Shafin farko › Surori › Suratu Al-Waaqia
Suratu Al-Waaqia الواقعة
Ayoyi 96 · Makka · tsarin saukarwa 46
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ إِذَا وَقَعَتِ ٱلْوَاقِعَةُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Idan mai aukuwa ta auku.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَيْسَ لِوَقْعَتِهَا كَاذِبَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
خَافِضَةٌ رَّافِعَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذَا رُجَّتِ ٱلْأَرْضُ رَجًّا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَبُسَّتِ ٱلْجِبَالُ بَسًّا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَكَانَتْ هَبَآءً مُّنۢبَثًّا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكُنتُمْ أَزْوَٰجًا ثَلَٰثَةً
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma kun kasance nau'i uku.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَصْحَٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ مَآ أَصْحَٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Watau mazõwa dãma[1]. Mẽne ne mazõwa dãma?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَصْحَٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ مَآ أَصْحَٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلسَّٰبِقُونَ ٱلسَّٰبِقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أُو۟لَٰٓئِكَ ٱلْمُقَرَّبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِى جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A ckin Aljannar ni'ima.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Jama'a ne daga mutãnen farko.[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَلِيلٌ مِّنَ ٱلْـَٔاخِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَلَىٰ سُرُرٍ مَّوْضُونَةٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيْهَا مُتَقَٰبِلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَٰنٌ مُّخَلَّدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بِأَكْوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّا يُصَدَّعُونَ عَنْهَا وَلَا يُنزِفُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفَٰكِهَةٍ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَحْمِ طَيْرٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَحُورٌ عِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَأَمْثَٰلِ ٱللُّؤْلُؤِ ٱلْمَكْنُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
جَزَآءًۢ بِمَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا تَأْثِيمًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا قِيلًا سَلَٰمًا سَلَٰمًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَصْحَٰبُ ٱلْيَمِينِ مَآ أَصْحَٰبُ ٱلْيَمِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِى سِدْرٍ مَّخْضُودٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَطَلْحٍ مَّنضُودٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَظِلٍّ مَّمْدُودٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآءٍ مَّسْكُوبٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wani ruwa mai gudãna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفَٰكِهَةٍ كَثِيرَةٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّا مَقْطُوعَةٍ وَلَا مَمْنُوعَةٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفُرُشٍ مَّرْفُوعَةٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّآ أَنشَأْنَٰهُنَّ إِنشَآءً
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَجَعَلْنَٰهُنَّ أَبْكَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan Muka sanya su budurwai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عُرُبًا أَتْرَابًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لِّأَصْحَٰبِ ٱلْيَمِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ga mazõwa dãma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْـَٔاخِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَصْحَٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصْحَٰبُ ٱلشِّمَالِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِى سَمُومٍ وَحَمِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَظِلٍّ مِّن يَحْمُومٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّا بَارِدٍ وَلَا كَرِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَبْلَ ذَٰلِكَ مُتْرَفِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكَانُوا۟ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلْحِنثِ ٱلْعَظِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكَانُوا۟ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَوَءَابَآؤُنَا ٱلْأَوَّلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin, kuma da ubanninmu na farko?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قُلْ إِنَّ ٱلْأَوَّلِينَ وَٱلْـَٔاخِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَمَجْمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَٰتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ إِنَّكُمْ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلْمُكَذِّبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَـَٔاكِلُونَ مِن شَجَرٍ مِّن زَقُّومٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَالِـُٔونَ مِنْهَا ٱلْبُطُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَشَٰرِبُونَ عَلَيْهِ مِنَ ٱلْحَمِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَشَٰرِبُونَ شُرْبَ ٱلْهِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا نُزُلُهُمْ يَوْمَ ٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
نَحْنُ خَلَقْنَٰكُمْ فَلَوْلَا تُصَدِّقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَرَءَيْتُم مَّا تُمْنُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ءَأَنتُمْ تَخْلُقُونَهُۥٓ أَمْ نَحْنُ ٱلْخَٰلِقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
نَحْنُ قَدَّرْنَا بَيْنَكُمُ ٱلْمَوْتَ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa[1] ba,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمْثَٰلَكُمْ وَنُنشِئَكُمْ فِى مَا لَا تَعْلَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ ٱلنَّشْأَةَ ٱلْأُولَىٰ فَلَوْلَا تَذَكَّرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَرَءَيْتُم مَّا تَحْرُثُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ءَأَنتُمْ تَزْرَعُونَهُۥٓ أَمْ نَحْنُ ٱلزَّٰرِعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَوْ نَشَآءُ لَجَعَلْنَٰهُ حُطَٰمًا فَظَلْتُمْ تَفَكَّهُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا لَمُغْرَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَرَءَيْتُمُ ٱلْمَآءَ ٱلَّذِى تَشْرَبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ءَأَنتُمْ أَنزَلْتُمُوهُ مِنَ ٱلْمُزْنِ أَمْ نَحْنُ ٱلْمُنزِلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَوْ نَشَآءُ جَعَلْنَٰهُ أُجَاجًا فَلَوْلَا تَشْكُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَرَءَيْتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِى تُورُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ءَأَنتُمْ أَنشَأْتُمْ شَجَرَتَهَآ أَمْ نَحْنُ ٱلْمُنشِـُٔونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
نَحْنُ جَعَلْنَٰهَا تَذْكِرَةً وَمَتَٰعًا لِّلْمُقْوِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَآ أُقْسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٌ لَّوْ تَعْلَمُونَ عَظِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ لَقُرْءَانٌ كَرِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِى كِتَٰبٍ مَّكْنُونٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A cikin wani littafi tsararre.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلْمُطَهَّرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَبِهَٰذَا ٱلْحَدِيثِ أَنتُم مُّدْهِنُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَجْعَلُونَ رِزْقَكُمْ أَنَّكُمْ تُكَذِّبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَوْلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلْحُلْقُومَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَنتُمْ حِينَئِذٍ تَنظُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنكُمْ وَلَٰكِن لَّا تُبْصِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَوْلَآ إِن كُنتُمْ غَيْرَ مَدِينِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
تَرْجِعُونَهَآ إِن كُنتُمْ صَٰدِقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلْمُقَرَّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَرَوْحٌ وَرَيْحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنْ أَصْحَٰبِ ٱلْيَمِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَلَٰمٌ لَّكَ مِنْ أَصْحَٰبِ ٱلْيَمِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلْمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَنُزُلٌ مِّنْ حَمِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَصْلِيَةُ جَحِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da ƙõnuwa da Jahĩm,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلْيَقِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka, ka tsarkake[1] sũnan Ubangijinka, Mai karimci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Ar-Rahmaan
Suratu Al-Hadid →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.