caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Abasa عبس

Ayoyi 42 · Makka · tsarin saukarwa 24

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ عَبَسَ وَتَوَلَّىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYã game huska[1] kuma ya jũya bãya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَن جَآءَهُ ٱلْأَعْمَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda makãho yã je masa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُۥ يَزَّكَّىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ ٱلذِّكْرَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKo ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمَّا مَنِ ٱسْتَغْنَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAmma wanda ya wadãtu da dũkiya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسْعَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَهُوَ يَخْشَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAlhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَنتَ عَنْهُ تَلَهَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKai kuma kã shagala ga barinsa!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّآ إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda wanda ya so ya tuna Shi (Allah).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فِى صُحُفٍ مُّكَرَّمَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَّرْفُوعَةٍ مُّطَهَّرَةٍۭ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAbãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

بِأَيْدِى سَفَرَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA cikin hannãyen mala'iku marubũta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كِرَامٍۭ بَرَرَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُتِلَ ٱلْإِنسَٰنُ مَآ أَكْفَرَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAn la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مِنْ أَىِّ شَىْءٍ خَلَقَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDaga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مِن نُّطْفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDaga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقْبَرَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَآ أَمَرَهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiHaƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلْيَنظُرِ ٱلْإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَنَّا صَبَبْنَا ٱلْمَآءَ صَبًّا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ شَقَقْنَا ٱلْأَرْضَ شَقًّا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَنۢبَتْنَا فِيهَا حَبًّا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَعِنَبًا وَقَضْبًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa inabi da ciyãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa zaitũni da itãcen dabĩno.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَحَدَآئِقَ غُلْبًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa lambuna, mãsu yawan itãce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَفَٰكِهَةً وَأَبًّا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَّتَٰعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَٰمِكُمْ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDomin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ يَفِرُّ ٱلْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa uwarsa da ubansa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَصَٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa mãtarsa da ɗiyansa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِكُلِّ ٱمْرِئٍ مِّنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiGa kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُّسْفِرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ضَاحِكَةٌ مُّسْتَبْشِرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMãsu dãriya ne, mãsu bushãra.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBaƙi zai rufe su.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أُو۟لَٰٓئِكَ هُمُ ٱلْكَفَرَةُ ٱلْفَجَرَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70