caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Qaari'a القارعة

Ayoyi 11 · Makka · tsarin saukarwa 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ ٱلْقَارِعَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَا ٱلْقَارِعَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْقَارِعَةُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

يَوْمَ يَكُونُ ٱلنَّاسُ كَٱلْفَرَاشِ ٱلْمَبْثُوثِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiRãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَتَكُونُ ٱلْجِبَالُ كَٱلْعِهْنِ ٱلْمَنفُوشِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَمَّا مَن ثَقُلَتْ مَوَٰزِينُهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَهُوَ فِى عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَٰزِينُهُۥ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأُمُّهُۥ هَاوِيَةٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, uwarsa Hãwiya ce.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا هِيَهْ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma me ya sanar da kai mece ce ita?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

نَارٌ حَامِيَةٌۢ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWata wuta ce mai kuna.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70