Suratu Al-Faatiha الفاتحة
Ayoyi 7 · Makka · tsarin saukarwa 5
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiDa sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiGodiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMai rahama, Mai jin ƙai;
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
مَٰلِكِ يَوْمِ ٱلدِّينِ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiMai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKai muke bautawa, kuma Kai kadai muke neman taimakonKa
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
ٱهْدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلْمُسْتَقِيمَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiKa shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ ٱلْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ
Hausa Translation - Abu Bakr JumiHanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.[1]
Duba dukkan fassarorin wannan aya →
Kana neman wani jigo? Gwada binciken ma'ana — an bincika tambayarka a cikin ayoyi 6,236.
→