caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Haaqqa الحاقة

Ayoyi 52 · Makka · tsarin saukarwa 78

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ ٱلْحَآقَّةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKiran gaskiya!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَا ٱلْحَآقَّةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMẽne ne kiran gaskiya?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْحَآقَّةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَذَّبَتْ ثَمُودُ وَعَادٌۢ بِٱلْقَارِعَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSamũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهْلِكُوا۟ بِٱلطَّاغِيَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَمَّا عَادٌ فَأُهْلِكُوا۟ بِرِيحٍ صَرْصَرٍ عَاتِيَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

سَخَّرَهَا عَلَيْهِمْ سَبْعَ لَيَالٍ وَثَمَٰنِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومًا فَتَرَى ٱلْقَوْمَ فِيهَا صَرْعَىٰ كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ خَاوِيَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَهَلْ تَرَىٰ لَهُم مِّنۢ بَاقِيَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَآءَ فِرْعَوْنُ وَمَن قَبْلَهُۥ وَٱلْمُؤْتَفِكَٰتُ بِٱلْخَاطِئَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَعَصَوْا۟ رَسُولَ رَبِّهِمْ فَأَخَذَهُمْ أَخْذَةً رَّابِيَةً

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّا لَمَّا طَغَا ٱلْمَآءُ حَمَلْنَٰكُمْ فِى ٱلْجَارِيَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِنَجْعَلَهَا لَكُمْ تَذْكِرَةً وَتَعِيَهَآ أُذُنٌ وَٰعِيَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِذَا نُفِخَ فِى ٱلصُّورِ نَفْخَةٌ وَٰحِدَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَحُمِلَتِ ٱلْأَرْضُ وَٱلْجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةً وَٰحِدَةً

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَيَوْمَئِذٍ وَقَعَتِ ٱلْوَاقِعَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA ran nan, mai aukuwa zã ta auku.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَهِىَ يَوْمَئِذٍ وَاهِيَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْمَلَكُ عَلَىٰٓ أَرْجَآئِهَا وَيَحْمِلُ عَرْشَ رَبِّكَ فَوْقَهُمْ يَوْمَئِذٍ ثَمَٰنِيَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَئِذٍ تُعْرَضُونَ لَا تَخْفَىٰ مِنكُمْ خَافِيَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَيَقُولُ هَآؤُمُ ٱقْرَءُوا۟ كِتَٰبِيَهْ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنِّى ظَنَنتُ أَنِّى مُلَٰقٍ حِسَابِيَهْ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَهُوَ فِى عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فِى جَنَّةٍ عَالِيَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA cikin Aljanna maɗaukakiya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُطُوفُهَا دَانِيَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiNunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ هَنِيٓـًٔۢا بِمَآ أَسْلَفْتُمْ فِى ٱلْأَيَّامِ ٱلْخَالِيَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَٰبَهُۥ بِشِمَالِهِۦ فَيَقُولُ يَٰلَيْتَنِى لَمْ أُوتَ كِتَٰبِيَهْ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَمْ أَدْرِ مَا حِسَابِيَهْ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَٰلَيْتَهَا كَانَتِ ٱلْقَاضِيَةَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَآ أَغْنَىٰ عَنِّى مَالِيَهْ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هَلَكَ عَنِّى سُلْطَٰنِيَهْ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ĩkona ya ɓace mini!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

خُذُوهُ فَغُلُّوهُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ ٱلْجَحِيمَ صَلُّوهُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ فِى سِلْسِلَةٍ ذَرْعُهَا سَبْعُونَ ذِرَاعًا فَٱسْلُكُوهُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّهُۥ كَانَ لَا يُؤْمِنُ بِٱللَّهِ ٱلْعَظِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَيْسَ لَهُ ٱلْيَوْمَ هَٰهُنَا حَمِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنْ غِسْلِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَّا يَأْكُلُهُۥٓ إِلَّا ٱلْخَٰطِـُٔونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَآ أُقْسِمُ بِمَا تُبْصِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا لَا تُبْصِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa abin da bã ku iya gani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّهُۥ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَاعِرٍ قَلِيلًا مَّا تُؤْمِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا بِقَوْلِ كَاهِنٍ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAbin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ ٱلْأَقَاوِيلِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَأَخَذْنَا مِنْهُ بِٱلْيَمِينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDã Mun kãma shi da dãma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ ٱلْوَتِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumisa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَمَا مِنكُم مِّنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَٰجِزِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbar Mu) daga gare shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّهُۥ لَتَذْكِرَةٌ لِّلْمُتَّقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّا لَنَعْلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّهُۥ لَحَسْرَةٌ عَلَى ٱلْكَٰفِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّهُۥ لَحَقُّ ٱلْيَقِينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙini.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70