caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu At-Tur الطور

Ayoyi 49 · Makka · tsarin saukarwa 76

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلطُّورِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiInã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَكِتَٰبٍ مَّسْطُورٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa wani littãfi rubũtacce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فِى رَقٍّ مَّنشُورٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْبَيْتِ ٱلْمَعْمُورِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلسَّقْفِ ٱلْمَرْفُوعِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa rufin nan da aka ɗaukaka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْبَحْرِ ٱلْمَسْجُورِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa tẽkun nan da aka cika (da ruwa).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَٰقِعٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَّا لَهُۥ مِن دَافِعٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã ta da mai tunkuɗẽwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ تَمُورُ ٱلسَّمَآءُ مَوْرًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَتَسِيرُ ٱلْجِبَالُ سَيْرًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَوَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ هُمْ فِى خَوْضٍ يَلْعَبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هَٰذِهِ ٱلنَّارُ ٱلَّتِى كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَفَسِحْرٌ هَٰذَآ أَمْ أَنتُمْ لَا تُبْصِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱصْلَوْهَا فَٱصْبِرُوٓا۟ أَوْ لَا تَصْبِرُوا۟ سَوَآءٌ عَلَيْكُمْ إِنَّمَا تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى جَنَّٰتٍ وَنَعِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٰكِهِينَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمْ رَبُّهُمْ وَوَقَىٰهُمْ رَبُّهُمْ عَذَابَ ٱلْجَحِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ هَنِيٓـًٔۢا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ سُرُرٍ مَّصْفُوفَةٍ وَزَوَّجْنَٰهُم بِحُورٍ عِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَٱتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَٰنٍ أَلْحَقْنَا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَمَآ أَلَتْنَٰهُم مِّنْ عَمَلِهِم مِّن شَىْءٍ كُلُّ ٱمْرِئٍۭ بِمَا كَسَبَ رَهِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu [1]suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَمْدَدْنَٰهُم بِفَٰكِهَةٍ وَلَحْمٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَتَنَٰزَعُونَ فِيهَا كَأْسًا لَّا لَغْوٌ فِيهَا وَلَا تَأْثِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ غِلْمَانٌ لَّهُمْ كَأَنَّهُمْ لُؤْلُؤٌ مَّكْنُونٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَآءَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوٓا۟ إِنَّا كُنَّا قَبْلُ فِىٓ أَهْلِنَا مُشْفِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَمَنَّ ٱللَّهُ عَلَيْنَا وَوَقَىٰنَا عَذَابَ ٱلسَّمُومِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلُ نَدْعُوهُ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْبَرُّ ٱلرَّحِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَذَكِّرْ فَمَآ أَنتَ بِنِعْمَتِ رَبِّكَ بِكَاهِنٍ وَلَا مَجْنُونٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ يَقُولُونَ شَاعِرٌ نَّتَرَبَّصُ بِهِۦ رَيْبَ ٱلْمَنُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ تَرَبَّصُوا۟ فَإِنِّى مَعَكُم مِّنَ ٱلْمُتَرَبِّصِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ تَأْمُرُهُمْ أَحْلَٰمُهُم بِهَٰذَآ أَمْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ يَقُولُونَ تَقَوَّلَهُۥ بَل لَّا يُؤْمِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلْيَأْتُوا۟ بِحَدِيثٍ مِّثْلِهِۦٓ إِن كَانُوا۟ صَٰدِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ خُلِقُوا۟ مِنْ غَيْرِ شَىْءٍ أَمْ هُمُ ٱلْخَٰلِقُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ خَلَقُوا۟ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ بَل لَّا يُوقِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ عِندَهُمْ خَزَآئِنُ رَبِّكَ أَمْ هُمُ ٱلْمُصَۣيْطِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ لَهُمْ سُلَّمٌ يَسْتَمِعُونَ فِيهِ فَلْيَأْتِ مُسْتَمِعُهُم بِسُلْطَٰنٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ لَهُ ٱلْبَنَٰتُ وَلَكُمُ ٱلْبَنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, Yanã da[1] 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ تَسْـَٔلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ عِندَهُمُ ٱلْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ يُرِيدُونَ كَيْدًا فَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ هُمُ ٱلْمَكِيدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْ لَهُمْ إِلَٰهٌ غَيْرُ ٱللَّهِ سُبْحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِن يَرَوْا۟ كِسْفًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ سَاقِطًا يَقُولُوا۟ سَحَابٌ مَّرْكُومٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَذَرْهُمْ حَتَّىٰ يُلَٰقُوا۟ يَوْمَهُمُ ٱلَّذِى فِيهِ يُصْعَقُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ لَا يُغْنِى عَنْهُمْ كَيْدُهُمْ شَيْـًٔا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ عَذَابًا دُونَ ذَٰلِكَ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعْيُنِنَا وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnun Mu, kuma ka tsarkake[1] Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَإِدْبَٰرَ ٱلنُّجُومِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) da lõkacin jũyãwar taurãri.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70