Suratu Al-Lail الليل
Ayoyi 21 · Makka · tsarin saukarwa 9
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiInã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا خَلَقَ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa abin da ya halitta namiji da mace.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَمَّا مَنْ أَعْطَىٰ وَٱتَّقَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَصَدَّقَ بِٱلْحُسْنَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ya gaskata kalma[1] mai kyãwo.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلْيُسْرَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَأَمَّا مَنۢ بَخِلَ وَٱسْتَغْنَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَكَذَّبَ بِٱلْحُسْنَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلْعُسْرَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا يُغْنِى عَنْهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLãlle aikin Mu ne, Mu bayyana shiriya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِنَّ لَنَا لَلْـَٔاخِرَةَ وَٱلْأُولَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لَا يَصْلَىٰهَآ إِلَّا ٱلْأَشْقَى
Hausa Translation - Abu Bakr JumiBãbu mai shigarta sai mafi Tabewa
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِى كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلْأَتْقَى
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma mafi taƙawa[1] zai nisance ta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلَّذِى يُؤْتِى مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعْمَةٍ تُجْزَىٰٓ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAlhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِلَّا ٱبْتِغَآءَ وَجْهِ رَبِّهِ ٱلْأَعْلَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiFãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَسَوْفَ يَرْضَىٰ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→