caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Ash-Shams الشمس

Ayoyi 15 · Makka · tsarin saukarwa 26

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلشَّمْسِ وَضُحَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiIna rantsuwa da rãnã da hantsinta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma da wata idan ya bi ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa yini a lõkacin da ya bayyana ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa dare a lõkacin da ya ke rufe ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa sama da abin da ya gina ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْأَرْضِ وَمَا طَحَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَنَفْسٍ وَمَا سَوَّىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa rai da abin da ya daidaita shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne wanda ya tsarkake[1] shi (rai) ya sãmi babban rabo.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne wanda ya turbuɗe[1] shi (da laifi) ya tãɓe.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَىٰهَآ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSamũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشْقَىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقْيَٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمْ فَسَوَّىٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا يَخَافُ عُقْبَٰهَا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70