Suratu Al-Mursalaat المرسلات
Ayoyi 50 · Makka · tsarin saukarwa 33
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلْمُرْسَلَٰتِ عُرْفًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiIna rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱلْعَٰصِفَٰتِ عَصْفًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلنَّٰشِرَٰتِ نَشْرًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱلْفَٰرِقَٰتِ فَرْقًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumisa'an nan, da ãyõyi[1] mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَٱلْمُلْقِيَٰتِ ذِكْرًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عُذْرًا أَوْ نُذْرًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDomin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan taurãri aka shãfe haskensu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, idan sama aka tsãge ta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْجِبَالُ نُسِفَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, idan duwãtsu aka nike su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لِأَىِّ يَوْمٍ أُجِّلَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDomin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لِيَوْمِ ٱلْفَصْلِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDomin rãnar rarrabẽwa.[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَلَمْ نُهْلِكِ ٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ نُتْبِعُهُمُ ٱلْـَٔاخِرِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِٱلْمُجْرِمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiHaka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَلَمْ نَخْلُقكُّم مِّن مَّآءٍ مَّهِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَجَعَلْنَٰهُ فِى قَرَارٍ مَّكِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَىٰ قَدَرٍ مَّعْلُومٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiZuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَقَدَرْنَا فَنِعْمَ ٱلْقَٰدِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَلَمْ نَجْعَلِ ٱلْأَرْضَ كِفَاتًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَحْيَآءً وَأَمْوَٰتًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiGa rãyayyu da matattu,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَجَعَلْنَا فِيهَا رَوَٰسِىَ شَٰمِخَٰتٍ وَأَسْقَيْنَٰكُم مَّآءً فُرَاتًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱنطَلِقُوٓا۟ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKu tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱنطَلِقُوٓا۟ إِلَىٰ ظِلٍّ ذِى ثَلَٰثِ شُعَبٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKu tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَّا ظَلِيلٍ وَلَا يُغْنِى مِنَ ٱللَّهَبِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiIta ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهَا تَرْمِى بِشَرَرٍ كَٱلْقَصْرِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَأَنَّهُۥ جِمَٰلَتٌ صُفْرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا يَوْمُ لَا يَنطِقُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَا يُؤْذَنُ لَهُمْ فَيَعْتَذِرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَٰذَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ جَمَعْنَٰكُمْ وَٱلْأَوَّلِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَإِن كَانَ لَكُمْ كَيْدٌ فَكِيدُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى ظِلَٰلٍ وَعُيُونٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشْتَهُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ هَنِيٓـًٔۢا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كُلُوا۟ وَتَمَتَّعُوا۟ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجْرِمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرْكَعُوا۟ لَا يَرْكَعُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَبِأَىِّ حَدِيثٍۭ بَعْدَهُۥ يُؤْمِنُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→