Suratu At-Taariq الطارق
Ayoyi 17 · Makka · tsarin saukarwa 36
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiInã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلطَّارِقُ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلنَّجْمُ ٱلثَّاقِبُ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShi ne taurãron nan mai tsananin haske.[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِن كُلُّ نَفْسٍ لَّمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلْيَنظُرِ ٱلْإِنسَٰنُ مِمَّ خُلِقَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
خُلِقَ مِن مَّآءٍ دَافِقٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAn halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَخْرُجُ مِنۢ بَيْنِ ٱلصُّلْبِ وَٱلتَّرَآئِبِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ عَلَىٰ رَجْعِهِۦ لَقَادِرٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
يَوْمَ تُبْلَى ٱلسَّرَآئِرُ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da ake jarrabawar asirai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَا لَهُۥ مِن قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSaboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلرَّجْعِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiIna rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلْأَرْضِ ذَاتِ ٱلصَّدْعِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa ƙasa ma'abociyar tsãgẽwa,[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ لَقَوْلٌ فَصْلٌ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا هُوَ بِٱلْهَزْلِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma shĩ bã bananci[1] bane
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَكِيدُ كَيْدًا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَمَهِّلِ ٱلْكَٰفِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًۢا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSaboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→