Shafin farko › Surori › Suratu Nooh
Suratu Nooh نوح
Ayoyi 28 · Makka · tsarin saukarwa 71
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ إِنَّآ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِۦٓ أَنْ أَنذِرْ قَوْمَكَ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ يَٰقَوْمِ إِنِّى لَكُمْ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَنِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُ وَأَطِيعُونِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõron Sa, kuma ku bĩ ni."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَغْفِرْ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمْ وَيُؤَخِّرْكُمْ إِلَىٰٓ أَجَلٍ مُّسَمًّى إِنَّ أَجَلَ ٱللَّهِ إِذَا جَآءَ لَا يُؤَخَّرُ لَوْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ رَبِّ إِنِّى دَعَوْتُ قَوْمِى لَيْلًا وَنَهَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَمْ يَزِدْهُمْ دُعَآءِىٓ إِلَّا فِرَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنِّى كُلَّمَا دَعَوْتُهُمْ لِتَغْفِرَ لَهُمْ جَعَلُوٓا۟ أَصَٰبِعَهُمْ فِىٓ ءَاذَانِهِمْ وَٱسْتَغْشَوْا۟ ثِيَابَهُمْ وَأَصَرُّوا۟ وَٱسْتَكْبَرُوا۟ ٱسْتِكْبَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ إِنِّى دَعَوْتُهُمْ جِهَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ إِنِّىٓ أَعْلَنتُ لَهُمْ وَأَسْرَرْتُ لَهُمْ إِسْرَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَقُلْتُ ٱسْتَغْفِرُوا۟ رَبَّكُمْ إِنَّهُۥ كَانَ غَفَّارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يُرْسِلِ ٱلسَّمَآءَ عَلَيْكُم مِّدْرَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيُمْدِدْكُم بِأَمْوَٰلٍ وَبَنِينَ وَيَجْعَل لَّكُمْ جَنَّٰتٍ وَيَجْعَل لَّكُمْ أَنْهَٰرًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَّا لَكُمْ لَا تَرْجُونَ لِلَّهِ وَقَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah,"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَدْ خَلَقَكُمْ أَطْوَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَلَمْ تَرَوْا۟ كَيْفَ خَلَقَ ٱللَّهُ سَبْعَ سَمَٰوَٰتٍ طِبَاقًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَجَعَلَ ٱلْقَمَرَ فِيهِنَّ نُورًا وَجَعَلَ ٱلشَّمْسَ سِرَاجًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱللَّهُ أَنۢبَتَكُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ نَبَاتًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ يُعِيدُكُمْ فِيهَا وَيُخْرِجُكُمْ إِخْرَاجًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ بِسَاطًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لِّتَسْلُكُوا۟ مِنْهَا سُبُلًا فِجَاجًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَالَ نُوحٌ رَّبِّ إِنَّهُمْ عَصَوْنِى وَٱتَّبَعُوا۟ مَن لَّمْ يَزِدْهُ مَالُهُۥ وَوَلَدُهُۥٓ إِلَّا خَسَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَكَرُوا۟ مَكْرًا كُبَّارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَالُوا۟ لَا تَذَرُنَّ ءَالِهَتَكُمْ وَلَا تَذَرُنَّ وَدًّا وَلَا سُوَاعًا وَلَا يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسْرًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Yans uƙa da Nasra."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَدْ أَضَلُّوا۟ كَثِيرًا وَلَا تَزِدِ ٱلظَّٰلِمِينَ إِلَّا ضَلَٰلًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مِّمَّا خَطِيٓـَٰٔتِهِمْ أُغْرِقُوا۟ فَأُدْخِلُوا۟ نَارًا فَلَمْ يَجِدُوا۟ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ أَنصَارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَقَالَ نُوحٌ رَّبِّ لَا تَذَرْ عَلَى ٱلْأَرْضِ مِنَ ٱلْكَٰفِرِينَ دَيَّارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّكَ إِن تَذَرْهُمْ يُضِلُّوا۟ عِبَادَكَ وَلَا يَلِدُوٓا۟ إِلَّا فَاجِرًا كَفَّارًا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyin Ka, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
رَّبِّ ٱغْفِرْ لِى وَلِوَٰلِدَىَّ وَلِمَن دَخَلَ بَيْتِىَ مُؤْمِنًا وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَٰتِ وَلَا تَزِدِ ٱلظَّٰلِمِينَ إِلَّا تَبَارًۢا
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi "Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka."
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Al-Ma'aarij
Suratu Al-Jinn →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.