Shafin farko › Surori › Suratu Qaaf
Suratu Qaaf ق
Ayoyi 45 · Makka · tsarin saukarwa 34
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ قٓ وَٱلْقُرْءَانِ ٱلْمَجِيدِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi K. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلْ عَجِبُوٓا۟ أَن جَآءَهُم مُّنذِرٌ مِّنْهُمْ فَقَالَ ٱلْكَٰفِرُونَ هَٰذَا شَىْءٌ عَجِيبٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا ذَٰلِكَ رَجْعٌۢ بَعِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَدْ عَلِمْنَا مَا تَنقُصُ ٱلْأَرْضُ مِنْهُمْ وَعِندَنَا كِتَٰبٌ حَفِيظٌۢ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurin Mu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلْ كَذَّبُوا۟ بِٱلْحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمْ فَهُمْ فِىٓ أَمْرٍ مَّرِيجٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَلَمْ يَنظُرُوٓا۟ إِلَى ٱلسَّمَآءِ فَوْقَهُمْ كَيْفَ بَنَيْنَٰهَا وَزَيَّنَّٰهَا وَمَا لَهَا مِن فُرُوجٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلْأَرْضَ مَدَدْنَٰهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَٰسِىَ وَأَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍۭ بَهِيجٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
تَبْصِرَةً وَذِكْرَىٰ لِكُلِّ عَبْدٍ مُّنِيبٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنَزَّلْنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً مُّبَٰرَكًا فَأَنۢبَتْنَا بِهِۦ جَنَّٰتٍ وَحَبَّ ٱلْحَصِيدِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلنَّخْلَ بَاسِقَٰتٍ لَّهَا طَلْعٌ نَّضِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
رِّزْقًا لِّلْعِبَادِ وَأَحْيَيْنَا بِهِۦ بَلْدَةً مَّيْتًا كَذَٰلِكَ ٱلْخُرُوجُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَأَصْحَٰبُ ٱلرَّسِّ وَثَمُودُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, [1]da Samũdãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَعَادٌ وَفِرْعَوْنُ وَإِخْوَٰنُ لُوطٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَصْحَٰبُ ٱلْأَيْكَةِ وَقَوْمُ تُبَّعٍ كُلٌّ كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ وَعِيدِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da ma'abũta ƙunci [1]da mutãnen Tubba'u,[2] kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَعَيِينَا بِٱلْخَلْقِ ٱلْأَوَّلِ بَلْ هُمْ فِى لَبْسٍ مِّنْ خَلْقٍ جَدِيدٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَٰنَ وَنَعْلَمُ مَا تُوَسْوِسُ بِهِۦ نَفْسُهُۥ وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنْ حَبْلِ ٱلْوَرِيدِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar hannayẽnsa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ يَتَلَقَّى ٱلْمُتَلَقِّيَانِ عَنِ ٱلْيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ قَعِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَّا يَلْفِظُ مِن قَوْلٍ إِلَّا لَدَيْهِ رَقِيبٌ عَتِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَجَآءَتْ سَكْرَةُ ٱلْمَوْتِ بِٱلْحَقِّ ذَٰلِكَ مَا كُنتَ مِنْهُ تَحِيدُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنُفِخَ فِى ٱلصُّورِ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْوَعِيدِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَجَآءَتْ كُلُّ نَفْسٍ مَّعَهَا سَآئِقٌ وَشَهِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّقَدْ كُنتَ فِى غَفْلَةٍ مِّنْ هَٰذَا فَكَشَفْنَا عَنكَ غِطَآءَكَ فَبَصَرُكَ ٱلْيَوْمَ حَدِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَالَ قَرِينُهُۥ هَٰذَا مَا لَدَىَّ عَتِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma abõkin haɗinsa[1] ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَلْقِيَا فِى جَهَنَّمَ كُلَّ كَفَّارٍ عَنِيدٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ مُّرِيبٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِى جَعَلَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَأَلْقِيَاهُ فِى ٱلْعَذَابِ ٱلشَّدِيدِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ قَرِينُهُۥ رَبَّنَا مَآ أَطْغَيْتُهُۥ وَلَٰكِن كَانَ فِى ضَلَٰلٍۭ بَعِيدٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Abõkin haɗinsa[1] ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ لَا تَخْتَصِمُوا۟ لَدَىَّ وَقَدْ قَدَّمْتُ إِلَيْكُم بِٱلْوَعِيدِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Kada ku yi husũma a wur Nalhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَا يُبَدَّلُ ٱلْقَوْلُ لَدَىَّ وَمَآ أَنَا۠ بِظَلَّٰمٍ لِّلْعَبِيدِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyi Na."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَوْمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ ٱمْتَلَأْتِ وَتَقُولُ هَلْ مِن مَّزِيدٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe,[1] akwai wani ƙãri?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأُزْلِفَتِ ٱلْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ غَيْرَ بَعِيدٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِكُلِّ أَوَّابٍ حَفِيظٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَّنْ خَشِىَ ٱلرَّحْمَٰنَ بِٱلْغَيْبِ وَجَآءَ بِقَلْبٍ مُّنِيبٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, [1]kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱدْخُلُوهَا بِسَلَٰمٍ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْخُلُودِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (A ce musu) "Ku shige ta da aminci, [1]waccan ita ce rãnar dawwama."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَهُم مَّا يَشَآءُونَ فِيهَا وَلَدَيْنَا مَزِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هُمْ أَشَدُّ مِنْهُم بَطْشًا فَنَقَّبُوا۟ فِى ٱلْبِلَٰدِ هَلْ مِن مَّحِيصٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'?[1] (Babu).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَذِكْرَىٰ لِمَن كَانَ لَهُۥ قَلْبٌ أَوْ أَلْقَى ٱلسَّمْعَ وَهُوَ شَهِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِى سِتَّةِ أَيَّامٍ وَمَا مَسَّنَا مِن لُّغُوبٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ ٱلشَّمْسِ وَقَبْلَ ٱلْغُرُوبِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi[1] game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَأَدْبَٰرَ ٱلسُّجُودِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱسْتَمِعْ يَوْمَ يُنَادِ ٱلْمُنَادِ مِن مَّكَانٍ قَرِيبٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri [1]makusanci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَوْمَ يَسْمَعُونَ ٱلصَّيْحَةَ بِٱلْحَقِّ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْخُرُوجِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا نَحْنُ نُحْىِۦ وَنُمِيتُ وَإِلَيْنَا ٱلْمَصِيرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَوْمَ تَشَقَّقُ ٱلْأَرْضُ عَنْهُمْ سِرَاعًا ذَٰلِكَ حَشْرٌ عَلَيْنَا يَسِيرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ وَمَآ أَنتَ عَلَيْهِم بِجَبَّارٍ فَذَكِّرْ بِٱلْقُرْءَانِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani,[1] ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Al-Hujuraat
Suratu Adh-Dhaariyat →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.