caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu An-Naba النبإ

Ayoyi 40 · Makka · tsarin saukarwa 80

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA kan mẽ suke tambayar jũna?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلْعَظِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِى هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّا سَيَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Zã su sani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, a'aha! Zã su sani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَمْ نَجْعَلِ ٱلْأَرْضَ مِهَٰدًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْجِبَالَ أَوْتَادًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَخَلَقْنَٰكُمْ أَزْوَٰجًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَعَلْنَا ٱلَّيْلَ لِبَاسًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَعَلْنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَنزَلْنَا مِنَ ٱلْمُعْصِرَٰتِ مَآءً ثَجَّاجًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِّنُخْرِجَ بِهِۦ حَبًّا وَنَبَاتًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَنَّٰتٍ أَلْفَافًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa itãcen lambuna mãsu lillibniya?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ يَوْمَ ٱلْفَصْلِ كَانَ مِيقَٰتًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ يُنفَخُ فِى ٱلصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتْ أَبْوَٰبًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَسُيِّرَتِ ٱلْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِّلطَّٰغِينَ مَـَٔابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiGa mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَّٰبِثِينَ فِيهَآ أَحْقَابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiFãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

جَزَآءً وِفَاقًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSakamako mai dãcẽwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّهُمْ كَانُوا۟ لَا يَرْجُونَ حِسَابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَٰتِنَا كِذَّابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, ƙaryatãwa!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَكُلَّ شَىْءٍ أَحْصَيْنَٰهُ كِتَٰبًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAlhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَذُوقُوا۟ فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

حَدَآئِقَ وَأَعْنَٰبًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLambuna da inabõbi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa yan Mata tsaraikun Juna

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَكَأْسًا دِهَاقًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa hinjãlan giya cikakku.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّٰبًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

جَزَآءً مِّن رَّبِّكَ عَطَآءً حِسَابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

رَّبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ٱلرَّحْمَٰنِ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiUbangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ يَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلْمَلَٰٓئِكَةُ صَفًّا لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحْمَٰنُ وَقَالَ صَوَابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ذَٰلِكَ ٱلْيَوْمُ ٱلْحَقُّ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّآ أَنذَرْنَٰكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ ٱلْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ ٱلْكَافِرُ يَٰلَيْتَنِى كُنتُ تُرَٰبًۢا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70