caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Mutaffifin المطففين

Ayoyi 36 · Makka · tsarin saukarwa 86

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَيْلٌ لِّلْمُطَفِّفِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكْتَالُوا۟ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسْتَوْفُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan sun auna musu da zakka[1] ko da sikẽli, suna ragẽwa

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَا يَظُنُّ أُو۟لَٰٓئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِيَوْمٍ عَظِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDomin yini mai girma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ يَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلْفُجَّارِ لَفِى سِجِّينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiHaƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا سِجِّينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كِتَٰبٌ مَّرْقُومٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWani ittãfi ne rubũtacce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ ٱلدِّينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا يُكَذِّبُ بِهِۦٓ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBabũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiIdan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّا بَلْ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّآ إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّمَحْجُوبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُوا۟ ٱلْجَحِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلْأَبْرَارِ لَفِى عِلِّيِّينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كِتَٰبٌ مَّرْقُومٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWani littãfi ne rubũtacce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَشْهَدُهُ ٱلْمُقَرَّبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMuƙarrabai[1] suke halarta shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عَلَى ٱلْأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA kan karagu, suna ta kallo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تَعْرِفُ فِى وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ ٱلنَّعِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخْتُومٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAna shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

خِتَٰمُهُۥ مِسْكٌ وَفِى ذَٰلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ ٱلْمُتَنَٰفِسُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسْنِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا ٱلْمُقَرَّبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجْرَمُوا۟ كَانُوا۟ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ يَضْحَكُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَا مَرُّوا۟ بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓا۟ إِلَىٰٓ أَهْلِهِمُ ٱنقَلَبُوا۟ فَكِهِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوٓا۟ إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أُرْسِلُوا۟ عَلَيْهِمْ حَٰفِظِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAlhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱلْيَوْمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مِنَ ٱلْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عَلَى ٱلْأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA kan karagu, suna ta kallo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هَلْ ثُوِّبَ ٱلْكُفَّارُ مَا كَانُوا۟ يَفْعَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70