caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Al-Aadiyaat العاديات

Ayoyi 11 · Makka · tsarin saukarwa 14

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ وَٱلْعَٰدِيَٰتِ ضَبْحًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiIna rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱلْمُورِيَٰتِ قَدْحًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَٱلْمُغِيرَٰتِ صُبْحًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَثَرْنَ بِهِۦ نَقْعًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai su motsar da ƙũra game da shi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَوَسَطْنَ بِهِۦ جَمْعًا

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلْإِنسَٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلْخَيْرِ لَشَدِيدٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِى ٱلْقُبُورِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiShin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَحُصِّلَ مَا فِى ٱلصُّدُورِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiAka bayyana abin da ke cikin zukata.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ رَبَّهُم بِهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّخَبِيرٌۢ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70