وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنْ عِلْمٍ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغْنِى مِنَ ٱلْحَقِّ شَيْـًٔا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.