caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu An-Naazi'aat النازعات

Ayoyi 46 · Makka · tsarin saukarwa 81

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلنَّٰزِعَٰتِ غَرْقًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiIna rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلنَّٰشِطَٰتِ نَشْطًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلسَّٰبِحَٰتِ سَبْحًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱلسَّٰبِقَٰتِ سَبْقًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱلْمُدَبِّرَٰتِ أَمْرًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ تَرْجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تَتْبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَبْصَٰرُهَا خَٰشِعَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAlhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِى ٱلْحَافِرَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمًا نَّخِرَةً

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَالُوا۟ تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSuka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِنَّمَا هِىَ زَجْرَةٌ وَٰحِدَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, ita kam, tsãwa guda kawai ce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai kawai gã su a bãyan ƙasa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِذْ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلْوَادِ ٱلْمُقَدَّسِ طُوًى

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَهْدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخْشَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَرَىٰهُ ٱلْـَٔايَةَ ٱلْكُبْرَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ya nũna masa ãyar[1] nan mafi girma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَحَشَرَ فَنَادَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلْأَعْلَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلْـَٔاخِرَةِ وَٱلْأُولَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ءَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُ بَنَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَخْرَجَ مِنْهَا مَآءَهَا وَمَرْعَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْجِبَالَ أَرْسَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa duwatsu, Yã kafe ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَتَٰعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَٰمِكُمْ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDomin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِذَا جَآءَتِ ٱلطَّآمَّةُ ٱلْكُبْرَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ يَتَذَكَّرُ ٱلْإِنسَٰنُ مَا سَعَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَبُرِّزَتِ ٱلْجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَمَّا مَن طَغَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, amma wanda ya yi girman kai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَءَاثَرَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِنَّ ٱلْجَحِيمَ هِىَ ٱلْمَأْوَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفْسَ عَنِ ٱلْهَوَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِنَّ ٱلْجَنَّةَ هِىَ ٱلْمَأْوَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, lalle ne Aljanna ita ce makõma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَىٰهَآ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMe ya haɗã ka da ambatonta?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَآ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiZuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوٓا۟ إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70