Suratu Al-Alaq العلق
Ayoyi 19 · Makka · tsarin saukarwa 1
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ ٱقْرَأْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلَّذِى خَلَقَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
خَلَقَ ٱلْإِنسَٰنَ مِنْ عَلَقٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa hahitta mutum daga gudan jini.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱقْرَأْ وَرَبُّكَ ٱلْأَكْرَمُ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِى عَلَّمَ بِٱلْقَلَمِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَلَّمَ ٱلْإِنسَٰنَ مَا لَمْ يَعْلَمْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa sanar da mutum abin da bai sani ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَلَّآ إِنَّ ٱلْإِنسَٰنَ لَيَطْغَىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَن رَّءَاهُ ٱسْتَغْنَىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin yã ga kansa, yã wadãta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجْعَىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يَنْهَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, kã ga wanda ke hana.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَبْدًا إِذَا صَلَّىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBãwã idan yã yi salla?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَرَءَيْتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلْهُدَىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَوْ أَمَرَ بِٱلتَّقْوَىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKo ya yi umurni da taƙawa?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَرَءَيْتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
أَلَمْ يَعْلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAshe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَلَّا لَئِن لَّمْ يَنتَهِ لَنَسْفَعًۢا بِٱلنَّاصِيَةِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
نَاصِيَةٍ كَٰذِبَةٍ خَاطِئَةٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMakwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلْيَدْعُ نَادِيَهُۥ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ya kirayi ƙungiyarsa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
سَنَدْعُ ٱلزَّبَانِيَةَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiZã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
كَلَّا لَا تُطِعْهُ وَٱسْجُدْ وَٱقْتَرِب
Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,[1] kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→