وَأَمَّا ثَمُودُ فَهَدَيْنَٰهُمْ فَٱسْتَحَبُّوا۟ ٱلْعَمَىٰ عَلَى ٱلْهُدَىٰ فَأَخَذَتْهُمْ صَٰعِقَةُ ٱلْعَذَابِ ٱلْهُونِ بِمَا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKuma amma Samũdãwa, sai Muka shiryar da su, sai suka fi son makanta a kan shiriya, dõmin haka tsawar azãbar wulãkanci, ta kamã su sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa (dõmin nẽman wata fã'ida).