Suratu Al-Infitaar الإنفطار
Ayoyi 19 · Makka · tsarin saukarwa 82
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiIdan sama ta tsãge.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan taurãri suka wãtse.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْبِحَارُ فُجِّرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan tẽkuna aka facce su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْقُبُورُ بُعْثِرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan kaburbura aka tõne su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiRai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلْكَرِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِى خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِىٓ أَىِّ صُورَةٍ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَٰفِظِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كِرَامًا كَٰتِبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMãsu daraja, marubũta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã sanin abin da kuke aikatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ ٱلْفُجَّارَ لَفِى جَحِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ ٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiZã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَآئِبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã zã su faku daga gare ta ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ مَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْـًٔا وَٱلْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِّلَّهِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→