Suratu Al-A'laa الأعلى
Ayoyi 19 · Makka · tsarin saukarwa 8
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ سَبِّحِ ٱسْمَ رَبِّكَ ٱلْأَعْلَى
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِى خَلَقَ فَسَوَّىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلَّذِى قَدَّرَ فَهَدَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلَّذِىٓ أَخْرَجَ ٱلْمَرْعَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَجَعَلَهُۥ غُثَآءً أَحْوَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiZa mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُ إِنَّهُۥ يَعْلَمُ ٱلْجَهْرَ وَمَا يَخْفَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiFãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَذَكِّرْ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكْرَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَيَذَّكَّرُ مَن يَخْشَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَيَتَجَنَّبُهَا ٱلْأَشْقَى
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِى يَصْلَى ٱلنَّارَ ٱلْكُبْرَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda zai shiga wutar da tã fi girma.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَكَّىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَذَكَرَ ٱسْمَ رَبِّهِۦ فَصَلَّىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ya ambaci sũnan[1] Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بَلْ تُؤْثِرُونَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلْـَٔاخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAlhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ هَٰذَا لَفِى ٱلصُّحُفِ ٱلْأُولَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, wannan[1] yanã a cikin littafan farko.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
صُحُفِ إِبْرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLittaffan Ibrãhĩm da Mũsã.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→