caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Qiyaama القيامة

Ayoyi 40 · Makka · tsarin saukarwa 31

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ لَآ أُقْسِمُ بِيَوْمِ ٱلْقِيَٰمَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã sai Nã yi rantsuwa[1] da Rãnar ¡iyãma ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَآ أُقْسِمُ بِٱلنَّفْسِ ٱللَّوَّامَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin[1] kansa ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَيَحْسَبُ ٱلْإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجْمَعَ عِظَامَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّىَ بَنَانَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiNa'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

بَلْ يُرِيدُ ٱلْإِنسَٰنُ لِيَفْجُرَ أَمَامَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَسْـَٔلُ أَيَّانَ يَوْمُ ٱلْقِيَٰمَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِذَا بَرِقَ ٱلْبَصَرُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَخَسَفَ ٱلْقَمَرُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجُمِعَ ٱلشَّمْسُ وَٱلْقَمَرُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAka tãra rãnã da watã

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَقُولُ ٱلْإِنسَٰنُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ ٱلْمَفَرُّ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّا لَا وَزَرَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! bãbu mafaka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ ٱلْمُسْتَقَرُّ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumizuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يُنَبَّؤُا۟ ٱلْإِنسَٰنُ يَوْمَئِذٍۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAna gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

بَلِ ٱلْإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفْسِهِۦ بَصِيرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَوْ أَلْقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَا تُحَرِّكْ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِۦٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKada ka mõtsar[1] da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُۥ وَقُرْءَانَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِذَا قَرَأْنَٰهُ فَٱتَّبِعْ قُرْءَانَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumisa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّا بَلْ تُحِبُّونَ ٱلْعَاجِلَةَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَتَذَرُونَ ٱلْـَٔاخِرَةَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKunã barin ta ƙarshen (Lãhira).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiZuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍۭ بَاسِرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تَظُنُّ أَن يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِىَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقِيلَ مَنْ رَاقٍ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumikuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلْفِرَاقُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ ٱلْمَسَاقُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiZuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa[1] take.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAmma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiHalaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَيَحْسَبُ ٱلْإِنسَٰنُ أَن يُتْرَكَ سُدًى

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَمْ يَكُ نُطْفَةً مِّن مَّنِىٍّ يُمْنَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ كَانَ عَلَقَةً فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَجَعَلَ مِنْهُ ٱلزَّوْجَيْنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَيْسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحْـِۧىَ ٱلْمَوْتَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70