Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saurũri (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui'ãni), mai ban mãmãki."
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba."
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai."
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa."
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne?"
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam."
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba."
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa."
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa."
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da Manzon Sa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada."
Hausa Translation - Abu Bakr JumiHar idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi.
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya[1] gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi."
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga."