caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Ad-Dukhaan الدخان

Ayoyi 59 · Makka · tsarin saukarwa 64

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ حمٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiḤ. M̃.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱلْكِتَٰبِ ٱلْمُبِينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiInã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّآ أَنزَلْنَٰهُ فِى لَيْلَةٍ مُّبَٰرَكَةٍ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَمْرًا مِّنْ عِندِنَآ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiUmurni na daga wurin Mu. Lalle Mũ ne Muka kasance Mãsu aikãwã.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

رَبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَآ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْىِۦ وَيُمِيتُ رَبُّكُمْ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلْأَوَّلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBabu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

بَلْ هُمْ فِى شَكٍّ يَلْعَبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱرْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِى ٱلسَّمَآءُ بِدُخَانٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَغْشَى ٱلنَّاسَ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

رَّبَّنَا ٱكْشِفْ عَنَّا ٱلْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYa Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَنَّىٰ لَهُمُ ٱلذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَآءَهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiInã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ تَوَلَّوْا۟ عَنْهُ وَقَالُوا۟ مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa[1] ne, mahaukaci."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّا كَاشِفُوا۟ ٱلْعَذَابِ قَلِيلًا إِنَّكُمْ عَآئِدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ نَبْطِشُ ٱلْبَطْشَةَ ٱلْكُبْرَىٰٓ إِنَّا مُنتَقِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَآءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَنْ أَدُّوٓا۟ إِلَىَّ عِبَادَ ٱللَّهِ إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَن لَّا تَعْلُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ إِنِّىٓ ءَاتِيكُم بِسُلْطَٰنٍ مُّبِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنِّى عُذْتُ بِرَبِّى وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِن لَّمْ تُؤْمِنُوا۟ لِى فَٱعْتَزِلُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنَّ هَٰٓؤُلَآءِ قَوْمٌ مُّجْرِمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَسْرِ بِعِبَادِى لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَٱتْرُكِ ٱلْبَحْرَ رَهْوًا إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَمْ تَرَكُوا۟ مِن جَنَّٰتٍ وَعُيُونٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa yawa suka bar gõnaki da marẽmari.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa shuke-shuke da matsayi mai kyau.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَنَعْمَةٍ كَانُوا۟ فِيهَا فَٰكِهِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَذَٰلِكَ وَأَوْرَثْنَٰهَا قَوْمًا ءَاخَرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ ٱلسَّمَآءُ وَٱلْأَرْضُ وَمَا كَانُوا۟ مُنظَرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka [1]a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ مِنَ ٱلْعَذَابِ ٱلْمُهِينِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مِن فِرْعَوْنَ إِنَّهُۥ كَانَ عَالِيًا مِّنَ ٱلْمُسْرِفِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDaga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدِ ٱخْتَرْنَٰهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى ٱلْعَٰلَمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَءَاتَيْنَٰهُم مِّنَ ٱلْـَٔايَٰتِ مَا فِيهِ بَلَٰٓؤٌا۟ مُّبِينٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَيَقُولُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle waɗannan mutãne[1], haƙĩka, sunã cẽwa,

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنْ هِىَ إِلَّا مَوْتَتُنَا ٱلْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأْتُوا۟ بِـَٔابَآئِنَآ إِن كُنتُمْ صَٰدِقِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ أَهْلَكْنَٰهُمْ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ مُجْرِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumishin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا خَلَقْنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَٰعِبِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَا خَلَقْنَٰهُمَآ إِلَّا بِٱلْحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBa Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ يَوْمَ ٱلْفَصْلِ مِيقَٰتُهُمْ أَجْمَعِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ لَا يُغْنِى مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْـًٔا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَّا مَن رَّحِمَ ٱللَّهُ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumifãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ شَجَرَتَ ٱلزَّقُّومِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

طَعَامُ ٱلْأَثِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiIta ce abincin mai laifi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَٱلْمُهْلِ يَغْلِى فِى ٱلْبُطُونِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَغَلْىِ ٱلْحَمِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKamar tafasar ruwan zãfi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

خُذُوهُ فَٱعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَآءِ ٱلْجَحِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ صُبُّوا۟ فَوْقَ رَأْسِهِۦ مِنْ عَذَابِ ٱلْحَمِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْكَرِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi(A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ هَٰذَا مَا كُنتُم بِهِۦ تَمْتَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى مَقَامٍ أَمِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فِى جَنَّٰتٍ وَعُيُونٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَٰبِلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَٰهُم بِحُورٍ عِينٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyawun idãnu, mãsu girmansu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَٰكِهَةٍ ءَامِنِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَا يَذُوقُونَ فِيهَا ٱلْمَوْتَ إِلَّا ٱلْمَوْتَةَ ٱلْأُولَىٰ وَوَقَىٰهُمْ عَذَابَ ٱلْجَحِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِنَّمَا يَسَّرْنَٰهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiDõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱرْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.[1]

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70