caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Hujuraat الحجرات

Ayoyi 18 · Madina · tsarin saukarwa 106

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تُقَدِّمُوا۟ بَيْنَ يَدَىِ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da Manzon Sa.[1] Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَرْفَعُوٓا۟ أَصْوَٰتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ ٱلنَّبِىِّ وَلَا تَجْهَرُوا۟ لَهُۥ بِٱلْقَوْلِ كَجَهْرِ بَعْضِكُمْ لِبَعْضٍ أَن تَحْبَطَ أَعْمَٰلُكُمْ وَأَنتُمْ لَا تَشْعُرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku[1] bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصْوَٰتَهُمْ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ أُو۟لَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱمْتَحَنَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُمْ لِلتَّقْوَىٰ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ عَظِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle waɗanda ke runtsẽwar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne waɗanda Allah Yã, jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra mai girma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُنَادُونَكَ مِن وَرَآءِ ٱلْحُجُرَٰتِ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle waɗanda ke kiranka daga bãyan ɗakuna, mafi Yawansu bã su aiki da hankali.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَوْ أَنَّهُمْ صَبَرُوا۟ حَتَّىٰ تَخْرُجَ إِلَيْهِمْ لَكَانَ خَيْرًا لَّهُمْ وَٱللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma dã lalle sũ, sun yi haƙuri har ka fita zuwa gare su, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri gare su, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِن جَآءَكُمْ فَاسِقٌۢ بِنَبَإٍ فَتَبَيَّنُوٓا۟ أَن تُصِيبُوا۟ قَوْمًۢا بِجَهَٰلَةٍ فَتُصْبِحُوا۟ عَلَىٰ مَا فَعَلْتُمْ نَٰدِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi[1] Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ فِيكُمْ رَسُولَ ٱللَّهِ لَوْ يُطِيعُكُمْ فِى كَثِيرٍ مِّنَ ٱلْأَمْرِ لَعَنِتُّمْ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ حَبَّبَ إِلَيْكُمُ ٱلْإِيمَٰنَ وَزَيَّنَهُۥ فِى قُلُوبِكُمْ وَكَرَّهَ إِلَيْكُمُ ٱلْكُفْرَ وَٱلْفُسُوقَ وَٱلْعِصْيَانَ أُو۟لَٰٓئِكَ هُمُ ٱلرَّٰشِدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ku sani (cẽwa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Dã Yana bin ku ga (hãlãye) mãsu Yawa na al'amarin, dã kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Yã sõyar da ĩmãni a gare ku, kuma Yã ƙawãta shi a cikin zukãtanku kuma Yã ƙyãmantar da kãfirci da fãsicci da sãɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifõfin nan) su ne shiryayyu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَضْلًا مِّنَ ٱللَّهِ وَنِعْمَةً وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBisa ga falala daga Allah da ni'ima. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِن طَآئِفَتَانِ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ ٱقْتَتَلُوا۟ فَأَصْلِحُوا۟ بَيْنَهُمَا فَإِنۢ بَغَتْ إِحْدَىٰهُمَا عَلَى ٱلْأُخْرَىٰ فَقَٰتِلُوا۟ ٱلَّتِى تَبْغِى حَتَّىٰ تَفِىٓءَ إِلَىٰٓ أَمْرِ ٱللَّهِ فَإِن فَآءَتْ فَأَصْلِحُوا۟ بَيْنَهُمَا بِٱلْعَدْلِ وَأَقْسِطُوٓا۟ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلْمُقْسِطِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan jama'a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu da ãdalci kuma ku daidaita.[1] Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّمَا ٱلْمُؤْمِنُونَ إِخْوَةٌ فَأَصْلِحُوا۟ بَيْنَ أَخَوَيْكُمْ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMũminai 'yan'uwan jũna kawai ne, sabõda haka ku yi sulhu a tsakãnin 'yan'uwanku biyu, kuma ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, a yi muku rahama.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا يَسْخَرْ قَوْمٌ مِّن قَوْمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُوا۟ خَيْرًا مِّنْهُمْ وَلَا نِسَآءٌ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيْرًا مِّنْهُنَّ وَلَا تَلْمِزُوٓا۟ أَنفُسَكُمْ وَلَا تَنَابَزُوا۟ بِٱلْأَلْقَٰبِ بِئْسَ ٱلِٱسْمُ ٱلْفُسُوقُ بَعْدَ ٱلْإِيمَٰنِ وَمَن لَّمْ يَتُبْ فَأُو۟لَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱجْتَنِبُوا۟ كَثِيرًا مِّنَ ٱلظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ ٱلظَّنِّ إِثْمٌ وَلَا تَجَسَّسُوا۟ وَلَا يَغْتَب بَّعْضُكُم بَعْضًا أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَن يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ إِنَّ ٱللَّهَ تَوَّابٌ رَّحِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَٰكُم مِّن ذَكَرٍ وَأُنثَىٰ وَجَعَلْنَٰكُمْ شُعُوبًا وَقَبَآئِلَ لِتَعَارَفُوٓا۟ إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِندَ ٱللَّهِ أَتْقَىٰكُمْ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kũ mutãne![1] Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالَتِ ٱلْأَعْرَابُ ءَامَنَّا قُل لَّمْ تُؤْمِنُوا۟ وَلَٰكِن قُولُوٓا۟ أَسْلَمْنَا وَلَمَّا يَدْخُلِ ٱلْإِيمَٰنُ فِى قُلُوبِكُمْ وَإِن تُطِيعُوا۟ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ لَا يَلِتْكُم مِّنْ أَعْمَٰلِكُمْ شَيْـًٔا إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi¡auyãwa suka ce: "Mun yi ĩmãni." Ka ce: "Ba ku yi ĩmãni ba, amma dai ku ce, 'Mun mĩƙawuya, ĩmani bai gama shiga a cikinzukãtanku ba. Kuma idan kun yi ɗã'a ga Allah da Manzon Sa, to, bã zai rage muku kõme daga ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّمَا ٱلْمُؤْمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ لَمْ يَرْتَابُوا۟ وَجَٰهَدُوا۟ بِأَمْوَٰلِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ أُو۟لَٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّٰدِقُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMũminan gaskiya kawai, sũ ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, sa'an nan ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihãdi da dũkiyarsu da kuma rãyukansu, cikin tafarkin Allah. Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ أَتُعَلِّمُونَ ٱللَّهَ بِدِينِكُمْ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ مَا فِى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Kuna sanar da Allah ne game da addininku, alhãli kuwa Allah Yã san abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Allah Masani ne ga dukan kõme?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَمُنُّونَ عَلَيْكَ أَنْ أَسْلَمُوا۟ قُل لَّا تَمُنُّوا۟ عَلَىَّ إِسْلَٰمَكُم بَلِ ٱللَّهُ يَمُنُّ عَلَيْكُمْ أَنْ هَدَىٰكُمْ لِلْإِيمَٰنِ إِن كُنتُمْ صَٰدِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuna yin gõri a kanka wai sun musulunta. Ka ce: "Kada ku yi gõrin kun musulunta a kaina. Ã'a, Allah ne ke yi muku gõri dõmin Ya shiryar da ku ga ĩmãni, idan kun kasance mãsu gaskiya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ غَيْبَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَٱللَّهُ بَصِيرٌۢ بِمَا تَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Lalle Allah yanã sanin gaibin sammai da ¡asa, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70