caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Ma'aarij المعارج

Ayoyi 44 · Makka · tsarin saukarwa 79

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ سَأَلَ سَآئِلٌۢ بِعَذَابٍ وَاقِعٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِّلْكَٰفِرِينَ لَيْسَ لَهُۥ دَافِعٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiGa kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مِّنَ ٱللَّهِ ذِى ٱلْمَعَارِجِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDaga Allah Mai matãkala.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تَعْرُجُ ٱلْمَلَٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ إِلَيْهِ فِى يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُۥ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMalã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱصْبِرْ صَبْرًا جَمِيلًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّهُمْ يَرَوْنَهُۥ بَعِيدًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَنَرَىٰهُ قَرِيبًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Mu, Muna ganin ta a kusa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ تَكُونُ ٱلسَّمَآءُ كَٱلْمُهْلِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَتَكُونُ ٱلْجِبَالُ كَٱلْعِهْنِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا يَسْـَٔلُ حَمِيمٌ حَمِيمًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يُبَصَّرُونَهُمْ يَوَدُّ ٱلْمُجْرِمُ لَوْ يَفْتَدِى مِنْ عَذَابِ يَوْمِئِذٍۭ بِبَنِيهِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAna sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَصَٰحِبَتِهِۦ وَأَخِيهِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa matarsa da ɗan'uwansa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَفَصِيلَتِهِ ٱلَّتِى تُـْٔوِيهِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa danginsa, mãsu tattarã shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَن فِى ٱلْأَرْضِ جَمِيعًا ثُمَّ يُنجِيهِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّآ إِنَّهَا لَظَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

نَزَّاعَةً لِّلشَّوَىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMai twãle fãtar goshi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تَدْعُوا۟ مَنْ أَدْبَرَ وَتَوَلَّىٰ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَمَعَ فَأَوْعَىٰٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلْإِنسَٰنَ خُلِقَ هَلُوعًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ جَزُوعًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiIdan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَا مَسَّهُ ٱلْخَيْرُ مَنُوعًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَّا ٱلْمُصَلِّينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai mãsu yin salla,

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ دَآئِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ فِىٓ أَمْوَٰلِهِمْ حَقٌّ مَّعْلُومٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لِّلسَّآئِلِ وَٱلْمَحْرُومِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiGa (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوْمِ ٱلدِّينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ هُم مِّنْ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشْفِقُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمْ غَيْرُ مَأْمُونٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَٰفِظُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَّا عَلَىٰٓ أَزْوَٰجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَٰنُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَمَنِ ٱبْتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُو۟لَٰٓئِكَ هُمُ ٱلْعَادُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ هُمْ لِأَمَٰنَٰتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَٰعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ هُم بِشَهَٰدَٰتِهِمْ قَآئِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أُو۟لَٰٓئِكَ فِى جَنَّٰتٍ مُّكْرَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَمَالِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ قِبَلَكَ مُهْطِعِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عَنِ ٱلْيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ عِزِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDaga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَيَطْمَعُ كُلُّ ٱمْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُدْخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَلَّآ إِنَّا خَلَقْنَٰهُم مِّمَّا يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَآ أُقْسِمُ بِرَبِّ ٱلْمَشَٰرِقِ وَٱلْمَغَٰرِبِ إِنَّا لَقَٰدِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ خَيْرًا مِّنْهُمْ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiGa Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا۟ وَيَلْعَبُوا۟ حَتَّىٰ يُلَٰقُوا۟ يَوْمَهُمُ ٱلَّذِى يُوعَدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ يَخْرُجُونَ مِنَ ٱلْأَجْدَاثِ سِرَاعًا كَأَنَّهُمْ إِلَىٰ نُصُبٍ يُوفِضُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

خَٰشِعَةً أَبْصَٰرُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ذَٰلِكَ ٱلْيَوْمُ ٱلَّذِى كَانُوا۟ يُوعَدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMaƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70