Shafin farko › Surori › Suratu Al-Muddaththir
Suratu Al-Muddaththir المدثر
Ayoyi 56 · Makka · tsarin saukarwa 4
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ يَٰٓأَيُّهَا ٱلْمُدَّثِّرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قُمْ فَأَنذِرْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَرَبَّكَ فَكَبِّرْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلرُّجْزَ فَٱهْجُرْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَا تَمْنُن تَسْتَكْثِرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلِرَبِّكَ فَٱصْبِرْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِذَا نُقِرَ فِى ٱلنَّاقُورِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَذَٰلِكَ يَوْمَئِذٍ يَوْمٌ عَسِيرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَلَى ٱلْكَٰفِرِينَ غَيْرُ يَسِيرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ذَرْنِى وَمَنْ خَلَقْتُ وَحِيدًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَجَعَلْتُ لَهُۥ مَالًا مَّمْدُودًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَبَنِينَ شُهُودًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da ɗiyã halartattu,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَهَّدتُّ لَهُۥ تَمْهِيدًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ يَطْمَعُ أَنْ أَزِيدَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَلَّآ إِنَّهُۥ كَانَ لِـَٔايَٰتِنَا عَنِيدًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyin Mu, mai tsaurin kai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَأُرْهِقُهُۥ صَعُودًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ فَكَّرَ وَقَدَّرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَقُتِلَ كَيْفَ قَدَّرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ قُتِلَ كَيْفَ قَدَّرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ نَظَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan, ya yi tunãni
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ عَبَسَ وَبَسَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ أَدْبَرَ وَٱسْتَكْبَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَقَالَ إِنْ هَٰذَآ إِلَّا سِحْرٌ يُؤْثَرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنْ هَٰذَآ إِلَّا قَوْلُ ٱلْبَشَرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Wannan maganar mutum dai ce."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَأُصْلِيهِ سَقَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Zã Ni ƙõna shi da Saƙar.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا سَقَرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَا تُبْقِى وَلَا تَذَرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَوَّاحَةٌ لِّلْبَشَرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَلَيْهَا تِسْعَةَ عَشَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A kanta akwai (matsara) gõma shã tara.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا جَعَلْنَآ أَصْحَٰبَ ٱلنَّارِ إِلَّا مَلَٰٓئِكَةً وَمَا جَعَلْنَا عِدَّتَهُمْ إِلَّا فِتْنَةً لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لِيَسْتَيْقِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَٰبَ وَيَزْدَادَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِيمَٰنًا وَلَا يَرْتَابَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَٰبَ وَٱلْمُؤْمِنُونَ وَلِيَقُولَ ٱلَّذِينَ فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌ وَٱلْكَٰفِرُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَٰذَا مَثَلًا كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهْدِى مَن يَشَآءُ وَمَا يَعْلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلَّا هُوَ وَمَا هِىَ إِلَّا ذِكْرَىٰ لِلْبَشَرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَلَّا وَٱلْقَمَرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A'aha! Ina rantsuwa da watã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلَّيْلِ إِذْ أَدْبَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلصُّبْحِ إِذَآ أَسْفَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da sãfiya idan ta wãye.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهَا لَإِحْدَى ٱلْكُبَرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
نَذِيرًا لِّلْبَشَرِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mai gargaɗĩ ce ga mutum.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لِمَن شَآءَ مِنكُمْ أَن يَتَقَدَّمَ أَوْ يَتَأَخَّرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كُلُّ نَفْسٍۭ بِمَا كَسَبَتْ رَهِينَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّآ أَصْحَٰبَ ٱلْيَمِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Fãce mutãnen dãma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِى جَنَّٰتٍ يَتَسَآءَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A cikin Aljanna suna tambayar jũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَنِ ٱلْمُجْرِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Game da mãsu laifi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَا سَلَكَكُمْ فِى سَقَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ لَمْ نَكُ مِنَ ٱلْمُصَلِّينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَمْ نَكُ نُطْعِمُ ٱلْمِسْكِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ ٱلْخَآئِضِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوْمِ ٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
حَتَّىٰٓ أَتَىٰنَا ٱلْيَقِينُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَا تَنفَعُهُمْ شَفَٰعَةُ ٱلشَّٰفِعِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَا لَهُمْ عَنِ ٱلتَّذْكِرَةِ مُعْرِضِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَأَنَّهُمْ حُمُرٌ مُّسْتَنفِرَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَرَّتْ مِن قَسْوَرَةٍۭ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sun gudu daga zãki.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلْ يُرِيدُ كُلُّ ٱمْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُؤْتَىٰ صُحُفًا مُّنَشَّرَةً
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَلَّا بَل لَّا يَخَافُونَ ٱلْـَٔاخِرَةَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَلَّآ إِنَّهُۥ تَذْكِرَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Dõmin wanda ya so, ya tuna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا يَذْكُرُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ هُوَ أَهْلُ ٱلتَّقْوَىٰ وَأَهْلُ ٱلْمَغْفِرَةِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Al-Muzzammil
Suratu Al-Qiyaama →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.