Shafin farko › Surori › Suratu Al-Burooj
Suratu Al-Burooj البروج
Ayoyi 22 · Makka · tsarin saukarwa 27
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلْبُرُوجِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلْيَوْمِ ٱلْمَوْعُودِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَشَاهِدٍ وَمَشْهُودٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta[1] a cikinsa
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قُتِلَ أَصْحَٰبُ ٱلْأُخْدُودِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi An la'ani mutãnen rãmi.[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلْوَقُودِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wato wuta wadda aka hura.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَهُمْ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ بِٱلْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا نَقَمُوا۟ مِنْهُمْ إِلَّآ أَن يُؤْمِنُوا۟ بِٱللَّهِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْحَمِيدِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِى لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ شَهِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُوا۟ ٱلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَٰتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا۟ فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ ٱلْحَرِيقِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمْ جَنَّٰتٌ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَٰرُ ذَٰلِكَ ٱلْفَوْزُ ٱلْكَبِيرُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَهُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلْوَدُودُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ذُو ٱلْعَرْشِ ٱلْمَجِيدُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mai Al'arshi mai girma
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلْجُنُودِ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Fir'auna da samũdãwa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فِى تَكْذِيبٍ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱللَّهُ مِن وَرَآئِهِم مُّحِيطٌۢ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da sanin Sa).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلْ هُوَ قُرْءَانٌ مَّجِيدٌ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فِى لَوْحٍ مَّحْفُوظٍۭ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi A cikin Allo tsararre.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
← Suratu Al-Inshiqaaq
Suratu At-Taariq →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→
Rubutun Larabci da fassarori ta Tanzil da QuranEnc — kalma-da-kalma, ba a canza ba · Fassarori mallakar masu fassara ne kuma ba Alqur'ani kansa ba
Wannan kayan aikin bincike ne, ba tushen fatawa ba.