Suratu Al-Ghaashiya الغاشية
Ayoyi 26 · Makka · tsarin saukarwa 68
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلْغَٰشِيَةِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ خَٰشِعَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَامِلَةٌ نَّاصِبَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
تَصْلَىٰ نَارًا حَامِيَةً
Hausa Translation - Abu Bakr JumiZã su shiga wata wuta mai zãfi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
تُسْقَىٰ مِنْ عَيْنٍ ءَانِيَةٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAna shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa su da wani abinci fãce dai daga danyi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِى مِن جُوعٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاعِمَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لِّسَعْيِهَا رَاضِيَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiGame da aikinsu, masu yarda ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِى جَنَّةٍ عَالِيَةٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّا تَسْمَعُ فِيهَا لَٰغِيَةً
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِيهَا عَيْنٌ جَارِيَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA cikinta akwai marmaro mai gudãna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِيهَا سُرُرٌ مَّرْفُوعَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَكْوَابٌ مَّوْضُوعَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa kõfuna ar'aje.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa filõli[1] jẽre,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَزَرَابِىُّ مَبْثُوثَةٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa katifu shimfiɗe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى ٱلْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِلَى ٱلسَّمَآءِ كَيْفَ رُفِعَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِلَى ٱلْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِلَى ٱلْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَذَكِّرْ إِنَّمَآ أَنتَ مُذَكِّرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumisabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّسْتَ عَلَيْهِم بِمُصَيْطِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiFãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَيُعَذِّبُهُ ٱللَّهُ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَكْبَرَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ إِلَيْنَآ إِيَابَهُمْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُم
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→