۦٓ أَهْدَىٰٓ أَمَّن يَمْشِى سَوِيًّا عَلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa yã fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ هُوَ ٱلَّذِىٓ أَنشَأَكُمْ وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمْعَ وَٱلْأَبْصَٰرَ وَٱلْأَفْـِٔدَةَ قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "(Allah) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku, Ya sanya muku ji da gani da tunãni, amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ هُوَ ٱلَّذِى ذَرَأَكُمْ فِى ٱلْأَرْضِ وَإِلَيْهِ تُحْشَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma kace "Shi ne Ya halitta ku daga ƙasã, kuma zuwa gare Shi ne ake tãshin ku."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَٰدِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma sunã cewa, "Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance mãsu gaskiya ne kũ?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ إِنَّمَا ٱلْعِلْمُ عِندَ ٱللَّهِ وَإِنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٌ مُّبِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyana (gargaɗin)."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَمَّا رَأَوْهُ زُلْفَةً سِيٓـَٔتْ وُجُوهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَقِيلَ هَٰذَا ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تَدَّعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, lokacin da suka gan ta (azãbar) a kusa, fuskokin waɗanda suka kãfirta suka mũnana, kuma aka ce (musu) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِنْ أَهْلَكَنِىَ ٱللَّهُ وَمَن مَّعِىَ أَوْ رَحِمَنَا فَمَن يُجِيرُ ٱلْكَٰفِرِينَ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce musu "Idan Allah Ya halaka ni nĩ da wanda ke tãre da ni, ko kuma, Yã yi mana rahama, to, wãne ne zai tserar da kafirai daga wata azãba mai raɗaɗi?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ هُوَ ٱلرَّحْمَٰنُ ءَامَنَّا بِهِۦ وَعَلَيْهِ تَوَكَّلْنَا فَسَتَعْلَمُونَ مَنْ هُوَ فِى ضَلَٰلٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Shĩ ne Mai rahama mun yi ĩmãni da Shi, gare Shi muka dogara, saboda haka zã ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِنْ أَصْبَحَ مَآؤُكُمْ غَوْرًا فَمَن يَأْتِيكُم بِمَآءٍ مَّعِينٍۭ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ko kun gani, idan ruwanku ya wãyi gari faƙaƙƙe, to, wãne ne zai zo muku da ruwa wani mai ɓuɓɓuga?"[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70