caseriqBinciken ma'ana a cikin Alqur'ani

Suratu Fussilat فصلت

Ayoyi 54 · Makka · tsarin saukarwa 61

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ حمٓ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiḤ. M̃.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

تَنزِيلٌ مِّنَ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSaukarwa (da Alƙur' ãni) dãga Mai rahama ne, Mai jin ƙai.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

كِتَٰبٌ فُصِّلَتْ ءَايَٰتُهُۥ قُرْءَانًا عَرَبِيًّا لِّقَوْمٍ يَعْلَمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLittãfi ne, an bayyana ãyõyinsa daki-daki, yanã abin karantãwa na Lãrabci, dõmin mutãnen dake sani

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

بَشِيرًا وَنَذِيرًا فَأَعْرَضَ أَكْثَرُهُمْ فَهُمْ لَا يَسْمَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiYanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Sai mafi yawansu suka bijire. Sabõda haka sũ, bã su saurãrãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالُوا۟ قُلُوبُنَا فِىٓ أَكِنَّةٍ مِّمَّا تَدْعُونَآ إِلَيْهِ وَفِىٓ ءَاذَانِنَا وَقْرٌ وَمِنۢ بَيْنِنَا وَبَيْنِكَ حِجَابٌ فَٱعْمَلْ إِنَّنَا عَٰمِلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suka ce: "Zukatanmu nã a cikin kwasfa daga abin da kake Kiran mu zuwa gare shi, kuma a cikin kunnuwanmu akwai wani nauyi, kuma daga tsakaninmu da tsakaninka akwai wani shãmaki. sahõda haka ka yi aiki, lalle mũ mãsu aiki ne."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ يُوحَىٰٓ إِلَىَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمْ إِلَٰهٌ وَٰحِدٌ فَٱسْتَقِيمُوٓا۟ إِلَيْهِ وَٱسْتَغْفِرُوهُ وَوَيْلٌ لِّلْمُشْرِكِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Nĩ mutum kawai ne kamarku, ãnã yin wahayi zuwa gare ni cẽwa abin bautãwarku, abin bautãwa guda ne. Sai ku daidaitu zuwa gare Shi, kuma ku nẽmi gafararSa." Kuma bone ya tabbata ga mãsu yin shirki.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ٱلَّذِينَ لَا يُؤْتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلْـَٔاخِرَةِ هُمْ كَٰفِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗanda bã su bãyar da zakka, kuma sũ a game da Lãhira su kafirai ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle wɗdanda suka yi ĩmãni, Kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bai yankẽwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ أَئِنَّكُمْ لَتَكْفُرُونَ بِٱلَّذِى خَلَقَ ٱلْأَرْضَ فِى يَوْمَيْنِ وَتَجْعَلُونَ لَهُۥٓ أَندَادًا ذَٰلِكَ رَبُّ ٱلْعَٰلَمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ashe lalle kũ, haƙĩƙa, kunã kafurta a game da wanda Ya halitta kasã a cikin kwanuka biyu, kuma kunã sanya Masa kĩshiyõyi? Wancan fa, shĩ ne Ubangijin halittu."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَجَعَلَ فِيهَا رَوَٰسِىَ مِن فَوْقِهَا وَبَٰرَكَ فِيهَا وَقَدَّرَ فِيهَآ أَقْوَٰتَهَا فِىٓ أَرْبَعَةِ أَيَّامٍ سَوَآءً لِّلسَّآئِلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Ya sanya, a cikinta, dũwatsu kafaffu daga samanta, kuma Ya sanya albarka a cikinta, kuma Ya ƙaddara abũbuwan cinta a cikinta a cikin kwanuka huɗu mãsu daidaita, dõmin matambaya.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ثُمَّ ٱسْتَوَىٰٓ إِلَى ٱلسَّمَآءِ وَهِىَ دُخَانٌ فَقَالَ لَهَا وَلِلْأَرْضِ ٱئْتِيَا طَوْعًا أَوْ كَرْهًا قَالَتَآ أَتَيْنَا طَآئِعِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSa'an nan Ya daidaita zuwa ga sama alhãli kuwa ita (a lõkacin) hayãƙi ce, sai Ya ce mata, ita da ƙasã "Ku zo, bisa ga yarda kõ a kan tĩlas." Suka ce: "Mun zo, munã mãsu ɗã'ã. "

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَقَضَىٰهُنَّ سَبْعَ سَمَٰوَاتٍ فِى يَوْمَيْنِ وَأَوْحَىٰ فِى كُلِّ سَمَآءٍ أَمْرَهَا وَزَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنْيَا بِمَصَٰبِيحَ وَحِفْظًا ذَٰلِكَ تَقْدِيرُ ٱلْعَزِيزِ ٱلْعَلِيمِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai Ya hukunta su sammai bakwai a cikin kwãnuka biyu. Kuma Ya yi wahayi, a cikin kõwace sama da al'amarinta, kuma Muka kãwata sama ta kusa da fitilu kuma don tsari. Wancan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِنْ أَعْرَضُوا۟ فَقُلْ أَنذَرْتُكُمْ صَٰعِقَةً مِّثْلَ صَٰعِقَةِ عَادٍ وَثَمُودَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan sun bijire sai ka ce: "Nã yi muku gargaɗi ga wata tsãwa kamar irin tsãwar Ãdãwa da samũdãwa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِذْ جَآءَتْهُمُ ٱلرُّسُلُ مِنۢ بَيْنِ أَيْدِيهِمْ وَمِنْ خَلْفِهِمْ أَلَّا تَعْبُدُوٓا۟ إِلَّا ٱللَّهَ قَالُوا۟ لَوْ شَآءَ رَبُّنَا لَأَنزَلَ مَلَٰٓئِكَةً فَإِنَّا بِمَآ أُرْسِلْتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiA lõkacin da Manzanninsu suka je musu daga gaba gare su kuma daga bãyansu, "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah." suka ce: "Dã UbangiJinmu Yã so, lalle dã Ya saukar da malã' iku, sabõda haka lalle mũ, mãsu kafirta ne a game da abin da aka aiko ku da shi."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَمَّا عَادٌ فَٱسْتَكْبَرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ بِغَيْرِ ٱلْحَقِّ وَقَالُوا۟ مَنْ أَشَدُّ مِنَّا قُوَّةً أَوَلَمْ يَرَوْا۟ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِى خَلَقَهُمْ هُوَ أَشَدُّ مِنْهُمْ قُوَّةً وَكَانُوا۟ بِـَٔايَٰتِنَا يَجْحَدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, amma Ãdãwa, sai suka yi girman kai a cikin kasã, bã da wani hakki ba, suka ce: "Wãne ne mafi tsananin ƙarfi daga gare mu?" Ashe, kuma ba su gani ba cẽwa Allah, wanda Ya halitta su Shĩne Mafi ƙarfi daga gare su, kuma sun kasance a game da ãyõyin Mu suna yin musu?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِيحًا صَرْصَرًا فِىٓ أَيَّامٍ نَّحِسَاتٍ لِّنُذِيقَهُمْ عَذَابَ ٱلْخِزْىِ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَلَعَذَابُ ٱلْـَٔاخِرَةِ أَخْزَىٰ وَهُمْ لَا يُنصَرُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSai Muka aika, a kansu, da iska mai tsananin sauti da sanyi, a cikin kwãnuka na shu'umci, dõmin Mu ɗanɗana musu azãbar wulãƙanci, a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi wulãƙantarwa, kuma sũ bã zã a taimake su ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَأَمَّا ثَمُودُ فَهَدَيْنَٰهُمْ فَٱسْتَحَبُّوا۟ ٱلْعَمَىٰ عَلَى ٱلْهُدَىٰ فَأَخَذَتْهُمْ صَٰعِقَةُ ٱلْعَذَابِ ٱلْهُونِ بِمَا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma amma Samũdãwa, sai Muka shiryar da su, sai suka fi son makanta a kan shiriya, dõmin haka tsawar azãbar wulãkanci, ta kamã su sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa (dõmin nẽman wata fã'ida).

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَنَجَّيْنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَكَانُوا۟ يَتَّقُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَيَوْمَ يُحْشَرُ أَعْدَآءُ ٱللَّهِ إِلَى ٱلنَّارِ فَهُمْ يُوزَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma rãnar da ake tãra maƙiyan Allah zuwa wutã, to, sũ anã kakkange su.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

حَتَّىٰٓ إِذَا مَا جَآءُوهَا شَهِدَ عَلَيْهِمْ سَمْعُهُمْ وَأَبْصَٰرُهُمْ وَجُلُودُهُم بِمَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiHar idan sun jẽ mata, sai jinsu da ganinsu da fãtunsu, su yi shaida a kansu a game da abin da suka kasance sunã aikatawa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالُوا۟ لِجُلُودِهِمْ لِمَ شَهِدتُّمْ عَلَيْنَا قَالُوٓا۟ أَنطَقَنَا ٱللَّهُ ٱلَّذِىٓ أَنطَقَ كُلَّ شَىْءٍ وَهُوَ خَلَقَكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma suka ce wa fãtunsu, "Don me kuka yi shaida a kanmu?" Suka ce: "Allah, Wanda ke sanya kõwane abu ya yi furuci, Shĩ ne Ya sanya mu mu yi furuci, kuma Shĩ ne Ya halitta ku can da farko, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا كُنتُمْ تَسْتَتِرُونَ أَن يَشْهَدَ عَلَيْكُمْ سَمْعُكُمْ وَلَآ أَبْصَٰرُكُمْ وَلَا جُلُودُكُمْ وَلَٰكِن ظَنَنتُمْ أَنَّ ٱللَّهَ لَا يَعْلَمُ كَثِيرًا مِّمَّا تَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Ba ku kasance kunã sani ba a ɓõye, cẽwa jinku zai yi shaida a kanku kuma ganinku zai yi, kuma fãtunku za su yi. Kuma amma kun yi zaton cẽwã Allah bai san abũbuwa mãsu yawa daga abin da kuke aikatãwa ba."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَذَٰلِكُمْ ظَنُّكُمُ ٱلَّذِى ظَنَنتُم بِرَبِّكُمْ أَرْدَىٰكُمْ فَأَصْبَحْتُم مِّنَ ٱلْخَٰسِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Kuma wancan zaton nãku wanda kuka yi zaton shi, game da Ubangijinku, ya halakar da ku, sai kuka wãyi gari a cikin mãsu hasãra."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِن يَصْبِرُوا۟ فَٱلنَّارُ مَثْوًى لَّهُمْ وَإِن يَسْتَعْتِبُوا۟ فَمَا هُم مِّنَ ٱلْمُعْتَبِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka idan sun yi hakuri, to, wutar, ita ce mazauni a gare su, kuma idan sun nẽmi yarda, to, ba su zama daga waɗanda ake yardwa ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَيَّضْنَا لَهُمْ قُرَنَآءَ فَزَيَّنُوا۟ لَهُم مَّا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَحَقَّ عَلَيْهِمُ ٱلْقَوْلُ فِىٓ أُمَمٍ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِم مِّنَ ٱلْجِنِّ وَٱلْإِنسِ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ خَٰسِرِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma Muka sallaɗar da mabiya[1] a gare su, sai suka ƙawãta musu abin da ke a gabansu da abin da ke a bãyansu. Kuma kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin wasu al'ummõmi da suka shũɗe a gabãninsu daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَا تَسْمَعُوا۟ لِهَٰذَا ٱلْقُرْءَانِ وَٱلْغَوْا۟ فِيهِ لَعَلَّكُمْ تَغْلِبُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka kafirta suka cc, "Kada ku saurãra ga wannan Alkur' ãni, kuma ku yi ta yin kuwwa a ckin (lõkacin karãtun) sa, tsammãninku zã ku rinjaya."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَلَنُذِيقَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ عَذَابًا شَدِيدًا وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَسْوَأَ ٱلَّذِى كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiSabõda haka, lalle zã Mu ɗanɗana wa waɗanda suka kafirta wata azãba mai tsanani, kuma lalle zã Mu sãka musu da mafi mũnin abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

ذَٰلِكَ جَزَآءُ أَعْدَآءِ ٱللَّهِ ٱلنَّارُ لَهُمْ فِيهَا دَارُ ٱلْخُلْدِ جَزَآءًۢ بِمَا كَانُوا۟ بِـَٔايَٰتِنَا يَجْحَدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWancan shĩ ne sakamakon makiyan Allah, watau wuta. Sunã a gidan dawwama a cikinta, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã yin musu game da ãyõyin Mu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ رَبَّنَآ أَرِنَا ٱلَّذَيْنِ أَضَلَّانَا مِنَ ٱلْجِنِّ وَٱلْإِنسِ نَجْعَلْهُمَا تَحْتَ أَقْدَامِنَا لِيَكُونَا مِنَ ٱلْأَسْفَلِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka nũnã mana wadannan biyun da suka batar da mu daga aljannu da mutãne, mu sanya su a karkashin, ƙafãfunmu, dõmin su kasance daga ƙaskantattu."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلَّذِينَ قَالُوا۟ رَبُّنَا ٱللَّهُ ثُمَّ ٱسْتَقَٰمُوا۟ تَتَنَزَّلُ عَلَيْهِمُ ٱلْمَلَٰٓئِكَةُ أَلَّا تَخَافُوا۟ وَلَا تَحْزَنُوا۟ وَأَبْشِرُوا۟ بِٱلْجَنَّةِ ٱلَّتِى كُنتُمْ تُوعَدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle waɗannan da suka ce: "Ubangjinmu, shĩ ne Allah," sa'an nan suka daidaitu, malã'iku na sassauka a kansu (a lõkacin saukar ajalinsu sunã ce musu) "Kada ku ji tsõro, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi bushãra da Aljanna, wadda kun kasance anã yi muku wa'adi da ita."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

نَحْنُ أَوْلِيَآؤُكُمْ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَفِى ٱلْـَٔاخِرَةِ وَلَكُمْ فِيهَا مَا تَشْتَهِىٓ أَنفُسُكُمْ وَلَكُمْ فِيهَا مَا تَدَّعُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"Mũ ne majibintanku a cikin rãyuwar dũniya da kuma a cikin Lãhira, kuma a cikinta kunã da abin da rãyukanku ke sha'awa, kuma kunã da abin da kuke kira (akawo muku) a cikinta.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

نُزُلًا مِّنْ غَفُورٍ رَّحِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi"A kan liyãfa daga Mai gafara, Mai jin ƙai."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَنْ أَحْسَنُ قَوْلًا مِّمَّن دَعَآ إِلَى ٱللَّهِ وَعَمِلَ صَٰلِحًا وَقَالَ إِنَّنِى مِنَ ٱلْمُسْلِمِينَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma wãne ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na ƙwarai kuma ya ce: "Lalle nĩinã daga mãsu sallamãwar al'amari zuwa ga Allah?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَا تَسْتَوِى ٱلْحَسَنَةُ وَلَا ٱلسَّيِّئَةُ ٱدْفَعْ بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ فَإِذَا ٱلَّذِى بَيْنَكَ وَبَيْنَهُۥ عَدَٰوَةٌ كَأَنَّهُۥ وَلِىٌّ حَمِيمٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma kyautatãwa bã ta daidaita kuma haka mũnanãwa. Ka tunkuɗe cũta da abin da yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai ƙiyayya a tsakaninka da tsakaninsa, kamar dai shi majibinci ne, masoyi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلَّذِينَ صَبَرُوا۟ وَمَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ذُو حَظٍّ عَظِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma bã za a cũsa wa kõwa wannan hãli ba fãce waɗanda suka yi haƙuri, kuma bã zã a cũsa shi ba fãce ga mai rabo mai gima.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ ٱلشَّيْطَٰنِ نَزْغٌ فَٱسْتَعِذْ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan wata fizga ta fizge ka daga Shaiɗan, to ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Masani.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمِنْ ءَايَٰتِهِ ٱلَّيْلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمْسُ وَٱلْقَمَرُ لَا تَسْجُدُوا۟ لِلشَّمْسِ وَلَا لِلْقَمَرِ وَٱسْجُدُوا۟ لِلَّهِ ٱلَّذِى خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma akwai daga ãyõyin Sa, dare da yini, da rãnã da watã. Kada ku yi sujada ga rãnã, kuma kada ku yi ga watã. Kuma ku yi sujada ga Allah wanda Ya halitta su, idan kun kasance Shĩ ne kuke bauta wa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

فَإِنِ ٱسْتَكْبَرُوا۟ فَٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ يُسَبِّحُونَ لَهُۥ بِٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ وَهُمْ لَا يَسْـَٔمُونَ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo, idan sun yi girman kai, to, waɗanda ke a wurin Ubangijinka, sunã tasbĩhi a gare Shi, a dare da rana, alhãli kuwa sũ, bã su ƙõsãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَمِنْ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنَّكَ تَرَى ٱلْأَرْضَ خَٰشِعَةً فَإِذَآ أَنزَلْنَا عَلَيْهَا ٱلْمَآءَ ٱهْتَزَّتْ وَرَبَتْ إِنَّ ٱلَّذِىٓ أَحْيَاهَا لَمُحْىِ ٱلْمَوْتَىٰٓ إِنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma akwai daga ãyõyinSa cẽwa lalle kai kanã ganin ƙasã ƙẽƙasasshiya, to, idan Mun saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura. Lalle wannan da Ya rãya ta, haƙĩƙa, Mai rãyar da matattu ne. Lalle Shĩ Mai ĩkon yi ne a kan kõwane abu.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُلْحِدُونَ فِىٓ ءَايَٰتِنَا لَا يَخْفَوْنَ عَلَيْنَآ أَفَمَن يُلْقَىٰ فِى ٱلنَّارِ خَيْرٌ أَم مَّن يَأْتِىٓ ءَامِنًا يَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِ ٱعْمَلُوا۟ مَا شِئْتُمْ إِنَّهُۥ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiLalle waɗannan da ke karkacẽwa a cikin ãyõyinMu, bã su fakuwa a gare Mu. Ashe fa, wanda ake jẽfãwa a cikin Wutã ne mafĩfĩci kõ kuwa wanda zai je amintacce a Rãnar ¡iyãma? Ku aikata abin da kuke so! Lalle Shĩ Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِٱلذِّكْرِ لَمَّا جَآءَهُمْ وَإِنَّهُۥ لَكِتَٰبٌ عَزِيزٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWaɗannan da suka kãfirta game da Alkur'ãni a lõkacin da ya je musu, kuma lalle shi haƙĩƙa littãfi ne mabuwãyi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَّا يَأْتِيهِ ٱلْبَٰطِلُ مِنۢ بَيْنِ يَدَيْهِ وَلَا مِنْ خَلْفِهِۦ تَنزِيلٌ مِّنْ حَكِيمٍ حَمِيدٍ

Hausa Translation - Abu Bakr Jumi¥arna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi. kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Gõdadde.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَّا يُقَالُ لَكَ إِلَّا مَا قَدْ قِيلَ لِلرُّسُلِ مِن قَبْلِكَ إِنَّ رَبَّكَ لَذُو مَغْفِرَةٍ وَذُو عِقَابٍ أَلِيمٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiBã zã a fada maka ba fãce abin da aka riga aka faɗa ga Manzannin da suke a gabãninka. Lalle Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne, kuma Ma'abũcin azãba mai raɗaɗi ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَوْ جَعَلْنَٰهُ قُرْءَانًا أَعْجَمِيًّا لَّقَالُوا۟ لَوْلَا فُصِّلَتْ ءَايَٰتُهُۥٓ ءَا۬عْجَمِىٌّ وَعَرَبِىٌّ قُلْ هُوَ لِلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ هُدًى وَشِفَآءٌ وَٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ فِىٓ ءَاذَانِهِمْ وَقْرٌ وَهُوَ عَلَيْهِمْ عَمًى أُو۟لَٰٓئِكَ يُنَادَوْنَ مِن مَّكَانٍۭ بَعِيدٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma da Mun sanya shi abin karãtu na ajamanci, lalle dã sun ce, "Don me ba a bayyana ãyõyinsa ba? Ashe, zai yiwu a sãmi littãfi ba'ajame da Manzo Balãrabe?" Ka ce: "Shi, shiriya ne da warkewa ga waɗanda suka yi ĩmãni. Kuma wadanda ba su yi ĩmãni ba akwai wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma shi wata makanta ne a kansu. Waɗannan anã kiran su daga wuri mai nĩsa."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا مُوسَى ٱلْكِتَٰبَ فَٱخْتُلِفَ فِيهِ وَلَوْلَا كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ لَقُضِىَ بَيْنَهُمْ وَإِنَّهُمْ لَفِى شَكٍّ مِّنْهُ مُرِيبٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle Mun bai wa Mũsã Littãfi, sai aka yi ɗãɓãni a cikinsa, Kuma ba dõmin wata kalma da tã gabata ba daga Ubangijinka, lalle dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle sũ, haƙĩƙa sunã a cikin shakka daga, gare shi, mai sanya kõkanto.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

مَّنْ عَمِلَ صَٰلِحًا فَلِنَفْسِهِۦ وَمَنْ أَسَآءَ فَعَلَيْهَا وَمَا رَبُّكَ بِظَلَّٰمٍ لِّلْعَبِيدِ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiWanda ya aikata aiki na ƙwarai to sabõda kansa ne, kuma wanda ya mũnanã, to, yanã akansa. Kuma Ubangiwinka, bã Mai zãlunci ga bãyin Sa ne ba.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

إِلَيْهِ يُرَدُّ عِلْمُ ٱلسَّاعَةِ وَمَا تَخْرُجُ مِن ثَمَرَٰتٍ مِّنْ أَكْمَامِهَا وَمَا تَحْمِلُ مِنْ أُنثَىٰ وَلَا تَضَعُ إِلَّا بِعِلْمِهِۦ وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ أَيْنَ شُرَكَآءِى قَالُوٓا۟ ءَاذَنَّٰكَ مَا مِنَّا مِن شَهِيدٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiZuwa gare Shi ake mayar da sanin Sa'a. Kuma waɗansu 'yã'yan itãce bã su fita daga kwasfõfinsu, kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma a rãnar da Yake kiran su (Ya ce): "Inã abõkan tãrayyaTa?" Sai su ce, "Mun sanar da Kai bãbu mai bãyar da shaida da haka nan daga gare mu."

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَدْعُونَ مِن قَبْلُ وَظَنُّوا۟ مَا لَهُم مِّن مَّحِيصٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma abin da suka kasance sunã kira a gabãnin haka ya ɓace musu, kuma suka yi zaton cẽwa bã su da wata mafakã.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

لَّا يَسْـَٔمُ ٱلْإِنسَٰنُ مِن دُعَآءِ ٱلْخَيْرِ وَإِن مَّسَّهُ ٱلشَّرُّ فَيَـُٔوسٌ قَنُوطٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiMutum bã ya kõsãwa daga addu 'ar nẽman alhẽri kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya zama mai yanke kauna, Mai nũna kãsãwa.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَلَئِنْ أَذَقْنَٰهُ رَحْمَةً مِّنَّا مِنۢ بَعْدِ ضَرَّآءَ مَسَّتْهُ لَيَقُولَنَّ هَٰذَا لِى وَمَآ أَظُنُّ ٱلسَّاعَةَ قَآئِمَةً وَلَئِن رُّجِعْتُ إِلَىٰ رَبِّىٓ إِنَّ لِى عِندَهُۥ لَلْحُسْنَىٰ فَلَنُنَبِّئَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِمَا عَمِلُوا۟ وَلَنُذِيقَنَّهُم مِّنْ عَذَابٍ غَلِيظٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma lalle idan Mun ɗanɗana masa wata rahama daga gareMu, daga bãyan wata cũta ta shãfe shi, lalle zai ce, "Wannan (ni'ima) tãwa ce kuma bã ni zaton Sã'a mai tsayuwa ce, kuma lalle idan aka mayar da ni zuwa ga Ubangijĩna, haƙĩƙa, inã da makõma mafi kyau, a wurin Sa." To, lalle zã Mu bã da lãbãri ga waɗanda suka kãfirta game da abin da suka aikata, kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, Mai kauri.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

وَإِذَآ أَنْعَمْنَا عَلَى ٱلْإِنسَٰنِ أَعْرَضَ وَنَـَٔا بِجَانِبِهِۦ وَإِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ فَذُو دُعَآءٍ عَرِيضٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma idan Muka yi ni'ima ga mutum, sai ya bijire, kuma ya nĩsantar da gẽfensa, kuma idan sharri ya sãme shi, sai ya zama ma'abũcin addu'a mai fãɗi.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِن كَانَ مِنْ عِندِ ٱللَّهِ ثُمَّ كَفَرْتُم بِهِۦ مَنْ أَضَلُّ مِمَّنْ هُوَ فِى شِقَاقٍۭ بَعِيدٍ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa ce: "Ashe, kun gani! Idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga Allah ne, sa'an nan kun kãfirta a game da Shi, wãne ne mafi ɓata daga wanda yake yanã a cikin sãɓani manisanci (daga gaskiya)?"

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

سَنُرِيهِمْ ءَايَٰتِنَا فِى ٱلْـَٔافَاقِ وَفِىٓ أَنفُسِهِمْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُ ٱلْحَقُّ أَوَلَمْ يَكْفِ بِرَبِّكَ أَنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ شَهِيدٌ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiZã Mu nũna musu ãyõyin Mu a cikin sãsanni da kuma cikin rãyukansu, har ya bayyana a gare su cẽwã lalle (Alƙur'ãni), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cẽwa lalle Shĩ halartacce ne a kan kowane abu ne?

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

أَلَآ إِنَّهُمْ فِى مِرْيَةٍ مِّن لِّقَآءِ رَبِّهِمْ أَلَآ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَىْءٍ مُّحِيطٌۢ

Hausa Translation - Abu Bakr JumiTo lalle sũ, sunã a cikin shakka daga gamuwa da Ubangijinsu. To, lalle Shĩ, Mai kẽwayẽwane ga dukan kõme ne.

Duba dukkan fassarorin wannan aya →

Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
Harshe — 70