Hausa Translation - Abu Bakr JumiShĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaitu a kan Al'arshi, Yanã sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta, kuma Shĩ yanã tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãza.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKu yi ĩmãni da Allah da Manzon Sa, kuma ku ciyar daga abin da Allah Ya wakilta ku a cikinsa (na dũkiya). To, waɗannan da suka yi ĩmãni daga cikinku, kuma suka ciyar, sunã da wani sakamako mai girma.
Hausa Translation - Abu Bakr Jumikuma me ya same ku, bã zã ku yi ĩmãni ba da Allah, alhãli kuwa manzon Sa na kiran ku dõmin ku yi ĩmãni da Ubangijinku, kuma lalle Allah Ya karɓi alkawarinku (cẽwa zã ku bauta Masa)? (Ku bauta Masa) idan kun kasance[1] mãsu ĩmãni.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShĩ ne wanda ke sassaukar da ãyõyi bayyanannu ga Bãwan Sa, dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai tausayi ne gare ku, Mai jin ƙai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma me ya sãme ku, bã zã ku ciyar ba dõmin ɗaukaka kalmar Allah, alhãli kuwa gãdon sammai da ƙasã na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabãnin cin nasara, kuma ya yi yãƙi daga cikinku, bã ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafĩfĩta girman daraja[1] bisa ga waɗanda suka ciyar daga bãya kuma suka yi yãƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWãne ne wanda zai ranta wa Allah rance mai kyau dõmin Allah Ya ninka masa shi (a dũniya) kuma Yanã da wani sakamako na karimci (a Lãhira)?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) "Bushãrarku a yau, ita ce gidajen Aljanna." Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan, shĩ ne babban rabo mai girma.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da munafikai maza da munãfikai mãtã ke cẽwa waɗanda suka yi ĩmãni: "Ku dũbẽ mu, mu yi makãmashi daga haskenku!" A ce (musu): "Ku kõma a bãyanku, dõmin ku nẽmo wani haske." Sai a danne a tsakãninsu da wani gãru yanã da wani ƙyaure, a cikinsa nan rahama take, kuma a bãyansa daga wajensa azaba take.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã kiran su, "Ashe, bã tãre muke da ku ba?" Su ce: "Ĩ, amma kũ, kun fitini kanku, kuma kun yi jiran wata masĩfa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu gũrace-gũrace sun rũɗe ku, har umurnin Allah ya jẽ muku, kumamarũɗi ya rũɗe ku game da Allah."
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"To, a yau bã zã a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma bã zã a karɓa daga waɗanda suka kãfirta ba. Makõmarku wutã ce, ita ce mai dacẽwa da ku, kuma makõmarku ɗin nan tã mũnana."
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, lõkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmãnĩ[1] zukãtansu su yi tawãlu'i ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda aka bai wa littãfi a gabãnin haka, sai zãmani ya yi tsawo a kansu, sabõda haka zukãtansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle mãsu gaskatãwa maza da mãsu gaskatãwa mãtã, kuma suka ranta wa Allah rance mai kyau, anã riɓanya musu, kuma suna da wani sakamako na karimci.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da Mazannin Sa waɗannan sũ ne kamãlar gaskatãwa kuma su ne mãsu shahãda awurin Ubangjinsu. sunã da sakamakonsu da haskensu. waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, waɗannan su ne'yan Jahĩm.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKu sani cẽwa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙẽƙashe, har ka ganta tã zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin rũɗi kawai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKu yi tsẽre zuwa ga (nẽman) gãfara daga Ubangjinku, da Aljanna fãɗinta kamar fãɗin samã da ƙasã ne, an yi tattalinta dõmin waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da Manzannin Sa. Wannan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah Mai falala ne Mai girma.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar alfahari da abin da Ya bã ku. Kuma Allah bã Ya son dukkan mai tãƙama, mai alfahari.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWatau, waɗanda ke yin rõwa, kuma sunã umumin mutãne da yin rõwa. Kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne kaɗai Mawadãci, Gõdadde.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiHaƙĩƙa, lalle Mun aiko Manzannin Mu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci, kuma Mun saukar da baƙin ƙarfe,[1] a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfãni ga mutãne, kuma dõmin Allah Ya san mai taimakon Sa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma haƙĩƙa, lalle, Mun aiki Nũhu da Ibrahĩm, kuma Muka sanya Annabci da Littĩfi a cikin zuriyarsu; daga cikinsu akwai mai nẽman shiryuwa, kuma mãsu yawa daga cikinsu fasiƙai ne.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan Muka biyar a bãyansu[1] da Manzannin Mu; kuma Muka biyar da ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin zukãtan waɗanda suka bĩ shi, da ruhbãnanci[2] wanda suka ƙãga, shi, ba Mu rubũta shi ba a kansu, fãce dai (Mun rubũta musu nẽman yardar Allah, sa'an nan ba su tsare shi haƙƙin tsarẽwarsa ba, sabõda haka Muka bai wa waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinsu sakamakonsu kuma mãsu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmãni da Manzon Sa[1] Ya bã ku rabo biyu daga rahamar Sa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi, kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai rahama.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin kada [1]mutãnen Littãfi su san cẽwa lalle bã su da ikon yi ga kõme na falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so (wannan jãhilci yã hana su ĩmani). Kuma Alah Mai falala ne mai girma.