Shafin farko › Surori › Suratu Al-Muzzammil
Suratu Al-Muzzammil المزمل
Ayoyi 20 · Makka · tsarin saukarwa 3
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ يَٰٓأَيُّهَا ٱلْمُزَّمِّلُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Yã wanda ya lulluɓe!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قُمِ ٱلَّيْلَ إِلَّا قَلِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
نِّصْفَهُۥٓ أَوِ ٱنقُصْ مِنْهُ قَلِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَوْ زِدْ عَلَيْهِ وَرَتِّلِ ٱلْقُرْءَانَ تَرْتِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا سَنُلْقِى عَلَيْكَ قَوْلًا ثَقِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ نَاشِئَةَ ٱلَّيْلِ هِىَ أَشَدُّ وَطْـًٔا وَأَقْوَمُ قِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ لَكَ فِى ٱلنَّهَارِ سَبْحًا طَوِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱذْكُرِ ٱسْمَ رَبِّكَ وَتَبَتَّلْ إِلَيْهِ تَبْتِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
رَّبُّ ٱلْمَشْرِقِ وَٱلْمَغْرِبِ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱتَّخِذْهُ وَكِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَٱهْجُرْهُمْ هَجْرًا جَمِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَذَرْنِى وَٱلْمُكَذِّبِينَ أُو۟لِى ٱلنَّعْمَةِ وَمَهِّلْهُمْ قَلِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ لَدَيْنَآ أَنكَالًا وَجَحِيمًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, a wurin Mu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَطَعَامًا ذَا غُصَّةٍ وَعَذَابًا أَلِيمًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَوْمَ تَرْجُفُ ٱلْأَرْضُ وَٱلْجِبَالُ وَكَانَتِ ٱلْجِبَالُ كَثِيبًا مَّهِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّآ أَرْسَلْنَآ إِلَيْكُمْ رَسُولًا شَٰهِدًا عَلَيْكُمْ كَمَآ أَرْسَلْنَآ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ رَسُولًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo[1] mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo[2] zuwaga Fir'auna,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَعَصَىٰ فِرْعَوْنُ ٱلرَّسُولَ فَأَخَذْنَٰهُ أَخْذًا وَبِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَكَيْفَ تَتَّقُونَ إِن كَفَرْتُمْ يَوْمًا يَجْعَلُ ٱلْوِلْدَٰنَ شِيبًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلسَّمَآءُ مُنفَطِرٌۢ بِهِۦ كَانَ وَعْدُهُۥ مَفْعُولًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ هَٰذِهِۦ تَذْكِرَةٌ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ رَبَّكَ يَعْلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدْنَىٰ مِن ثُلُثَىِ ٱلَّيْلِ وَنِصْفَهُۥ وَثُلُثَهُۥ وَطَآئِفَةٌ مِّنَ ٱلَّذِينَ مَعَكَ وَٱللَّهُ يُقَدِّرُ ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ عَلِمَ أَن لَّن تُحْصُوهُ فَتَابَ عَلَيْكُمْ فَٱقْرَءُوا۟ مَا تَيَسَّرَ مِنَ ٱلْقُرْءَانِ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم مَّرْضَىٰ وَءَاخَرُونَ يَضْرِبُونَ فِى ٱلْأَرْضِ يَبْتَغُونَ مِن فَضْلِ ٱللَّهِ وَءَاخَرُونَ يُقَٰتِلُونَ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ فَٱقْرَءُوا۟ مَا تَيَسَّرَ مِنْهُ وَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَقْرِضُوا۟ ٱللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا وَمَا تُقَدِّمُوا۟ لِأَنفُسِكُم مِّنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيْرًا وَأَعْظَمَ أَجْرًا وَٱسْتَغْفِرُوا۟ ٱللَّهَ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌۢ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Al-Jinn
Suratu Al-Muddaththir →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.