Shafin farko › Surori › Suratu Al-Inshiqaaq
Suratu Al-Inshiqaaq الإنشقاق
Ayoyi 25 · Makka · tsarin saukarwa 83
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Idan sama ta kẽce,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْأَرْضُ مُدَّتْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَلْقَتْ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَٰنُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدْحًا فَمُلَٰقِيهِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَوْفَ يُحَاسَبُ حِسَابًا يَسِيرًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيَنقَلِبُ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ مَسْرُورًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَٰبَهُۥ وَرَآءَ ظَهْرِهِۦ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَوْفَ يَدْعُوا۟ ثُبُورًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, zã shi dinga kiran halaka!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيَصْلَىٰ سَعِيرًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ya shiga sa'ĩr.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ كَانَ فِىٓ أَهْلِهِۦ مَسْرُورًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lale ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلَىٰٓ إِنَّ رَبَّهُۥ كَانَ بِهِۦ بَصِيرًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَآ أُقْسِمُ بِٱلشَّفَقِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلَّيْلِ وَمَا وَسَقَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da dare, da abin da ya ƙunsa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلْقَمَرِ إِذَا ٱتَّسَقَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da watã idan (haskensa) ya cika.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَتَرْكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَا لَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا قُرِئَ عَلَيْهِمُ ٱلْقُرْءَانُ لَا يَسْجُدُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يُكَذِّبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُوعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍۭ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Al-Mutaffifin
Suratu Al-Burooj →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.