caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Fajr الفجر

Ayoyi 30 · Makka · tsarin saukarwa 10

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلْفَجْرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiInã rantsuwa da alfijiri.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَيَالٍ عَشْرٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa darũruwa gõma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلشَّفْعِ وَٱلْوَتْرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa (adadi na) cikã da (na) mãrã.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّيْلِ إِذَا يَسْرِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa dare idan yana shũɗewa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هَلْ فِى ذَٰلِكَ قَسَمٌ لِّذِى حِجْرٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKo a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِرَمَ ذَاتِ ٱلْعِمَادِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiIramawa mãsu sakon[1] ƙĩrar jiki.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّتِى لَمْ يُخْلَقْ مِثْلُهَا فِى ٱلْبِلَٰدِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَثَمُودَ ٱلَّذِينَ جَابُوا۟ ٱلصَّخْرَ بِٱلْوَادِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi[1] suka yi gidãje)?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَفِرْعَوْنَ ذِى ٱلْأَوْتَادِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa Fir'auna mai turãku.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ طَغَوْا۟ فِى ٱلْبِلَٰدِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَكْثَرُوا۟ فِيهَا ٱلْفَسَادَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَابٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ رَبَّكَ لَبِٱلْمِرْصَادِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَمَّا ٱلْإِنسَٰنُ إِذَا مَا ٱبْتَلَىٰهُ رَبُّهُۥ فَأَكْرَمَهُۥ وَنَعَّمَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّىٓ أَكْرَمَنِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَمَّآ إِذَا مَا ٱبْتَلَىٰهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّىٓ أَهَٰنَنِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّا بَل لَّا تُكْرِمُونَ ٱلْيَتِيمَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا تَحَٰٓضُّونَ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَتَأْكُلُونَ ٱلتُّرَاثَ أَكْلًا لَّمًّا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَتُحِبُّونَ ٱلْمَالَ حُبًّا جَمًّا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma kuna son dũkiya, so mai yawa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّآ إِذَا دُكَّتِ ٱلْأَرْضُ دَكًّا دَكًّا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَآءَ رَبُّكَ وَٱلْمَلَكُ صَفًّا صَفًّا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, sahu- sahu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجِا۟ىٓءَ يَوْمَئِذٍۭ بِجَهَنَّمَ يَوْمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ ٱلْإِنسَٰنُ وَأَنَّىٰ لَهُ ٱلذِّكْرَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَقُولُ يَٰلَيْتَنِى قَدَّمْتُ لِحَيَاتِى

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَيَوْمَئِذٍ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُۥٓ أَحَدٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُۥٓ أَحَدٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurin Sa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَٰٓأَيَّتُهَا ٱلنَّفْسُ ٱلْمُطْمَئِنَّةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã kai rai mai natsuwa!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱرْجِعِىٓ إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةً مَّرْضِيَّةً

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱدْخُلِى فِى عِبَٰدِى

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõbda haka, ka shiga cikin bãyi Na (mãsu bin umurui a dũniya).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱدْخُلِى جَنَّتِى

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70