ٱللَّهُ ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِى سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ ٱسْتَوَىٰ عَلَى ٱلْعَرْشِ مَا لَكُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَلِىٍّ وَلَا شَفِيعٍ أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiAllah ne wanda Ya halitta sammai da ƙassai da abin da yake a tsakãninsu a cikin kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaita a kan Al'arshi. Bã ku da, baicin Shi, wani majiɓinci kuma babu wani maceci. Shin, bã zã ku yi tunãni ba?