Shafin farko › Surori › Suratu Adh-Dhaariyat
Suratu Adh-Dhaariyat الذاريات
Ayoyi 60 · Makka · tsarin saukarwa 67
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلذَّٰرِيَٰتِ ذَرْوًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱلْحَٰمِلَٰتِ وِقْرًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱلْجَٰرِيَٰتِ يُسْرًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱلْمُقَسِّمَٰتِ أَمْرًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَصَادِقٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ ٱلدِّينَ لَوَٰقِعٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلْحُبُكِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّكُمْ لَفِى قَوْلٍ مُّخْتَلِفٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يُؤْفَكُ عَنْهُ مَنْ أُفِكَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قُتِلَ ٱلْخَرَّٰصُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi An la'ani mãsu ƙiri-faɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِينَ هُمْ فِى غَمْرَةٍ سَاهُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَسْـَٔلُونَ أَيَّانَ يَوْمُ ٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَوْمَ هُمْ عَلَى ٱلنَّارِ يُفْتَنُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ذُوقُوا۟ فِتْنَتَكُمْ هَٰذَا ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تَسْتَعْجِلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى جَنَّٰتٍ وَعُيُونٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ءَاخِذِينَ مَآ ءَاتَىٰهُمْ رَبُّهُمْ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَبْلَ ذَٰلِكَ مُحْسِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَانُوا۟ قَلِيلًا مِّنَ ٱلَّيْلِ مَا يَهْجَعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَبِٱلْأَسْحَارِ هُمْ يَسْتَغْفِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفِىٓ أَمْوَٰلِهِمْ حَقٌّ لِّلسَّآئِلِ وَٱلْمَحْرُومِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفِى ٱلْأَرْضِ ءَايَٰتٌ لِّلْمُوقِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفِىٓ أَنفُسِكُمْ أَفَلَا تُبْصِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفِى ٱلسَّمَآءِ رِزْقُكُمْ وَمَا تُوعَدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَوَرَبِّ ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ إِنَّهُۥ لَحَقٌّ مِّثْلَ مَآ أَنَّكُمْ تَنطِقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ضَيْفِ إِبْرَٰهِيمَ ٱلْمُكْرَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ دَخَلُوا۟ عَلَيْهِ فَقَالُوا۟ سَلَٰمًا قَالَ سَلَٰمٌ قَوْمٌ مُّنكَرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَرَاغَ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ فَجَآءَ بِعِجْلٍ سَمِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَقَرَّبَهُۥٓ إِلَيْهِمْ قَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَوْجَسَ مِنْهُمْ خِيفَةً قَالُوا۟ لَا تَخَفْ وَبَشَّرُوهُ بِغُلَٰمٍ عَلِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَقْبَلَتِ ٱمْرَأَتُهُۥ فِى صَرَّةٍ فَصَكَّتْ وَجْهَهَا وَقَالَتْ عَجُوزٌ عَقِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوا۟ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْحَكِيمُ ٱلْعَلِيمُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا ٱلْمُرْسَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi (Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالُوٓا۟ إِنَّآ أُرْسِلْنَآ إِلَىٰ قَوْمٍ مُّجْرِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لِنُرْسِلَ عَلَيْهِمْ حِجَارَةً مِّن طِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ لِلْمُسْرِفِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَخْرَجْنَا مَن كَانَ فِيهَا مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَا وَجَدْنَا فِيهَا غَيْرَ بَيْتٍ مِّنَ ٱلْمُسْلِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَتَرَكْنَا فِيهَآ ءَايَةً لِّلَّذِينَ يَخَافُونَ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَلِيمَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفِى مُوسَىٰٓ إِذْ أَرْسَلْنَٰهُ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ بِسُلْطَٰنٍ مُّبِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَتَوَلَّىٰ بِرُكْنِهِۦ وَقَالَ سَٰحِرٌ أَوْ مَجْنُونٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَخَذْنَٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذْنَٰهُمْ فِى ٱلْيَمِّ وَهُوَ مُلِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفِى عَادٍ إِذْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمُ ٱلرِّيحَ ٱلْعَقِيمَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَا تَذَرُ مِن شَىْءٍ أَتَتْ عَلَيْهِ إِلَّا جَعَلَتْهُ كَٱلرَّمِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفِى ثَمُودَ إِذْ قِيلَ لَهُمْ تَمَتَّعُوا۟ حَتَّىٰ حِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَعَتَوْا۟ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِمْ فَأَخَذَتْهُمُ ٱلصَّٰعِقَةُ وَهُمْ يَنظُرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَا ٱسْتَطَٰعُوا۟ مِن قِيَامٍ وَمَا كَانُوا۟ مُنتَصِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَوْمًا فَٰسِقِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلسَّمَآءَ بَنَيْنَٰهَا بِأَيْي۟دٍ وَإِنَّا لَمُوسِعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلْأَرْضَ فَرَشْنَٰهَا فَنِعْمَ ٱلْمَٰهِدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمِن كُلِّ شَىْءٍ خَلَقْنَا زَوْجَيْنِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَفِرُّوٓا۟ إِلَى ٱللَّهِ إِنِّى لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَا تَجْعَلُوا۟ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ إِنِّى لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَٰلِكَ مَآ أَتَى ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا قَالُوا۟ سَاحِرٌ أَوْ مَجْنُونٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَتَوَاصَوْا۟ بِهِۦ بَلْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَتَوَلَّ عَنْهُمْ فَمَآ أَنتَ بِمَلُومٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَذَكِّرْ فَإِنَّ ٱلذِّكْرَىٰ تَنفَعُ ٱلْمُؤْمِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا خَلَقْتُ ٱلْجِنَّ وَٱلْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَآ أُرِيدُ مِنْهُم مِّن رِّزْقٍ وَمَآ أُرِيدُ أَن يُطْعِمُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلرَّزَّاقُ ذُو ٱلْقُوَّةِ ٱلْمَتِينُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ ذَنُوبًا مِّثْلَ ذَنُوبِ أَصْحَٰبِهِمْ فَلَا يَسْتَعْجِلُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِن يَوْمِهِمُ ٱلَّذِى يُوعَدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Qaaf
Suratu At-Tur →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.