Suratu At-Takwir التكوير
Ayoyi 29 · Makka · tsarin saukarwa 7
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ إِذَا ٱلشَّمْسُ كُوِّرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiIdan rãna aka shafe haskenta
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْجِبَالُ سُيِّرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْعِشَارُ عُطِّلَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan rãƙuma mãsu cikunna[1] aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْوُحُوشُ حُشِرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْبِحَارُ سُجِّرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan rãyuka aka haɗa[1] su da jikunkunansu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْمَوْءُۥدَةُ سُئِلَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan wadda aka turbuɗe[1] ta da rai aka tambaye ta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
بِأَىِّ ذَنۢبٍ قُتِلَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiIdan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan sama aka fẽɗe ta.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْجَحِيمُ سُعِّرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan Jahĩm aka hũra ta
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَإِذَا ٱلْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّآ أَحْضَرَتْ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiRai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَلَآ أُقْسِمُ بِٱلْخُنَّسِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã[1] ba.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلْجَوَارِ ٱلْكُنَّسِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMãsu gudu suna ɓũya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa dare idan ya bãyar da bãya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَٱلصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa sãfiya idan ta yi lumfashi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنَّهُۥ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ذِى قُوَّةٍ عِندَ ذِى ٱلْعَرْشِ مَكِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مُّطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَلَقَدْ رَءَاهُ بِٱلْأُفُقِ ٱلْمُبِينِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne, yã gan shi[1] a cikin sararin sama mabayyani.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا هُوَ عَلَى ٱلْغَيْبِ بِضَنِينٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma shi, ga gaibi[1] bã mai rowa ba ne.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَٰنٍ رَّجِيمٍ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, a inã zã ku tafi?
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
لِمَن شَآءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiGa wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→