caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Balad البلد

Ayoyi 20 · Makka · tsarin saukarwa 35

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ لَآ أُقْسِمُ بِهَٰذَا ٱلْبَلَدِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã sai Na yi rantsuwa da wannan gari[1] ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنتَ حِلٌّۢ بِهَٰذَا ٱلْبَلَدِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAlhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَوَالِدٍ وَمَا وَلَدَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa mahaifi da abin da ya haifa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَٰنَ فِى كَبَدٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَيَحْسَبُ أَن لَّن يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَدٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالًا لُّبَدًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYana cẽwa "Na[1] halakarda dũkiya mai yawa,"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَيَحْسَبُ أَن لَّمْ يَرَهُۥٓ أَحَدٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَمْ نَجْعَل لَّهُۥ عَيْنَيْنِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلِسَانًا وَشَفَتَيْنِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa harshe, da leɓɓa biyu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَهَدَيْنَٰهُ ٱلنَّجْدَيْنِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi[1] biyu ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَا ٱقْتَحَمَ ٱلْعَقَبَةَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْعَقَبَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَكُّ رَقَبَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiIta ce fansar wuyan bãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَوْ إِطْعَٰمٌ فِى يَوْمٍ ذِى مَسْغَبَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKo kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiGa marãya ma'abũcin zumunta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKo kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ كَانَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَتَوَاصَوْا۟ بِٱلصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا۟ بِٱلْمَرْحَمَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أُو۟لَٰٓئِكَ أَصْحَٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗannan ne ma'abũta albarka[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِـَٔايَٰتِنَا هُمْ أَصْحَٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Mu, sũ ne ma'abũta shu'umci[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عَلَيْهِمْ نَارٌ مُّؤْصَدَةٌۢ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA kansu akwai wata wuta abar kullewa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70