Hausa Translation - Abu Bakr JumiKõ sunã cẽwa (Muhammadu ne) ya ƙirƙira shi? Ã'a, shĩ ne gaskiya daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda wani mai gargaɗi bai je musu ba a gabãninka, fãtan zã su shiryu.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAllah ne wanda Ya halitta sammai da ƙassai da abin da yake a tsakãninsu a cikin kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaita a kan Al'arshi. Bã ku da, baicin Shi, wani majiɓinci kuma babu wani maceci. Shin, bã zã ku yi tunãni ba?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiYanã shirya al'amari daga sama zuwa ga ƙasã, sa'an nan ya tãka zuwa gare Shi a cikin yini, wanda gwargwadonsa shẽkaru dubu ne ga abin da kuke lissafãwa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan Ya daidaita shi, kuma Ya hũra a cikinsa, daga ruhinSa kuma Ya sanya muku ji, da ganunuwa da zukãta. Gõdiyarku kaɗan ce ƙwarai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suka ce: "Shin, idan mun ɓace a cikin ƙasã, shin, lalle mu, tabbas ne munã zama a cikin wata halitta sãbuwa?" Ã'a, su game da gamuwa da Ubangijinsu kãfirai
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Mala, ikin mutuwa ne. wanda aka wakkala a gare ku, shĩ ne ke karɓar rãyukanku.[1] Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku."
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma da kã gani a lõkacin da mãsu laifi suke mãsu sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, "Ya Ubangijinmu! Mun gani, kuma mun ji, to, Ka mayar da mu mu aikata aiki na ƙwarai. Lalle mũ mãsu yaƙĩni ne."
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma dã Mun so dã Mun bai wa kõwane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata daga gare Ni! Lalle ne Inã cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, ku ɗanɗana sabõda abin da kuka manta na haɗuwa da ranarku wannan. Lalle Mũ mã Mun manta da ku, kuma ku dãnɗani azãbar dawwama sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda ke ĩmãni da ãyõyin Mu kawai, sũ ne waɗanda idan aka karanta musu ãyõyinMu sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma su yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, alhãli kuwa su bã su yin girman kai.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSãsanninsu nã nĩsanta daga wurãren kwanciya, sunã kiran Ubangijinsu bisa ga tsõro da ɗammãni, kuma sunã ciryawa daga abin da Muka azurta su.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka wani rai bai san abin da aka ɓõye musu ba, na sanyin idãnu, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAmma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwafai, to, sunã da gidãjen Aljannar makõma, a kan liyãfa sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka yi fãsiƙanci to makõmarsu ita ce wuta, kõ da yaushe suka yi nufin su fita daga gare ta, sai a mayar da su a cikinta, kuma a ce musu: "Ku ɗanɗana azãbai wutã, wadda kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda aka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa, sa'an na ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu laifi.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littafi,[1] sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga haɗuwa da shi. Kuma Mun sanya shi ya zama shiriya ga Banĩ Isrã'ĩla.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Mun sanya shugabanni daga cikinsu, sunã shiryarwa da umurnin Mu, a lõkacin da suka yi haƙuri, kuma sun kasance sunã yin yaƙĩni da ãyõyin Mu.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle Ubangijinka shĩ ne zai rarrabe a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa.
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, ba ya shiryar da su cẽwa da yawa Muka halakara gabãninsu, daga al'ummõmi sunã tafiya a cikin masaukansu?[1] Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi. Shin, ba su jĩ ne?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle Mũ, Munã kõra ruwa zuwa ga ƙasã ƙeƙasasshiya, sa'an nan Mu fitar, game da shi, wata shũka wadda dabbõbinsu, da su kansu ke ci daga gare ta? Ashe fa ba su gani ba?
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ranar hukuncin nan, ĩmãnin waɗanda suka kãfirta bã zai amfãne su ba (a cikinta) kuma bã zã a yi musu jinkiri ba."